AUREN GADO Page 11 to 20
Wasa wasa aka fara aikin ginin malam Wanda batasan daga Ina Abun ya samo Asali ba, cikin wata guda har angine dakunan Al majirai sunkoma andawo gyaran cikin gidan Wanda aka rushe gefen da suke ciki aka bugawa Inna flat Dan madai daici Da bazai cinye filin tsakar gidan ba sai dakuna biyu a waje, daya na Malam daya nasu Naziya. Aiki ne dayaja kudi Abunka da akwai su gamasu aiki birjik, mamaki takeyi sosai akan Wannan gyaran Wanda saida takasa daurewa ta tanbayi Inna shin Waye yake musu irin Wannan gyaran ne? Tafada mata wasiyyar mijinta ce kanin shi ke isarwa, a ranar saida ta shiga daki tayi kuka sosai.
Tareda yi mai Addu’ar Allah yakai haske kabarin shi, tasan tayi babban rashi a rayuwar ta, a duk lokacinda ta tuna da kudurin shi nason ya huta da ita sai tayi kuka, yaso ya taba kirjin ta kamar me kunya ta hanata, Ina ma ana dawo da hannun agogo baya da ta Bashi dama yayi yanda yaga dama da jikinta kila data rage takaici, wani irin bakin ciki takeji idan ta tuna cewar Khaleel zata Aura domin tasani Malam baya magana biyu.
Cikin wata uku gidan nan yayi tsab bazaka taba gane shiba waje da ciki kowa sai ya yaba a unguwar, Almajirai sun samu gata domin odar katifu irin na yan boarding akayi musu Wanda a wanna dalilin yasa tsangayar take Kara bunkasa. A gefen gidan momy kuwa tun bayan tafiyar khaleel da sati biyu Fauziya ta tattara nata tayi tafiyar ta Tareda cewa “wallahi sai mijin ta yadawo zata dawo bazatayi gadin wata uwar miji ba, Wanda hakan ya taba mommy sosai domin tasa ran ita zata tsaya ta debe mata kewa, wani lokacin ta kanyi kukan rashin Ahmed don dai tana fita aiki ne Amma zaman kadaicin yana mugun tabata, watannin Sam ba masu sauki bane a wurin ta. Gefen Fauziya a kullum suna waya da khaleel yana kiranta tareda fada mata tayi hakuri idan yadawo komai zai dai dai ta, domin yasan cewa akwai hakkin ta a wuyan shi yana kokarin tursasa zuciyar shine kawai gudun hakkin ubangiji, bata taba fadamai cewa bata gidan ba, sai ranarda sukayi waya yafada mata yana hanya cikin satin bayan ya kwashe kyawawan watanni hudu a kasar ta China,
Kawai Mommy ganin ta tayi tana shiga part dinsu lokacin tafito zata tafi aiki, “A’a Fauziya andawo? ” eh bakya kaunar indawo din ne to na dawo. “A’a murna nakeyi ai gidan shiru ni kadai, yanzu dai zanje aiki in nadawo mayi magana, ta bita da harara, “Y’ar sa ido kawai mtswew.
Wanda Mommy murna takeyi domin ita zaman Fauziya a gidan ta Kara mata girma yakeyi tareda mutunci a cikin kawayen ta don haka duk yanda zatayi zatayi taga ta rusa maganar Auren Naziya da khaleel, zakuma ta gyaro zaman Fauziya da khaleel Indai ita tahaife shi……. ????
*Matar Soja*
????????AUREN GADO????????
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA
Y’AY’AN GATA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y’an ???????? Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
2⃣3⃣&2⃣4⃣
………….. A katon filin jirgin yafito yana Takawa daya bayan daya kamar wani prince, sheki yakeyi yana wani irin haske, idanun shi dauke da katon eye glass, baka ko ganin kwayar idanun shi, fuskar shi dif take ba Annuri yakara haiba da cika ido, watannin hudu sunyi matukar taimaka mai wajen warkar da damuwar rashin dan uwan shi kadan, driver ne tare da manager dinsu ya tareshi, gaisawa sukayi ya shiga motar suka zuba mai duk kayan da yazo dasu, suna tafiya yana discussing harkar business din su Wanda an samu cigaba sosai a cikin watannin fiyeda shekarun baya, domin shi mai zafine kuma baida sanyi kamar yayan shi, yana bin diddigin komai ma’aikatan sun san an samu canjin boss ba wasa, kuskure kadan yagani ko yaji tun yana China zaisa ayi firing mutum a aiki.
