AMANA TA CE 1-END

AMANA TA CE Page 51 to 60 (The End)

Taku a kulum mai k’aunar ku

Rash Kardam

[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                       

   Motoci ne a jere suka sh’iga layin duk jama’ar dake unguwan sai lek’e sukeyi don basu taba ganin motoci sun jero irin haka ba, wasu kamma cewa suke yau gwamna ya zo umguwansu, dai-dai k’ofar gidan su Auta motar ta perker body gurad d’insa ne suka fito sai da suka rarrabu a gun kafin aka bude ma Ammar k’ofar motan ya fito, zagawa yayi ya bud’e ma Zee sai yara suka fito daga motarsu, duk yan gurin ba wanda ya shaidasu sai dai sunga ansa AS Saraki a jikin motar kuma suna jin lbrsa. Baba sani dake sh’irin fitowa yaga mota a k’ofar gd sa tabbas yana jin lbr AS Saraki k’odai mafarki yakeyi ne kam ya san ba abunda zai kawosa gidan.

 Ammar ya mika masa hannu suka gaisa yace ka sai dani kuwa Baba Sani da yayi mutuwar tsaye yace”Eh! A S Saraki da nake jin lbrsa ne ko? Ammar yayi murmushin kasaita yace”kw’arai kuwa nine, mush’iga daga ciki falo su Auta aka sh’iga da su sai da aka kawo musu kayan shaye-shaye sam Baba Sani bai ganesu ba, sabida shekaru sun tafi da yawa ga naira ya zauna musu, Ammar ganin bai ganesa ba yace wata kasuwanci ne nake so muyi da kai, na samu lbrka gurin wani yaron ka mai suna Gumus, ya yaba da kai sh’iyasa naji ka kwantamin a rai da mu had’a business, sun d’anyi hira kafin yamasa sallama ya rako su har bakin mota saida suka sh’iga ya kima gd cike da murna tabbas tsun-tsu daga sama gashashe, nikam Rash nace”wato mai hali baya fasa halinsa a ko ina yake”. Sun d’ansoma tafiya kenan sai ga motar Futha ya danno kai dake glass gin ta fari ne Ammar yasa aka dakatar da ita sam Auta bata lura da itaba sai da yace mata”Sweet kali can aiko ta kalo futa zata fita da gudu ya riketa yace zaki wargaza mana plan d’in mu Short note yayi ya bama body gurad d’inda ya bata, ko da ta karanta ta bud’e murfin mota da sauri ta fito Ammar ya rage glass d’in motar sa tabbas sune ba gizo suke mata ba. Ammar yace kin gane a kw’ai Adress din mu so kizo ki same mu anan plan d’in mu zai iya wargajewa ok! Motar ta takoma cike da murna tana gode ma Allah da ya bayya na mata su Zee dinta

Da yamma Barrister Futha ta nufi gd su Ammar ko da taje sunyi murna ita da Zee sannan suka bama juna lbr bayan rabo Futha cikin mamaki tace”no wonder biri yayi kama da mutum dom na dad’e ina zarginsa kam nan ta ce bari na sanar da Sadiya don baza a rasa wani evidence a gunta ba, ringing biyi yayi ta d’auka sun gaisa futha ta bata lbr komai cikin murna tace”Futha suna ina nan ta bata Address d’in gidan bata dad’e bakuwa ta iso sun gaisa itama aka bata lbr taci kuka jin Babanta ke da hannu kuma ta d’au alwansh’i basu goyon baya don a kamash’i, Futha tace”yau weekend ne bazaiyu ayi karansa ba amma zuwa Monday sai ayi yanzu dai Ammar duk abun zai zama a hannuka ne duk yanda za’ayi kar kabari ya bar gari ko ya ganeka ok! Haka suka watse.

        Yau monday duk wani ma’aikaci ya fita aiki, yau ne su Ammar suka kai karan Baba Sani, police har gd sa suka je aka kamasa C.I.D aka kaisa, ba irin wahalar da ba’a masa ba ama fir yak’i fad’ar gsky harranan sh’iga kotu, kowa ya hallara a koto, mai gabatar da kara ya tashi ya koro bayani ba alkali, barrister Futha ta fito ta gaida alkali kafin ta soma yan tambayoyi ma Baba Sani amma fir yak’i yarda da sh’i yayi, rashin wata kw’akw’aran shaida aka d’aga karan har sai 5/3/2016 haka aka watse amma kotu ta hana belin Baba Sani har sai ansamu gsky.

