AMANA TA CE Page 51 to 60 (The End)

Ammar ya sh’igo zai musu sallama ya wuce yatarab ba Mum ya musu sai da safe ya fita.
Biyo sa tayi da ta sha gabansa kasancewar ida suke ba haske kafin ka isa harabar gdn ne, kuma tasoma masa tace”ni wlh bana son auren inada wanda nake so kuma shiya yace yana sona ai, ganin Ammar yayi sh’iru baice mata komai ba tasa ta fada jikinsa ta sake kuka nan take Ammar taji lbr yasoma sauyawa, kara rungume Auta yayi yace”Zainab sai da taji sunan har cikin kw”anyanta, bata iya amsawa ba sai binsa da tayi da ido yace wa kike so?, jin tambayar tayi tazomata a BAZATA, shiru tayi ta kafe sa da ido ganin yanayin da take kuma ya fahimci sh’itake so, sai yamata dabara sunanta yasake kira akaro na biyu kasa amsawa tayi yace”Zainab kina Sona?.da sauri ta daga kai alamar eh! Lallausar murmushi ya saki ya kara rungumeta fuskansa ya duko zuwa dai-dai kunne ta yace Zainab nine mijin da zaki aura, nayi hakane don in ga kina qauna ko ba ky’a qauna ta. Dukan wasa ta kai masa a kirji yace”wash ashh kika dake sai na rama zata gudu ya cabkota ya kara mannata da jukinsa tana kiciniyar kw’acewa ta kasa sai da ya bata lafiyayan kiss tukun ya saketa don kar ya wuce gona da iri.
Da gudu tayi cikin gd tana yar dariya.
H Mamu ta sanar da kausar ita ma ba a samu matsala da ita ba. Don haka suka ci gaba da sh’iri.
Ammar akw’ati Uku da kit ya yi ma auta bai wani yi kayan karya ba turmi ish’irin ya mata sai English wears da ya samata. Ban garen Ahyan shima turmi talatin yayi da akw’ati hud’u da kit komai sai son barka a talakance ba karya aciki.
H Mamu ta had’a yan Amareta tana ta tsumasu su Munay sai shirin biki akeyi.
Ammar gida ya kama musu plat su kadai ba mai tsadan daga hankaliba 80k ya samu.
Ya sh’irya shida Auwal sukaje k’auyen su Malam ya sanar musu da Inna laure yace”Malam ina son kazama waliyin Auren mu, yaji dad’i sosai basu bar kauyen ba sai tare da su Malam gd da suke ya kaisu d’aki Auta.
Amare liyafa suka sh’irya sai angwaye da suka sh’irya Dinner.
Yau take laraba duk gidan acike yake da yan biki yan sokoto sun zo, Amare ko Mum ta hana su fita anata gyara su Ammar da Ahyan sun had’a kai tare suke komai da Auwal Munay ko da Auwal tunda aka fara hidimar biki naga abunsu sai a slow.
Yau Al’hamis takama yau za’ayi liyafa Mum ne ta kawo musu wani sari mai ky’au sosai, masu kw’aliya suka gyara Amare lokacin da suka fito gun liyafar dake acikin gd za’ayi hmmm masu karatu lokacin da suka fito karkuso ku gansu ohoho abun bacewa komai don sun sha ky’au kamar ba gibe, liyafa akayi na gani na fada malama Khadija da Malam Juwairiya suka gabatar da nasiha game da rayuwan aure.
Bayan an tash’i a gunne suka nufo gida suna d’aki munay ke zi-zita irin ky’an da sukayi tace”Allah yasa wankar Dinner tafi na yau murmushi sukayi dukansu gabaki d’aya.
Ran jumma’ah tun da safe suke aiki dafa abinci yan d’aurin Aure sai da suka kammala komai H Mamu tazo tasa Amare sukayi wanka cikin atafa sun sha turare had’in yar mai duguri, bayan Sallah Jumma’ah aka saida Aure Ahyan da Kausar, Ammar da Zainab daga guri yan d’aurin aure suka wuce zaranda holel don gudanar da walima.
Da dad’dare Amare sunsha ky’au cikin gown kowacce kala d’aya da angonta Ammar yasha shadda fari da ratsin marun yayinda Auta tasha gown fari da ratsin maroon colour aciki ta sha make-up sosai tayi ky’au.
Ahyan kuma daga nesa na hango shi da farin shadda yasha aiki da zare blue colour, Kausar ma gown ta sha fari da ratsin blue colour bakaramin ky’au tayi ba.
