Uncategorized

MATAR UBA 4

 ????????????????????????????????          *MATAR UBA* 

????????????????????????????????

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️

 _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

???????? *MATAR UBA* ????????

     _(A True Life Story)_

           *Short story*

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`

Follow me on Wattpad @Milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*????????️

 _’kungiya d’aya tamkar da dubu_

https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa

_____________________________

 *MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.

 *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*

CHAPTER 4

????????????????????????????????????????????

…….. Da Sallama ta shigo ta tura kofan ga mamakin ta sai taga parlon a hargitse Rai a b’ace ta ce “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, me zan gani haka? Wato yaran Nan sun ga bana gida shiyasa suka hargitsa min gida?”

Rai a b’ace ta Fara kwala Kiran sunan Asiyah ganin Basu amsa ba da saurin ta tayi niyar hawa sama, sai Taji wayan ta na ringing da har kamar baza ta duba ba, ta zaro shi a jaka ganin mijin tane ta zaro Ido, gyaran murya tayi Kan ta yi picking bayan sun gaisa yace “Ya kuke da yaran?”

Kirkiran Murmushi tayi Tace “muna Nan lafiya Lau Kai fa?”

Yace “Nima Haka Ina yaran suke ne ki basu mu gaisa please”

Cikin Rawar murya tace “Na Basu wayar ku gaisa?”

Yace “Eh”

Tace “Emm…kasan bamu dad’e da dawo wa daga Shan Ice cream ba Kuma munje park sunyi Wasa sun gaji”

“Allah sarki Baraka nagode Sosai Allah ya saka da Alhairi ya Miki Albarka”

Yar karamar dariya tayi Tace “Haba me na godiya? Ai jinin ka nawa ne ba sai ka gode min ba”

“Masha Allah to basu wayar”

Cikin inda inda Tace “A a ai suna suna suna emmm d’aki suna bacci sun gaji”

“Allah sarki nayi kewar su”

Murmushi tayi Tace “Suma suna kewar ka Amma kasan nafi kewar ka fiye da kowa ko?”

Dariya yayi yace “Baraka Kenan”

Tace “Kar ka damu idan sun tashi zan Kira na had’a ku”

“To nagode Allah ya Miki Albarka.”

Ta amsa da ameen, a tare suka kashe wayan.

Cikin sauri ta take tafiya tana Kiran sunan Anisah da Asiyah Amma Basu amsa ba tana Shiga d’akin ga mamakin ta taga Asiyah a tsaye ta jingina a kusuwar d’akin a tsawace Tace “Madam Ashe dama kina ji Ina Kiran ki baki amsa ba?”

Shiru bata kalle ta ba bare ta amsa sai Tace “ba wannan ba me ya faru da Parlor na” tana maganar tana kallon Anisah dake kwance tace “Ita Kuma wannar me ke damin ta? Ta kwanta bata motsi kamar matacciya?”

Kallon ta Asiyah tayi cikin kuka Tace “Eh sabida matacciyar ce” tana Kai Nan ta fice.

A hankali take tafiya har zuwa inda gawar Anisah ke kwance a hankali tasa hannun ta tab’a taji bata motsi jikinta Kuma yayi sanyi da sauri ta sake hannun ta ta fice daga d’akin tana ambatan “na Shiga uku” a cikin Zuciyar ta.

Daddy na jin Labari ya dawo da sassafe, a gaban shi akayi komai har aka kaita makwancin ta, zaune suke a parlor Yan Uwa da abokan arziki, kuka yake Sosai kamar wani karamin yaro Yana fad’in “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un ban kasance uba na gari ba, nayi alkawari wa mahaifiyar su zan kula da su Amma gashi na kasa cika alkwari.

Baraka dake zaune a gefen sa wani irin kallo take Masa na irin ko in kula idan ta ga alamun ana kallon ta Nan da nan sai ta canza fuska ta zama abin tausayi.

Kirkiran kuka tayi tana fad’in “Allah sarki Anisah ta, ta mutu ta barni bayan irin kud’aden da na kashe a gun lura da ita amma an raba Ni da ita” tana Maganar tana hararar Asiyah dake kallon ta, “Mutuwa Meyasa baki d’aukeni ba Kika d’auki yar auta ta Wacce nake Wasa da ita tana d’ebe min kewa Mai Wasa da gashin Kai na, yanzu wa zai kirani da Mummy? Bayan addu’o’in da nayi Mata ba dare ba Rana Ashe baza ta zauna ba” ta Karasa maganar cikin kuka.

