AUREN GADO Page 11 to 20

“Comment share the free pages please and Wannan ne last free page ku biya ku karanta cigaban yanda zata kasance, ya za ayi da rayuwar Naziya shin zata Amince, shin zataso Khaleel, ya rayuwar su zata kasance da Fauziya, idan Naziya ta Amince da Auren Khaleel wace wainar mommy zata toya????? Muje zuwa yanzu za afara wasan this is just the beginning, let’s go my fans ????, ga masu bukatar biya kofa a bude take chart me up 09011251444
*Matar Soja*
????????AUREN GADO????????
*Matar soja ce*
Daga marubuciyar
KUSKURE NA
BARIKI AUREN SOJA
MUK’ADDARI
WANAKE AURE
ZANYI BIYAYYA Y’AY’AN GATA
And now AUREN GADO,
Ga masu bukatar Wnn littafi ku turo kudin ku ta Asusun banki na 7304736012 nafisa sani hassan Fcmb ko katin wayar ku ta Wannan number 09011251444, sai kuma y’an ???????? Niger ku tuntubi Wannan number domin biyan naku, +225 0748153903, littafina Dari biyar ne kacal 500 sai najiku nagode,
2⃣1⃣&2⃣2⃣
……………. Tuki yakeyi cikin kwarewa tareda bin k’aidar hanya, ya riga yasan hanyar gidan nasu Naziya, tunda yazo sau biyu, har kofar gidan ya isa, lokacin yana mak’il da Almajirai, da Alama Malam na gida, fitowa yayi yana wani irin sheki da haske duk da ya rame saboda mutuwar d’an uwan shi, wani Almajiri ya Kira yace yamai iso wurin Malam yace mai Ibrahim ne kanin Ahmed, ko minti biyu ba ayi ba saiga Malam cikin fararen manyan kaya, tsohon akwai tsafta da kwarjini, yayi saurin dukawa zai gaida shi, a’a Ibrahima tashi shigo daga ciki,
Har tsakar gidan yajashi domin zauren akwai mutane, yanayi yana kallon tsarin wurin Wanda zuciyar shi ke ayyana mai komai, tsakar gidan akwai inuwar bishiya wadda a karkashin ta aka samai kujera ya zauna Malam ma ya zauna suka gaisa kafin Matar k’irki ta fito, d’an dukar da kanshi yayi ya gaidata ta Amsa tareda yi mai gaisuwa, kafin Malam yace Hauwa Kira min Naziya, kafin nan shukrah ta kawowa bako ko sobo ne mai sanyi. Wani irin lugude yaji zuciyar shi tayi jin ankira sunan ta, ta’ aziya Malam yakuma yi mai tareda fatan Samun Rahamar ubangiji, yabishi da nasihohin da duk in zakazo wurin shi sai ya maka su. Shukrah ce ta kawo zobo mai sanyi a tsaftataccen sabon jug cikin na Naziya, ta Ajiye tareda gaida shi tayi gaba,
Fitowa naziya tayi cikin katon hijabin ta, kana ganin ta kasan ta rame sosai,
Sallama tayi, ya dago kanshi suka hada ido, Wanda tunda akayi rasuwar daga ita harshi basu hadu ba.
Allah ya gani bata son shan inuwa daya da gayen nan don kawai yaci Albarkacin Ahmed ne batada yadda zatayi dashi, Amma tunda yanzu mai rabawa ta raba shikenan ta huta,
Gaida Malam tayi batada niyyar gaida shi, saida Malam yace ga kanin mijin ki naziya, dama Ina so in samu lokaci muyi magana daku dukan ku, akan wasiyar da mijinki yabari, wani irin faduwa gaban su yayi duka shi tsoron reaction dinta yakeyi ita kuma batasan wace wasiyya bace.
“Ibrahim Alhaji Amadu yazo min da maganar kuma ni bazanyi jayayya da wasiyyar mamaci ba” don haka yanzu magana na wurin ku, Naziya mijinki yabar wasiyya d’an uwan shi ya Aureki, don haka idan kinfita takaba sai adaura muku Aure.
Wani irin kukan tasa tareda zama gaban Malam d’in. Kallon lafiya Malam ke yi mata, shikuwa wani irin tsalle zuciyar shi keyi saboda fargaba, “Malam don Allah karka Yarda nidai bazan koma gidan su ba, ni bazan yi Aure ba ni bana ma son shi kawai abarni haka, ni karatu nakeso inyi don Allah Malam karka hadani dashi.