Mutar d’aukan ya biki ne ta tsaya duk suka debi wayanda suka dace, Munay da Auwal ya d’auketa a motarsa yayinda aka tafi da Kausar da Ahyan a motar abokinsa, sai da aka gama kw’ashe su kafi naga wata k’atuwar Jeep baka mai bak’ak’en glass perker ba a dad’e ba naga wata mata tafito da Auta tun daga nesa take zuba ky’ali. Ammar kam sake baki yakeyi yana kallonta baita ba d’aukar ky’an Auta ya kai haka ba, bud’e murfin motar aka sata aciki, sai da ta zauna tukum taji k’amshin da tasaba ji, da sauri ta kalli gefenta Ammar ta gani yana mata murmushi. Lokacin aka jasu a motar hannusa ya sanya cikin nata yafara murzawa dake cikin motar ba haske matsowa yayi kusa da ita ya janyo ta jikinsa ya sanya haske wayarsa yana haska fuskanta sai da yagama kalon fuskanta ya gan-garo zuwa bakinta da ya sha jan baki a gankali ya soma. Oh!! Na gaji masu karatu sai zuwa page d’in gaba zaku jini.
Taku a kulum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Wayar sa ya haska ta da ita tayi ky’au kamar ba Auta da ya sani ba, a hankali ya soma bin fuskan da kalo har yazo dan k’aramin bakin ta da yasha janbaki maroon, idonta ya haska yaga ta lumshe su wani kyau na musamman ta kara masa a hakan, take yaji wani farin ciki ya lulubesa yau Autarsa ta dawo mallakinsa YAR’AMANA sa, a zuciyara yace”ina ma da su dad suna yare suga wannan rana nasan zasu fi kowa farinciki. Ya Allah kajikansu kamusu Rahma Ameen.
Kashe wayar yayi ya kara matso da fuskansa har Auta na jiyo numfash’insa, nan take yasoma jin wani abu na tsirga masa, bakinsa yasa cikin nata yafara mata wasu salon, dai-dai lokacin suka iso, a hankali ya matsa gefe jiki ba kw’ari.
Duk yan dinner sun shuga su Ammar kadai ake jira, sai da su Ammar suka d’au lokaci kafin suka fito Ahyan na rike da hannu Kausar gsky sunyi ky’au. Ammar yace”amana afuwa mun bata muku lokaci. Murmush’i Ahyan yayi yace “mush’iga kawai don lokaci na kara tafiya. Ahayan da Kausar sune a gaba sai Ammar da Zainab, tunda suka saka kafa acikin hall d’in na saki baki ina k’alon Amaren nan, gsky Allah yayi halita a gun baran na bayannan wato Ammar da Auta. Amrah ce ta zungureni kai Rash wannan wani irin kalo ne kamar zaki cimyesu, hmmm nace”My Amrah ke dai bari kawai Amaren ne sun tafi dani sun had’u sosai gsky sun dace da junansu.
High table din nake bi da kallo gefen Ammar Auwal ne da Munay sai kujeran kusa da su Jidda da Ghali(Haughal) na gani, ko da na kali gefen Kausar Raheenat da MY na gano sai wata kawar kausar da saurayinta.
Kid’a ne ke tashi a gun ko ina ka duba jama’a ne suke zaune kowa da masoyinsa ga Mrs Umar ma da Sojanta sai luv suke sha. ‘Daya daga cikin abokan Angwaye ya bud’e taro da addu’a, kafin aka soma gudanar ta dinner sai da suka danci abun motsa baki, aka umurci Amarya Kausar da Angonta suka fara sauka kid’a aka sake musu nan fa yan liki suka taso bayan sun taka ne, aka umurci Zainab da Ammar su fito, tunda aka kira sunasu Auta ta lafe ajikin Ammar bata son sauk’a, Ammar ya janyota jikinsa kai ka dauka wani zai kw’aceta ita ko ta lafe ajikinsa, cikim nutsuwa suke sauk’owa abun gwanin burgewa ohoho masu karatu naso ace kunje gun dinner nan don duk lbr da zan baku na Ammar da Auta zai d’auke mu lokaci mai tsawo.
Waka aka sake musu kan kace me yan likin Ammar da Auta sum taso suka fara musu har suka zo tsakiyar hall din, a hankali Ammar ke ta kawa amma Auta taki rawa ganin haka yasa ya kara matsowa kusa da ita ya mata cakulkuli aiko ta kw’ato jikinsa nan yafara ju-juya ta, in ka gansu kw’a d’auka salon soyyansu suke zubawa.