Mutanen dake gun sukayi ta rarrashin ta, cikin dare Baraka ta farka a tsorace tana Kiran sunan Anisah a razane ya farka yace “Baraka lafiya?”

Sai Kiran sunan Anisah take sai yace “Ko mafarki kikayi ne?”

Ta amsa da “Eh” a tsorace, yace “kiyi addu’a mu kwanta” 

Cikin Rawar murya Tace “A’a Kar ka damu ka kwanta kawaii” yayi da ita Taki sai ya hakura yayi kwanciyar sa.

*BAYAN KWANA ARBA’IN*

Kawar Baraka Mai suna Nana mahaifiyar yesmin ce ta kawo Mata ziyara, juice ta d’auko Mata a fridge ta Mata godiya tace “kamar kin San Ina bukatar hakan na d’ebo Rana”

Dariya tayi Tace “Asha lafiya” bayan ta gama Tace “Qawata ya ture ture?”

Dariya tayi tace “Nana Kenan cikin sati biyar d’in shine Zaki ce ya ture ture?”

Murmushi tayi Tace “Ya Sadeeq da Asiyah?”

“Suna Nan lafiya Lau”

Ajiye kofin dake hannun tayi Tace “Qawata yadai Naga duk kinyi sanyi ne ko kin manta maganar mune? Kin manta cewar zaki b’atar da yaran dukka su biyu ne kamin ki haifi naki? Sabida ki gaji duk abinda Sadeeq ya mallaka Amma kinyi Shiru”

Baraka langwabe Kai tayi Tace “Qawata mutuwar Anisah ya kashe min jiki, ban san Meyasa nake ji kamar Ni ce na kashe ta ba”

“Kece Kika kashe ta Mana”

Baraka gyara Zama tayi had’e da fad’in “What?”

Nana Tace “What do you mean what? Mahaukaciya,Kina so kice min Baki san cewa ke Kika kashe Anisah ba? Da ace kin kaita asibiti da bata mutu ba, Kiyi gaggawan kashe d’ayar sabida Karta hanaki Rawar gabar hantsi”

Tashi Baraka tayi Rai a b’ace Tace “Tashi ki fita” tana nuna Mata kofar fita, cike da mamaki Nana Tace “Baraka!! Korata kike a gidan ki?”

“Eh ki fice min daga gida”

Tashi tayi Tace “Aikin banza Ina nan da kafafunki Zaki nemi ni.”

“Naji ki fita ko na sab’a miki”

Nana Tace “Me yayi zafi? Zan fita Amma Bari na karasa Shanye juice d’in”

A tsawace Tace “Aje Munafuka tunda ba da kud’in ubanki aka saya ba”

Murmushin takaici tayi ta fita, Zama Baraka tayi, tayi Shiru na d’an wasu lokuta sannan a fili Tace “Kuma ta fad’i gaskiya da ace na kaita asibiti da bata mutu ba, Asiyah Kema lokacin ki yayi dole na kashe ki abin da zan Haifa ya taso cikin gata.”

Tashi tayi ta Shiga kitchen tayi girki dake Sadeeq na gari dole tayi girki, bayan ya taso daga gun aiki ya biya ya d’auko Asiyah a makaranta duk ta lalace ta kasa sakin jikin ta kullum cikin kuka take shi duk a tunanin sa duk sabida mutuwar Anisah ce ita Kuma tunanin ya had’u ya Mata yawa mutuwar mahaifiyar su da anisah kuma tasan cewar Baraka ce sillar mutuwar Anisah Amma ba hali ta fad’a Masa don Tace zata kashe idan ta fad’a Masa abubuwan da take musu shiyasa tayi Shiru.

Da Sallama suka shigo, tana ganin sa ta rungume shi, Tace “My Asiyah jeki cire uniform kizo kici abinci ko?” Ta amsa da “Toh” sai ta haura sama shi Kuma yace “Bari na watsa ruwa” ya haura sama.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button