AMANA TA CE Page 51 to 60 (The End)

Haka tarin dinner ta kare cike da farin ciki suka dawo gida, kyar Ammar ya bar Zee tash’iga gd.
Taku a kullum mai k’aunar ku
Rash Kardam
[8:01PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Hajiya Mamu taso akai amare yau Amma dare yayi, haka ta hakura.
Da safe bayan sun karya ta zo d’akin Amaren da kayan fruit ta basu da wani abu kowacce cikin kofi d’aya, ni Rash nace “ko miye wannan oho!?.
Haka suka yini Mum sai d’irka musu abubuwa takeyi tun daya yamma ta hada su a daki d’aya ta soma musu nasiha gami da basu sirrikan saye zuciyar miji.
Da dad’dare aka zo d’aukan Amare sunsha kuka kam da ky’ar aka fita dasu, kowacce akayi kaita gidanta.
Abokan Ahyan ne suka raka sh’i saida suka dan tsokani Amarya, da yan barkw’acin su kafin suka masu sallama da fatan samun zuri’a na gari suka tafi, nima fatan alkairi namusu nafito tare da jan musu gate d’in gdn. Na nufi gidansu Auta don inga wainar da ake toyawa ta.
Ina isa na tarar da Auwal ne da Saeed suka rakash’i, nasiha sosai suka musu da yan shawarwari kafin suka musu sallama suka fito, Ammar ya musu rakiya bai wani dad’e ba ya dawo gefen Auta ya Auna tare da furta Alhamdulila!. Agogon dake hannusa ya cire yace Zainab kije kiyi alwala muyi nafila mu gode ma Allah da wannan babban ni’ima daya mana. Mikewa tayi ta nufi toilet ta d’aro alwala bata dad’e da fitowa ba shima ya fito suka suka tada kabbara. Raka’a 2sukayi kafin ya dafa kanta yasoma karanto addu’ar da in mutum yayi Amarya ko sabon abu zaiyi kafin yafara amfani da abun. Ga addu’ar kamar haka”Allahummah inni as’aluka khairi ha wa khaira ma jabaltaha alai, wa ‘a’ uzubika min sharri ha wa sharri majabalta ha alai”. Ma’anarsa sh’ine Ya Allah ina rokonka Alkairinta da d’abi’anta akansa, kuma ina neman tsari da sharrinta da sharrin da ka d’abi’antar ta akansa.( yan’uwa yana da kyau mu runka yawaita yin wannan addu’a yayin da mukayi sabon abu, Addu’ar tana da matuakan amfani, Allah yasa mudace Ameen).
Sai da ya gama karantawa tana amsawa da Ameen har ya kai karshe, kitchen yaje ya d’auko musu plate ya saka musu kazan da fresh milk mai sanyi yasa musu a kofi, Auta ta kasa sakin jikinta da sh’i, naman ya d’auko yazo dai-dai bakin ta ta kawar da fuska tana yar murmushi kasa-kasa, cikin zolaya ya dawo ta gefen da ta mayar fa fuskanta cike da tsokana yace” Amarya yau kunyata kike ji?. Uhmm ta fada tare da sake mayar da guskanta ta d’aya barin mikewa yayi cikin shauk’in so da kauna yace”baringa ta ina zamu fara, ita ko sai zi-zilewa takeyi.
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Haka sukayi ta hiransu cikin barkw’anci, Ammar ne ya mik’e ya yace barin watsa ruwa d’akinsa ya nufa, Auta ma ta mike taje tayi wanka mai ta shafa sai man baki ta kw’anta ta lumshe idonta tamkar mai bacci, Ammar ya sh’igo cikin sh’irin kwanciya yayi ky’au, ya tsaya k’are ma Auta kallo tayi ky’au cikin kayan baccin, wani lalalusan murmushi ya saki ya kashe musu wuta. Ni Rash nace”oh! Wanan mirmush’in kam yau na sam Auta sai ta gane kurenta agun Ammar, bare mai nema ya samu.
Da safe na leka gidan Zee Auta na tarar tayi wanka Ammar ma ya shirya cikin sh’iga mai ky’au, yazo dab da ita yace my swt muje mu yi breakfast, cikin shagwaba tace” ni ni sai tayi sh’iru, bai tsaya kara sauraronta ba d’auketa kamar wata baby sai dinning ya direta abaki ya rinka bata abinci har sai da ya tabbatar ta kosh’i tukun ya ky’aleta sh’ima ya karya. Ammar da Zee soyayya suke gudanarwa mai tsabta, basa son ganin d’ayansu cikin damuwa komai tare sukeyi in Ammar na gd.
