Uncategorized

TAKUN SAKA 40

 

*_Chapter Forty_……….A kallo ɗaya da sukai masa suka fahimci lallai bashi da wadataccen lafiya, dauriya da jarumtace kawai irin tasa ya sashi amsa kiran nasu. I.G da gaba ɗaya dama burinsa yaga halin da Master ɗin ke ciki dan bashi da nutsuwar zuciya akan harbin da akai masa tun jiya ya mike da sauri ya nufesa. 

        Dai-dai master na karasowa garesa ya dan kame jikinsa alamar girmamawa. “Shuraim wannan gangancine ai. Shiyyasa nace maka basai kazo ba a wannan halin da kake ciki ka aiko Habib kawai”.

        Murmushi Master yay mai ciwo, cike da girmamawa a garesa ya ce. “Karka damu Uncle ina lafiya. Idan mun biyema ciwon da kawai mukeji a jiki su kuma masu ji a cikin zuciyoyinsu fa?. Tabbas inajin ciwo a jikina, dan shigar bullets a cikin jiki ba wasan yara bane, amma idan ina kwatantashi da ciwon da su waɗanda babu inda zasu kai kukansu sukeji sai naga ban cancanci raki ba”.

         I.G da ke murmushi mai ciwo ya ɗan bubbuga kafaɗar Master. Tabbas shima yanajin irin ciwon da Master ɗin keji a cikin ransa. Dan shine ma ya horesa akan wannan tsarin duk da dama shima yanada irin wannan zuciyar ta damuwa da halin da al’umma ke ciki fiye da kansa. Bin master ɗin dake ƙoƙarin isa gaban Efcc Chairman da General yay da kallo, yana jin ƙaunar yaron matuƙa a cikin ransa tun kafin randa ya gansa a wajen taron bikin gama secondary school. Kwazonsa ya sashi jin kwaɗayin biya masa kuɗin karatu. 

        Master da ya juya ga General da efcc chairman duk da kuwa haɗakace ta aiki ta haɗasu dalilin I.G duk yana basu girma suma, kodan shekarunsu da ƙyaƙyƙyawar zuciyarsu. Ƙame jikinsa ya sakeyi da risinar da kansa ya ce. “Good Everning Sirs”.

            Sosai ƙwazonsa da ƙoƙarin mutunta na gaba da shi ke sake saka musu ƙaunar yaron a zuciya. Efcc Chairman ya miƙa masa hannu alamar suyi musabaha. Babu musu Master ya bashi dan shima yafi bukatar hakan. Shima General musabahan sukai. 

           Cikin nuna kulawa suka tambayesa jikinsa? Akan harbin da ya sha. Ya tabbatar musu babu wani damuwa yaji sauƙi. Karkuma su damu tsautsayi ne kawai.

     Dukansu murmushi sukai, dan sun san dai Master ɗinsu ya faɗa soyayya da gaske. Dukansu sun san Hibbah, tun harin farko data kai masa batare da wani niyya ba I.G ya bashi shawaran aurenta, a cewarsa ba’a sakaci da irin waɗan nan yaran masu ƙwazo. Ko basu fito duniya ta sansu ba zasu taimakama mazajensu da ƙasa a gidajen aurensu. Da farko Master yaso zillewa. Sai dai kuma shiga cikin ahalinta da yay ya fahimci matsalar da suke ciki a hannun Halilu ya sashi amincewa. I.G ɗin ma da kansa suka nema masa auren nata.

        “Madam dai ta rantse sai da kasha bullets”.

        Efcc Chairman ne mai maganar cikin ƴar tsokana. Dariya sukayi gaba ɗaya, yayinda Master ya ɗan kai hannu ya shafi ƙeyarsa yana murmushi shima. A zuciyarsa kam aiyanawa yake (ai itama yau tasha nata bullets ɗin).

            Sai da suka ɗan gama barkwancinsu Master dai na tayasu da murmushi kafin su fara abinda ya tarasu. Cikin nutsuwarsa da bama aikinsa dukkan hankalinsa ya fara musu bayani akan abinda suka buƙata. Harma da wanda basu san da shi ba. 

        Mamakin yanda Master ke tafida aikin da har wanda bai shafesaba ya basu. Shi dai ɗan sanda ne, ɗan sandan ma normal ɗan sanda. Sai dai a dalilin faruwar wani abu da ya shafi I.G yake ɗaurasa akan wasu ayyuka na sirri da yake yi domin hidimtama ƙasa batare da wani mahaluki ya sani ba. General abokinsa ne, hakama Efcc Chairman. Kamanceceniyar halinsu na kirki yasa akoda yaushe suke zaman tattaunawa akan abinda ya shafi yankinsu dama ƙasar baki ɗaya. Wanda suna iya bakin ƙoƙarinsu sai dai sukan rasa a ina matsalar take akoda yaushe suna tufƙawa ana warwarewa?. 

