AUREN GADO Page 11 to 20

Har zuwa dare ya kasa bacci shi kadai yasan ciwon zuciyar shi, a kwance yake dagashi sai boxer jikin shi na sheki kadaicin d’an uwan shi kawai idan aka barshi dashi wani Abu, amma yana ganin duk duniya ba wanda zai iya fahimtar halin da yake ciki, how he wish yayan shi na tare dashi, yafi son rayuwar shi fiyeda soyayyar Naziya, wadda ya Amince ta kashe shi akan yarasa d’an uwan shi gwara shi ya mutu, saboda yanzu ma ba Amfana zaiyi ba don ya dade da sanin bata kaunar ganin shi.
Turo kofar da akayi ne yasa yadago kanshi, fauzy ce, ta shigo cikin Sanyin jiki fuskar ta sharkab da hawaye, tana sanye cikin kana nan kayan bacci, kusan duk komai nata a bayyane yake Wanda shi ba abunda ya burgeshi ciki, domin zuciya ma saida natsuwa take samun wani feelings, halin da yake ciki ko tsirara ta shigo gaban shi ba tashi zaiyi ba.
Zubewa tayi kan jikin shi tasa mai kuka mai ban tausayi, “meye illa ta, meye aibuna da ka kasa bani koda sakon zuciyar kace? Khaleel Ina sonka why ni baka sona? nayi hakuri da duk wani halin ka, yau kusan sati biyu Auren mu ba wani kulawa baka ko zuwa gefen da nake, Khaleel nifa mutum ce Inada jini, ni lafiyayyar mace ce, dole in bukaci mijina please tauye hakkin yayi yawa, sannan me nakeji? Auren Naziya? “That village girl”?.
Tunda take magana jikin shi yayi mugun sanyi, yes she is right ba ruwan Ubangiji da halin da yake ciki, tunda igiyar Auren ta na wuyan shi bai kamata ya watsar da hakkin Allah ba, amma this her last statement mess up things. Wani irin wancakalar da ita yayi kasa tareda mikewa yana nuna ta da yatsa ” look that girl, I value her more than you, she is more important to me right now, karki sake inji wani mum munan kalma daga bakin ki akan ta, duk wani Abu da ya shafi d’an uwana yanada muhimmanci A rayuwa ta, ko a mafarki naji kin kuma kiran ta village girl sai na saba miki.
Tashi tayi tareda girgiza kai ” lallai Khaleel, tell me, yaushe kafara sonta? This is not About yaya Ahmed ,this is about you, yes saboda naji yanda kukayi da salifa why kaki Amincewa da salifa ka amsa Naziya, why?
Zaburowa yayi ya nufota kamar zai shake ta, “baki Ajiye ni ba so don’t question me again, kuma kije kiyi duk tunanin da zakayi I don’t care, one last thing, in kinga ban Aure taba sai in bana raye, idan zaki iya zama ki zauna idan bazaki iyaba see your road. Yafada yana nuna mata hanya, juyawa tayi da gudu tafita ya bita da tsaki tareda cewa “useless.
Dakin momy tafada har bacci ya dauke ta Wanda ta dade batasamu tayi irin shiba domin rasuwar Ahmed, yau ma da taimakon maganin hawan Jinin da Aka bata ta samu yadan dauke ta, fadowar datayi tareda buga kofar yasa ta zabura tareda dafe kirji tana jin bugawar zuciyar ta yana karuwa, “kalu innalillahi, ke Fauziya lafiya kika bugamin kofa tareda fadomin daki kamar y’an fashi.
Kuka tasa mata mai karfi, kince zakiyi mai magana gashi yace sai ya Aureta, ni wallahi bazanyi kishi da yar talaka ba kuma Y’ar kauye. “Oh yanzu bazaki iya bari muyi maganar da safe ba? kinga bacci nakeji. “Allah bazaki runtsa ba Indai ni bazan runtsa ba.”Toh baki Yarda dani bane Fauziya? nice fa, bazan taba Amince wa a hada min iri da jinin talaka ba, saboda soyayyar da Ahmed ke mata ya fadi ya mutu yabar ni don haka bazan Yarda ta dawo ta karasa min gudan da yarage ba, kina ganin Y’ar nan kinsan ta gaji maita daganin ta mayya ce.
“Ni Ina ganin yana sonta ne fa. “No no no ba wani so, yaushe d’an uwan nashi ya mutu ke baki san soyayyar dake tsakanin shi dashi bane ko Auren ki ya karba saboda sa bakin Ahmed badon niba, a duniya Khaleel zaiyi komai saboda Ahmed Inada Wannan yakinin, don haka kicire zancen Khaleel zaiso yarinyar nan bayan yanada mace kamar ke. “Hmmm ni ai baya sona kema kin sani Khaleel baya son kowacce mace baida lokacin mace, Ina tsoron ranar da zaiso wata irin su basu iya fadawa soyayya ba, ranar za ayi biyu kuwa domin zan iya kashe macen da duk Khaleel yaso, ni nayi dakon soyayyar shi don haka idan har akwai wadda Khaleel zai so to nice.