Kw’aki sun ja, watani sun tafi, shekaru da yawa sun shud’e, wani make-ken gida na hango wanda ya tafi da hankali na, ina tsaye ina kale-kale na hango wata mota k’iran Toyota Camry 2016 blue colour, ta sh’iga wannan gidan, da sauri na da gudu yanda komai gadi ba zai iya rik’eni ba bare ya hanani sh’iga gd, cikin flowers na lab’e, motar ne ta karasa sh’igowa ina kallo tayi parking a wajen ajiye mota, duk na kagu in ga wacece zata fito ta dad’e kafin ta bud’e k’ofar motar, k’afarta ta fara sauko da su Yasalam na furta, masu karatu sai kunga kafar tamkar na Zee hrt tsaban kyau…lol… A hankali ta k’arasa fitowa sai naga wasu yara su biyu mata sun fito d’ayar zata kai 10 yrs karamar kuma zata kai 7yrs yaran sun had’u kama, mai gadi ne ya musu sannu da dawowa ta amsa da sakin fuska, ta nufi cikin gd. Zarah ce tayi nufi stairs tana kw’ala kira ma nanny su k’ira, khairat kuwa dake suka zube a falo ita da Mum d’inta.
Wani had’ad’en guy fa ba zai wuce 40yrs ba ya sauko rike da hannun wani yaro kamar su d’aya da sh’i sai a lokacin na gane ko suwaye AMMAR da ZEE AUATA da yaransu, duk ta canza ta k’ara ky’au ta da girma.
Yazo kusa da ita ya zauna yace”Madam kin dawo ya hanya? Alhamdulilah! Ya kalleta kafin yace “My Luv ina son yau zanje na taho da su Malam da Inna, don an gama gyara gidan ansa komai aciki, cikin jin dad’i tace” Abban zarah ka ky’auta Allah ya kara bud’i Ameen, Zainab Malam sun can-canci haka don sun mana abunda bazamu manta ba, tace” hakane kam ALKAIRI DANKO NE book by Ummu Aisha, Baya tab’a fad’uwa kasa bamza.
A ranar ya je ya taho dasu Malam da Inna gd ya musu mai ky’au sunyi murna sosai.
Taku a kullum mai k’aunar ku.
Rash Kardam
[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE
By
©Rasheedah .A. Kardam
Alhaji Ammar Sa’ad Saraki ya dawo hamshakin d’an kasuwa mai cike da naira ya sanu ciki da wajen kasannan, yana da company a yawancin State d’in dake 9ja.
Jerin gwanon motoci na hango sunyi com boys abun gwanin burgewa number motar kuwa duk iri d’aya ne ansa A S Saraki1 har zuwa 10 ya nufi gdn sa, ko da ya shiga matarsa ceta taso cikin shiga ta alfarma ta yi welcoming d’insa, sai da ya huta yaci abinci ya kaleta yace Madam kinyi ky’au kuma kulum kara ky’au kikeyi, cikin salon da ta saba rikita sh’i ta juya ido tace”kaima haka sh’iyasa kulum nake k’ara sonka. A natse ya kalleta yace”Zainab ku shirya ke da yara tunda suna hutu nagama yi mana booking din jirgi ran friday zamu kaduna. Da sauri tazo ta run gumesa ko mai ta tuna sai tafara zubar da hawaye janyota yayi jikinsa yasoma lalash’inta yace”nasan me kike ma kuka ki share hawayenki yanzu ne lokacin da zamu dau fansa.
A yanzu dum wani moving din Baba Sani ina da lbr akansa kuma Baba Isya ya rasu a razane ta d’ago amma tuna abunda sukayi ma iyayenta cikim kasa-kasa da murya tace”to yau ina Baba Isiya yake gash’i ya tara da su Dad, rayuwa ke nan duniya ba gurin matabbata ba ne.
Tun ran Alhamis suka je gidan H Mamu suka mata sallama tare da musu fatan nasara daga gidan kuma suka nufi gidansu Malam suma Addu’a suka musu.
Ran friday tun karfe 1:00pm aka kaisu Airport basu dad’e ba jirginsu ya d’aga sai KD, 1hrs ya kaisu cikin garin KD, wani katafaren gd da Ammar ya gina acikin garin kaduna suka sauk’a, garin duk ya fawo ma Auta wani iri basu fita ko ina ba sai washe gari suka sh’irya cikin sh’iga ta alfarma da yan yarasu uku Zarah ce baba sai mai bi mata Kairat sai Al-hasan mai sunan Dad suna kiransa da junior, yaran ky’awawa da su gwanin burgewa. Motocin Ammar ne suka jero zuwa k’ofar gdn. Ammar rik’e da hannu junior sai Auta rik’e da hannu Kairat suka sh’iga mota suka nufi Hayin Rigasa.