      Akoda yaushe sai dai suyi zaman kawai su tashi, dan duk da kasancewarsu manya masu faɗa aji a hukumomin tsaro basu iya yin komai dake dai-dai da burikansu. Aikin da I.G ya fara ɗaura master a sirance yayi nasarane yaja ra’ayinsu gareshi har sukai kwaɗayin dinga sakashi ayyuka na musamman, duk da kuwa shi baida alaƙar aiki da su ta wani fanin. Ba yau kawai bane Master ya fara musu aiki. Yasha zaƙulo musu bara gurbi a cikin jami’ansu da manyan mutanen dake akan karagun mulki, kuma idan sukabi diddiginsu sukan samu abinda suke buƙatar.

    Bai wani jimaba tare da su saboda halin da yake ciki, sun tabbatar ƙarfin haline kawai yakeyi badan lafiya ta ishesa ba. Sallama yay musu akan zai ƙarasa sauran ayyukan da suka rage masa na tattare dukkanin bayanai na kowanne fanni nan da kwanaki biyu insha ALLAH da zasu kasa komai a fai-fai dangane dasu A.G da ire-irensa. Daga haka yay musu sallama ya fito cike da dakewa kamar yanda ya shigo. dan baya buƙatar wani ya fahimci halin da yake ciki musamman akan ciwukan harbin dake tare da shi.

★★★★

        Gudu yayi sosai akan titin, hakan yasashi isowa gidan cikin ƙanƙanin lokaci duk da kuwa ya ɗan tsaya a wani waje. Ledojin dake bayan motarsa na tsarabar su Habib ya ɗiba zuwa sashensu. Koda ya shigo suna baje a falo suna aikin da ya sasu, sai dai hakan bai hanasu shan shaftarsu ta hira ba kamar ko yaushe. Ko sallamarsa basuji ba sai da Sharifat ta nufosa da gudu tana kiran “Uncle oyoyo”.

      Tattausan murmushi ya saki a karon farko yana ajiye ledojin hanun nasa ya kai duƙe dai-dai da tsahonta yana buɗe mata hannayensa. Jikinsa ta haye tana dariya, ya lakaci hancinta shima yana murmushi da faɗin, “Beauty ɗin gidanmu batai barci ba”.

         Sharifat data makale masa kafaɗa tai yar dariyarta da kwantar da kanta kan kafaɗarsa. “Uncle ina game ne a wayan Yaya Idris”.

        “Lallai ƴar gatan Yaya Idris”.

Ya faɗa yana kaiwa zaune batare da ya kula su Habib da sukai tsitt ba tun kiran da Sharifat tai masa. Ledojin daya ajiye ma Adam ne ya miƙe ya kwasosu. Leda ɗaya ya amsa a ciki ya bama Sharifat. “Tom ga wannan maza ki cinyesa duka ki kara ƙatuwa. Kina gamawa kuma ayi brush da alwalan barci ai addu’a. Ki gaidamin baba sai da safe”.

      Cike da ɗoki ta amsa sheƙa da gudu tana faɗin, “Yeee thanks you Uncle ”.

          Hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa yana binta da kallo da murmushi harta shige. Yana son yara matuƙa tun shima yana yaron, shiyyasa a yanzu bashi da babban burin daya wuce yaga jininsa a rayuwa. Numfashi ya ɗan ja da gyara fuskarsa ya gimtse yana maido dubansa gasu Habib. A kusan tare suka haɗa baki wajen gaishesa da tambayarsa jikinsa. Cike da nazartar yanayinsu ya amsa musu dai-dai idonsa na sauka kan Habib da yaƙi yarda ya kallesa.

        Dukansu tarbiyarsa ce, dan haka ko laifi sukai masa a ƙanƙanin lokaci yake gano wanda ya aikata ɗin. Komai baice ba game da abinda ke a bakinsa ya miƙe, kai tsaye ƙofar fita ya nufa, sai da yaje gab fitar batare da ya juyo ba yace, “Habib ka sameni”. Daga haka yay ficewarsa.

         Dama tun kallon da yake binsu da shi suka sha jinin jikinsu akan an masa laifi, kowa fatansa kar yazam shine ya aikata. Jin ya ambaci Habib ya sasu maida kallonsu kansa. “Yaron nan wane ruwa ka ɓallo mana ne?”.

   Cewar Musbahu cikin ɗan tsoro. Harararsa Habib ɗin yayi yana miƙewa yabi bayan Master ɗin dan gudun sake wani laifin. Yana fita Adam yace, “Ni wlhy tun shigi da ficin danaga yanayi jiya akan waya nai tunanin hegen mai jajayen kunne wata tsiyar yake shiryawa. Sai dai banyi tunanin bahagon zaki zai ɓallo ba”.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button