Tashi kibani wuri Naziya banson shiririta, yaushe kika canja hali haka? tashi kafin ranki ya baci, wucewa tayi da gudu dakin Inna, Malam ya kalle shi, Kayi hakuri kaima bansan naka ra’ayin ba, Amma tunda kaine namiji in har ka Amince Naziya ita ba Matsala bace, kaje Allah ya maka Albarka yajikan d’an uwan ka, Ameen yace kawai zuciyar shi na wani suya, maganar ta ta bata son shi really touch his heart, wani irin zafi yakeji a kirjin shi, cikin dauriya yace Malam Wannan filin nakusa daku yaya Ahmed ya siye shi da sunan zai gina maka dakunan Almajirai batareda sanin kowa ba, bayan rasuwar shi Nagani a rubuce ya gama biyan contract din komai Allah bai nufa ya yi ba, inaso Inturo su, su duba yadda zasu tsara komai zanbar komai kafin intafi, zanje domin shigo da wasu kaya,
“Allahu Akbar Allah ya jikan shi yasa mutuwa hutuce a gareshi” Allah ya Albarkace ku baki daya. Ya Amsa da Amin, ya tashi yana farin cikin zai fara cikawa d’an uwan shi burin shi, duk da yatafi da ciwon maganar Naziya.
Bayan tafiyar shi ya kira Inna kulu da Naziya, ranshi a bace yace “Hauwa bansan cewa zan haifi yaron da zai yi musu dani ba, yau Naziya ke da nake yabonki kike kokarin watsamin kasa a ido, a gaban yaron nan kice bakya son gidan su bakya son shi, a Ina kika koyo Wannan d’abi’a? “Subuhanallahi Naziya me nake shirin ji”? Inna ni dai Don Allah ku yafemin Amma ni bana son komawa gidan nan nayi hakuri batareda nayi wa kowa korafi ba, yanzu idan na koma mutuwa zanyi, wallahi bana sonshi baida hali ba irin Ahmed bane, malam baka san shi ba.
Toh Hauwa tariga ta girma Y’ar taki, ni bazance komai ba tunda ta isa da kanta. Yafada tareda tashi yabar gidan kawai, a tarihin rayuwar shi itace ya’ ta farko data farayi mai musu da gaddama.
“Naziya me kikeso ki yi”? Kin taba ganin ko Y’ar nan malam ya yi magana ta amsa shi bare ke? Wane irin abu ne nake gani ni kulu yau? “Allah Inna bana son shi ya zan iya zama dashi ni dai bazan koma gidan nan ba. Ta tashi tana hawaye tareda shigewa dakin su, kwalawa shukrah kira Inna Tayi, “gani Inna. Kiramin Y’ar nan a waya. Tasan wa take nufi don haka takira Aunty Raliya ta bata, Inna tace “kuzo kuyiwa Y’ar uwar ku magana ta canjo hali, nan tafada mata komai, tace karta damu za tazo tayi mata magana ita da Aisha. Dakin su ta koma tana kuka, tareda kudurin duk Abinda zai faru sai dai yafaru bazata taba Auren Khaleel ba, saboda tun farko jinin su bai hadu da juna ba, tayi hakuri ta zauna da Ahmed saboda tana son shi, Amma bazata taba Y’arda ta zauna da Khaleel ba, wai ma yaza ayi ta yarda da Wannan kwamacalar, bayan agaban shi yaga yanda Ahmed yake nuna mata so lokacin da suka samu sarari,
Shigowa shukrah tayi tace “Aunty wai fadan me Inna takeyi yi miki? Kuka kikeyi me yafaru? Rungume shukrah tayi tareda jin wani sabon kuka, “Shukrah bana son shi. “Waye bakyaso Aunty? ” Khaleel, I hate him, bana sonshi wallahi bazan zauna dashi ba. “Ni Aunty bansan me kike fada ba.
“Ya za’ayi kisani tunda Auren ya koyo mata taurin kai, Naziya ki rufawa kanki Asiri karki wahalar da kanki a banza idan Malam ya karb’i lamarin nan ba mai canja shi, don haka na hore ki kiyi biyayya ki gama lafiya shine kawai.
Hadiye kukan ta tayi, dif jin fadan Inna, Shukrah ta tashi tabar dakin domin tasan ba hurumin ta bane, zama Inna tayi gefen ta tafara yimata nasiha akan bin duk abinda Malam ya zartar, shiru kawai tayi domin bata saba jayayya da iyayen ta ba, Amma zuciyar ta bata lankwasu ba, Sam bataji zata iya zama da wani kanin mijin ta ba, dama wani ne ba Wannan ba.
Yana tuki yana tunanin kalmomin ta,” ni bana son shi. Kalmar datafi kona mai rai, don haka speed ya Kara, saida yagan shi cikin gidan su ya fito a zuciye, ya matsu gari bai Waye ba yagan shi yabar kasar nan, kwabewa yayi tareda watsar da kayan jikin shi ya zube akan kujera zuciyar shi mugun zafi da turiri takeyi, she is the first girl da ta kalli tsabar idon shi tace bata son shi, huci yake fesar wa saboda zafin zuciya.