Taku a kullum mai k’aunar ku

Rash Kardam

[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                       

Yau takama ranar da za’a koma kotu,tun da wuri su Futha suka hallara don su had’a shaidar da Ammar yace ya samu amma shiru bash’i ba lbr sa, sai dab da za’a sh’iga ya k’araso gunsu jiki ba kw’ari ya iso Futha cikin damuwa ta ce”ya dai ina fatan ansamu nasara. Ammar yace”wa yanda zasu taho da su gumus da Duna da su baba mai gadi na kira wayarsu a kashe kuma bawani lbr, wani iska mai zafi ta furzar tace”ga Sady sh’iru itama bata iso ba, dai-dai lokacin aka sh’iga kotu mai gabatar da kara ya karanto kara da akeyi, lauyan mai kara ta fito bayan ta gabatar da sunan ta ta zauna, lauyan mai kariya sh’ima ya gabatar da sunansa, nan aka nemi mai kara ta gabatar da shai du, sh’i alkali ya ce”rash’in wata gamsash’iyar shaida kotu zata… Bai karaba Sady tash’igo cikin hanzari tace ranka sh’idade akw’ai shaida a tare da ni, gabad’aya aka juya ana kalonta, a hankali ta zo gaban mutane d’auke da wata envelope ta mika wa Alkali ta sake bash’i wasu kaya tace”ranka sh’i dad’e ni d’iyar wacce ake kara ne, sanan bin ciken danayi, na samo wad’anan kayan da su akayi amfani gurin kashe Alhaji Al-hassan da Matarsa sanan hatta bindigar da akayi kisar akw’ai sanna akw’ai ta kardan da sukayi tsakani mahaifina da Marigayi Baba Isiya akan zasu raba dukiyar Mahaifin Auta. Wayar Ammar ne yayi k’ara yana dubawa yaga number Kabir ne da sauri ya d’agawa yace kana ina? “Gani a k’ofar kotu muna tare da su gaba d’aya, right! Sai da ya nimi permission ya sai dama Futha ga sunan azo dasu, batare da bata likaci ba ta sanar da alkali ga wasu saidan ma an taho dasu, nan ta bukaci a had’a ta da police suka fita aka sh’igo dasu, Baba sani ya cika da tsanani mamakin gani su Gumus Da Duna da Masu aikin gdn, nan aka gatar da su, alkali ya ce”bisa ga kw’araran shaidar da aka samu na Sani da laifin kashe d’anuwansa da Matarsa, kotu ta yanke masa hukun d’aurin rai da rai, alkali ya mike kafin sauran mutane suka fito, Auta rungume Sady tayi tana kuka irin wanna jahadin da tayi, suna fitowa daga kotu gidansu Futha suka nufa sai da suka ci abinci tukun Auta suka koma gdsu.

Auta bata bar garin kaduna ba saida ta raba ma Matar Baba isiya da Su Sady sauran duk’iyarta ta mallaka musu don su samu abun rayuwa, cike da farin ciki suka dawo Bauchi Ammar ya kalli Auta yace”Alhamdulilah! Yau na sauke nauyi da nayi ma kaina alkawari shekara da shekaru.

Taku a kullum mai k’aunar ku

Rash Kardam

[8:02PM, 9/20/2016] Rash Kardam: AMANA TA CE

                        By

©Rasheedah .A. Kardam

 

                       

      Zaune suke a falo Zee Auta sai zuba shagwaba take wa Ammar ko sai biye mata yakeyi, junior ne ya biyo Khaira ta d’aukar masa yar babynsa da gudu, suka sauko falo, ya kasa kamata sai yaje gun Ammar da yar kukan shagwaba yace”Dad kaga Khairat ta d’aukan YAR AMANA TA Ammar yayi dariya kafin ya karbi Teddy ya basa, yace” kema zan sanyo miki naki, da murna tace” thanks u My Sweet Dad luv u too, junior ya kalli Ammar yace” Dad kaifa ina YAR AMAN KA?. Cike da fara’a ya nuno musu Mummy su, da gudu suka haura sama, sh’ikuma yazo ya d’auki Auta kamar yarinya yana ju-juyata yace” ina kara sonki ko da yaushe yarinya kike k’ara dawowa, kw’ayar idonta ya kalla yace” sh’iya sa nake kara tattala AMANA TA CE.

Alhamdulilah!! Tsarki da mulki iko su tabbata ga Ubangijin Talikai,

Ina mika godia ta ga Allah(S.W.T.A) da yabani damar na kawo k’arshen littafina mai sunan AMANA TA CE.

Yan’uwa ina fatan zaku d’au darasin da ke cikin wannan littafin, ko da yaushe mukasance masu kula da zumunci, hadisi ne guda ankarbo daga (musulum ya karbo daga manzon Allah tsira da aminci Allah su tabbata a garesh’i yace”la yadakulul jannati khad’i’u rahimi, mai yanke zumunta bazai shiga Aljannah ba” ya Yan’uwa kusani Zumunci da Amana suna gefen siradi duk wanda ya yanke daya acikinsu kugiyace zata jash’i zuwa wuta). Sanna kuma duk wanda yayi riko da Zumunci da Amana to zaiga sakamako mai ky’au, yana da ky’au muna tarayya da mutanen kw’arai sanna nu neman tsari da shaid’an don harda sh’i yake in gizamu zuwa aikata ba dai-dai ba.

Previous page 1 2 3 4 5Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button