AUREN GADO Page 11 to 20

Khaleel kuwa zazzabi mai karfi ya rufeshi Saida likita yazo ya kuma dubashi, su Malam na tausar shi tareda mai nasiha mai ratsa zuciya, kabi d’an uwan ka da Addu’a shine kawai soyayyar da zaka nuna mai yanzu.
Gefen Amare Fauziya tafi d’an natsuwa domin mutuwar ta taba zuciyar ta don duk shashancin mutum yau ace Wanda kasani yafadi ya mutu, dole kaji jikin ka yayi sanyi idan akwai Imani a tareda kai.
Gefen Amaryar Ahmed mommyn ta da y’an uwan ta nafama akan ta shirya takaba tace atafau bazata yimai takaba ba tunda ko kwana basuyi ba tare, maganar har taje kunnen mommy, bata iya cewa komai ba domin ta shiga rayuwar kurame na wucin gadi, Naziya kam bazata iya bude baki tace wai mijinta bai kusance taba, domin akwai Alkunya kuma ko saboda soyayyar datake mai tareda hakkin igiyoyin nan uku dake wuyan ta dole tayi mai takaba, in akwai Abinda yafi haka ma zatayi mai domin ita tasan tayi rashi babba Wanda maida irin shi zaiyi wuya, ita ai jitake ma ta rufe shafin Aure a rayuwar ta.
A cikin kwanakin uku zuwa bakwai bamasu sauki bane ga duk makusantan mamacin, tun daga kan mommy, Naziya, Khaleel da duk wasu masoyan Ahmed,
A dakinta take tanayi mai takaba mai tsabta tareda binshi da Addu’oi dare da rana, kuka kuwa kullum dare sai tayishi rayuwar da sukayi dashi batada tsawo Amma yabar mata memories da zasu rika tuno mata dashi har karshen Rayuwar ta.
Seven days
Khaleel Ko part d’in shi bai zuwa tun ranar da fauzy ta shigo ko kallon ta baiyi ba, Abinci ma baya iya ci ya rame a fuskar shi sosai daka kalle shi, Aunty zarah ce ta shiga dakin shi yana zaune rikeda waya karatun Alqur’ani mai girma natashi, idanun shi a rufe, sanye yake cikin jallabiya fara, “Ibrahim” kazo Alhaji na Kira ta fada tareda juyawa, tashi yayi yana sa stop tareda rike gefen jallabiyar shi ya fita, a katon falon ya samesu dukan su har Naziya tana nade cikin hijabin ta, gefe daya Maman Salifa ce da ta Fauziya duk suna hakimce sai kuma Amaren a gefe, Wanda shi tun ranar da aka kawo su bai sasu a idoba, Kawu da malam ne zaune a kujera sai kannin kawun mata biyu gefe, mommy ce tayi shiru kamar ruwa ya cinyeta, kana ganin ta kasan mutuwar ta tabata. Kawun ne yace “Malam Abubakar na taraku ne anan saboda Abubuwa uku na farko dai Ina Kara mika ta’aziya ta gareka Ibrahim domin kai Kayi rashi, Allah ya Kara maka dangana tareda ikon daukar nauyin da aka dora a wuyanka, na biyu akan maganar Matar Ahmed, sun kirani akan zasu tafi da ita gida domin bazata iya yimai takaba ba, don haka ga Malam muji shima idan zai tafi da Ita uwar gidan ne gida. Saurin dago kanshi yayi ya kalli gefen ta, sai yanzu yaga yanda ta rame tareda yin zuru zuru, gwanin tausayi, ya ce Kawu duk yanda kukayi daidai ne. Abinda ya iyacewa kenan,
Addu’a malam yayi kafin yabisu da nasihohi ya karayi musu ta’aziya, ya dora dacewa Idan so samune Naziya ta zauna a dakin ta, Amma a yanzu saboda dalilai masu yawa zan mayarda ita gida tayi takabarta, Allah ya gafartawa Ahmed.
Wani irin daci Khaleel keji a zuciyar shi, yarasa wane irin tunani zaiyi baida kalma daya da zai iya furtawa a halin yanzu,
Kukan mommy ne yasa suka kalle ta, ba Wanda yaji tausayin ta har Khaleel din ma, domin tsawon kwana bakwai din nan baya ko kallon gefen ta.
Toh Hajiya bilkisu Ahmed ya tafi, Amaryar da kika buga kirji kukayi mai yau tace bazata iya zama dashi ba, sannan Inada yakinin mugun halin ki ne yasa itama Matar tashi za a tafi da ita, domin ni Nafi kowa sanin halin ki bazaki taba canzawa ba, da zaki canza da mutuwar yaya na zata fara canzaki, mundade muna daukar mugun halin ki yau kinga ni, Allah yasa ki dauki darasin idan har akwai sauran kwakwal akan ki.
“Ya isheka Modu karka manta d’ana na rasa babban dana duk Wanda yayi kukan mutuwar nan Kara yayi min, sannan maganar bakin hali, naji abarni da kayana duk ko wacce tafi ruwa gudu cikin su, ni Abarni da zafin rashin d’ana kawai, tafada tana mikewa cikin zafi tayi daki tana kuka mara madafa.