Kamar daga sama suna zaune dai dai itada mommy suna hira mommy na Kara lallashin ta tareda alkawarin komai zaiyi dai dai idan yadawo tunda yafara sauraran ta. Kawai sukaji sallamar shi sama sama, wani irin zabura sukayi duka tareda sakin baki, suna mai welcome, zama yayi kawai gefen mommy ya gaida ita tareda dan sakin fuska, domin uwa uwace koda kuwa abola take yawo, he missed her domin fushin da yakeyi da ita yasa tunda yaje baya kiranta baya son ko jin muryar ta sai in ita takirashi, he know she is wrong, kuma shima he is wrong, domin ba Wanda yabashi damar watsar da uwar shi, riko Hannun ta yayi tareda sakin murmushi, “mommy am back. I’m glad my son, ya harkokin ina ji a bakin manager komai na tafiya normal. “Yeah Alhamdulillah. Wani irin rawar kafa Fauziya keyi ta matso tareda zama gefen shi tadafa cinyoyin shi dake cikin blue jeans dinshi sabo dal, “Baby wannan irin surprise haka dama kafada, am happy wallahi. Ture hannun ta yayi tareda mikewa yace” OK bari inshiga ciki zanyi wanka in huta, mommy please am hungry. Jikin ta narawa tace bari in hada maka meal din ka just five minute,Ta wuce murna fal cikin ta, tarar shi Fauziya tayi tace “darling muje part din mu mana nan akwai takura ba sakewa”.
Mugun kallo ya watsa mata kafin cikin zafin rai yace “uban waye zai takuraki anan, now listing I know exactly what you are doing, ko ki dawo nan ko ki yi ta zama acan ke kadai, saboda bana ra’ayin zuwa wanna gidan if you are ready ga dakin ki can! Ya wuce abun shi.
“Kutumar uba wato dakin da Y’ar kauyen nan ta zauna yakeso ta dawo wallahi bazata dawo nan ba sai dai duk Abinda zai faru ya faru. Bin bayan shi tayi bayan ta gama dogon tunanin ta, lokacin harya tube ya daura towel, tuni taji wani irin feeling ya taso mata domin khaleel fa namiji ne complete ba algus ya ginu ya keru, wani fesar da zafin bakin ta tayi kafin ta matsa tana karairaya zata rungume shi.
Hannu yadaga mata “please, bana son disturbance, nagaji now get out.
Haba khaleel wane irin daukar Alhaki ne wannan? you’re my husband why All this?, ko bankai mace bane, Auren mu wata hudu Amma ace ko hug baka bani damar yiba. “Go and ask mommy idan ta Amince da hakan saiki dawo now out. Yafada yana wucewar shi bathroom. Fita tayi kawai rai abace taci karo da mommy, me yafaru kuma kinfito da bacin rai? “Ba dole ba, yaza’ayi ace wai sai na tanbayi izinin ki zan rungumi miji na? gaskiya kekam a bincike ki kina wa yayan ki asiri ne wane irin biyayya ce suke miki kike cutar dasu, so kikeyi nima inyi rayuwa irin ta Naziya? wallahi ko kina so ko bakyaso sai kinganni da cikin khaleel. “Haba Y’ar lelen mommy zo kiji, ke baki iya siyasa ba keda zaki caba ado ki makalewa mijin ki, ya zakice banason hada iri dake Fauziya, duk soyayyar da nake nuna miki haba ki rika ragamin mana. “Nidai kiyimai magana yadawo gefen mu Ina jiran shi. “Jeki zanturo shi kin ji. Ko sauraran ta batayi ba ta fice, saida ya dauki kusan minti talatin yana kwance tareda runtse idanun shi a cikin ruwan, shi kadai yasan tunanin zuciyar shi, wani irin murmushi yayi na gefen baki, kafin ya fito ya dauraye jikin shi, ya daura towel ya fito, mommy da ya gani zaune da Abincin shi tana jiran shi yasa yace “oh my mommy am coming tank you, I really miss your cooking.