Al-Ajab

An Cafke Matar Da Ake Zargi Da Kashe Kishiyarta Da Tabarya A Bauchi

Rundunar ‘Yan Sanda ta kama wata matashiya ‘yar shekara 20 bisa zargin kashe kishiyarta da tabarya a kauyen Gar da ke Karamar Hukumar Alkaleri a Jihar Bauchi.

Kakakin ‘yan sandan, SP Ahmed Wakil, wanda ya bayyana hakan ga manema labarai a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Bauchi, ya ce mijin matan biyu, Ibrahim Sambo ne ya kai korafin faruwar lamarin ga ofishin ‘yan sanda na Maina-maji.

Wakil ya ce, “A ranar 22 ga watan Nuwamba, 2022 Ibrahim Sambo Gar daga unguwar Pali, Karamar Hukumar Alkaleri, ya shigar da kara a hedikwatar ‘yan sanda ta Maina-maji.

“A nan ne ya bayar da rahoton cewa a ranar da misalin karfe 12:00 na dare, matarsa ​​ta biyu mai shekara 20 dauki tabarya ta shiga dakin uwar gidansa mai shekara 32, ta same ta tana tsakar barci ta rotsa mata a kai.

“Ya ce wannan ya sa ta samu mummunan rauni kuma da aka garzaya da ita zuwa Cibiyar Lafiya ta Gar,  a nan likita ya tabbatar da rasuwarta.”

Wakil ya bayyana cewa, da samun rahoton, wata tawagar jami’an ‘yan sanda da ke aiki a rundunar ta dauki matakin damke wadda ake zargin.

A yayin da aka yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa aikata laifin.

Ta bayyana cewa “A ranar Talata 22 ga watan Nuwamba 2022 da misalin karfe 11:00 na safe, uwargidanta ta aiki danta, Abdulaziz Ibrahim dan shekara biyar ya kai mata tsire, wanda bayan ta ci naman ne, ta fara jin wani yanayi wanda ya kai ta ga yin amai.

“Bayan haka ne, wadda ake zargin ta kira wata matar kanin mijin mai suna Fa’iza Hamisu da suka zaune a gidan tare, ta shaida mata abin da ya faru, sai ta ce da ita watakila Olsa gare ta, hakan ya sa ta ba ta magani don ta sha,” in ji Wakil.

Wakil ya bayyana cewa, ana tsakar haka ne wadda ake zargi ta dauko tabarya sannan ta shiga dakin uwar gidan wadda ta ke tsaka da barci ta rusa mata a kai wanda hakan ya yi sanadin ajalinta.

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button