Ko dago kai Naziya batayi ba Saida malam yace “su shukrah na nan zasu hada miki kayan ki su taho dake, ni zantafi dalibai na jirana a gida. Ya musu sallama yatafi. Saura y’an uwan kawai da iyayen matan, Maman Fauzy tace toh Saura mu yaza’ayi da yarinya tun da tashigo ace bata samu kwanciyar hankali ba.
Cikin zafi yace “Zaku iya tafiya da ita in kun so I don’t need her.
Yafada cikin fada da kuma iyakar gaskiyar shi, “dama momy ta Aurota idan kunga bazaku iya zama ba ga hanya.
Cikin rawar jiki tace ” no mommy please kuje ni Ina nan. Tafada domin tana matukar kaunar Khaleel, bayan ta aureshi da kyar ta yaya zatayi sake ta fita, don haka tuni ta kashe bakin uwar, salifa ce taja uwar ta gefe, “mommy nidai kinga kisa kawun su yasa Khaleel ya Aureni tunda anayin Auren gado, kinga yafi ma Ahmed din haduwa mommy wallahi zan zauna in ya Yarda. “Y’ar gari nima tunani na kenan ai kinga yaron ya Tara dukiya kan dukiya gatashi gata uwar shi gata d’an uwan shi yanzu, ke fa uwar shi duk cikin mu tafimu kudi shegiyar, bari mukoma inyi magana.
Jiki na rawa suka koma falon lokacin Naziya ta mike tayi daki inda su Aunty Raliya ke hada mata kayan ta, daga Khaleel sai kawu sai gwaggon nin shi, mommy dasu zarah na daki,
Zama Maman Salifa tayi tana Washe baki “Alhaji Inada magana. Suka zuba mata ido kafin yace “munajin ki. “Yauwa nace ba, tunda dai ga d’an uwan shi mezai hana ayi tunani mai kyau a bashi Salifa sai a hada Auren gado. Wani irin saurin dago kanshi yayi tareda watsa musu kallon kun haukace ya ce “kuna hauka wallahi kun haukace, toh kusani kune sanadin duk Abinda ya faru a rayuwar d’an uwana, koda ace mata sunkare a duniya bazan taba Auren Y’ar kiba, don haka kawu ni natafi Inka gama domin one more minutes a nan zanyi Abinda bashi bane. Yafada yana wucewa a zuciye,
“Toh kunji sai ku tashi kubamu wuri, inji daya daga cikin matan, shigewa dakin mommy sukayi jiki a sanyaye,
Dayar tace “yaya dakasa baki ya Auri Wannan Y’ar mai Hankali, itace Matar Aure ba wa’innan y’an barikin ba. “Zamuyi Wannan maganar ba yanzu ba kubari mu gama war ware rashin da mukayi sannan shima Khaleel baya cikin natsuwar shi yana bukatar natsuwa, company su ma manager din ne ke kulada komai tunda ba Ahmed.
Dakin mommy su zarah ke lallashin ta domin sunsan koma meye ita tafi kowa rashi, har suka samu tayi shiru tana Ajiyar zuciyar, Shigowar kawar tata yasa tace kuna nan Hajiya? Eh kawata ai na canja shawara, nace ai basai na dauketa ba kawai tunda zumunci mukayi niyyar hadawa tun farko ko yanzu bata baci ba tunda kanin shi na nan sai a hadasu Auren gado kawai.
Kallon su tayi kawai domin tasan Waye Khaleel kuma yanzu bata isa ta tunkare shiba sai bayan komai ya natsa, amma Ajiye mata biyu irin Salifa da fauzy Abun Alfaharin tane a matsayin surukai.
Zarah ce tace, “ai yanzu saidai abari komai yanatsa kafin Wannan maganar ta taso, kuma Karku manta yanada wata Matar fauzy kuma kinsan Y’ar waye. “Badamuwa nidai inzai Aure ni zan zauna da ko mata goma ne Salifa tafada, domin itafa kawai tasa rai.
“Oh Allah kasa mu zamo iyaye nagari ga ya’yan mu Amen.
Kwana ki natafiya Naziya yanzu tana gidan su duk kayanta dake gidan ankwashe har wainda bata moraba, tafara warware wa Amma kusan kullum cikin yiwa Ahmed Addu’a take da sadaka idan tasamu hali, har Azumi takeyi litinin da Al hamis domin Allah yakai ladan kabarin shi. Khaleel kuwa haryanzu bai dawo dai dai ba, fauzy tayi binshi har tagaji bai komawa kanta, ko fuskar shi bata gani. Yau yana kwance a katon falon mommy ta shigo ciki ita kanta ta rame, “Ibrahim, wai kai wane irin yaro ne, yazaka sawa yarinya ido tun kawo ta gidan ku bayan kasan akwai hakkin ta akan ka, kai bazakayi koyi da halin d’an uwan ka ba, Ahmed dina ba haka yake ba, idan har kaunar da kakewa d’an uwan ka gaskiya ne Kayi koyi da halin shi.