“Naji zo ki kwanta a nan don girman Allah kibarni in kwanta maganin nan aiki yakeyi ajikina. Da k’yar ta samu ta kwanta sukayi bacci.
Asubar Fari yabar musu kasar su batare da yajira sun tashiba, maid ya fadamawa tafada ma mommy ya tafi, Wanda saida tayi kuka sosai lokacin da yarinyar ta fada mata, wani gefe tana mai kewar Ahmed yaro mai biyayya, “Allah ya jikan ka yaron kirki”, zabin ka ne kawai ya sabawa ra’ayina Amma kai d’a ne nagari Ahmed, Allah yakai haske kabarin ka.
Koda ta nemi wayar shi, lokacin yayi nisa a sararin samaniya, Wanda yatafi da kewar Abu biyu, Wanda yana fatan kafin yadawo yarage tunanin su domin samun zaman lafiyar zuciyar shi.
Gefen Naziya haduwa sukayi washe gari Wanda Aisha tabi bayan Naziya tareda cewa “gaskiya Innan mu Ki cire kara ki fadawa Malam gaskiya kar ya Yarda da had’in nan, domin tasha wuya a gidan nan batareda mun fada muku ba, nidai bana goyon bayan ta Auri wani kanin mijin ta, wane dadi ta tarar a gidan mijin nata da zata koma cikin shi?.
“Toh madallah naji ku kuma nasan inda tasamu zuga, Wato dukan ku kun canja hali banida labari? Malam ya fara fada kafin ya karaso ciki ya zauna, “Hauwa, ki zama sheda, da farko bani nayiwa Naziya zabin mijin ta ba duk da a Musulunce ni keda hakkin zaba mata mijin Aure a matsayin ta na budurwa, banyi hakan ba, can suka hadu dashi tace taji tagani, duk Abinda ta fuskan ta a gidan Aure kaddarar tata rayuwar kenan, kuma yanzu mijin ki ya tafi yabar wasiyya akan d’an uwan shi ya Aureki na fita hakkin ki a matsayi na na mahaifin ki ba neman shawarar ki nakeyi ba, Agaban ido na da na yaron nan ki kace wai bakya son shi, saboda rashin da’a, to ki rubuta ki Ajiye Indai Ina numfashi, daga ranar da kika fita takaba daga ranar zan daura miki Aure da Ibrahim don Allah Naziya kifito ki nunawa duniya ni Malam Abu nayi miki Auren da bakiso, don haka nagama magana. “Kayi hakuri Malam” inji Inna da sai yanzu ta fara magana, don Allah karkayi wani dogon tunani kazartar da duk Abinda yake dai dai, nasan duk hukuncin daka yanke kana da taka hikima. “Malam Kayi hakuri kokarin lallashin ta mukeyi wallahi. Inji Raliya, tashi yayi kawai ya kade babbar rigar shi ya fita, Wanda sai lokacin tasaki d’an karamin kuka tareda toshe bakinta kar Malam ya jita, “Akul Naziya, Aure na sama da shekara talatin idan kikaja min bacin rai saboda boyayyan bakin halin ki bazan yafe miki ba. A’a Inna ya haka? don Allah karkiyi saurin yimata baki. Inji Raliya, ba baki nake mata ba dawo da ita nake cikin hayyacin ta. Rarrafawa tayi da sauri ta rike kafar Inna. “Na tuba Inna wallahi bazaki kuma jin nace wani Abu ba akan maganar nan, ba zan kuma musu ba, ki yafemin don Allah Inna. “Allah yawa Rayuwar ku Albarka baki daya, Aisha kirika hakuri ke babba ce a saman ta in bazaki kwantar mata da hankali ba karki nemi tayar mata dashi.
“Afuwan Inna kuyafe mana. Tashi tayi itama tabarsu a cikin dakin, suna Kara tausar ta. Matsowa Raliya tayi tareda dafa ta tace ” ki share hawayen ki, jikina nabani Naziya zakiyi farin ciki fiyeda Auren ki na farko, kinsan me? Girgiza kai kawai tayi badon tana farin ciki ba sai don tana gudun bacin ran iyayen ta, “saboda Khaleel daban yake bazaki gane ba sai nan gaba keda kanki zaki fadamin. Allah kadai yasan Abinda ke ranta amma ita tasan bazata taba son Khaleel ba domin jinin ta da nashi bai hadu ba, zaman ta da Ahmed soyayya ce sanadi Amma shi tasan zama ne bamai dadi ba. Haka suka wuni suka tafi gidajen su, Wanda daga nan ta Kama kanta tareda dukufa Addu’oi akan mijinta.