AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 21 to 30

Ta kureshi kamar ya dora hannu akai yakeji ya kurma ihu cikin sauri ya duro tareda fisgota rashin sanin madafa yasa ya cafke bakinta da ke fadamai Abun haushi yafara tsotsa cikin mugunta harda ciccizawa yakeyi idanun ta a waje ga zafi gashi takasa ture shi saida yayi son ranshi ya tureta tareda nuna ta da yatsa, ” karki kuma furtamin kinyi Auren soyayya a rayuwar ki me kike nufi da nawa Auren, what is wrong with me? Niba namiji bane ko bankai ki soni kiyi kishi na ba? Look ni inada kishin Abinda yake nawa koda ace ke zabin Yaya na ce now you are under me, ikona ce ke you must love me, dole kiyi kishina dole. Yafada yana fita saboda takaici yarasa Ina zai saka ranshi kishin ta yayi yawa a zuciyar shi,koda yayan shi ne ta Aura Abun na tabashi kuma duk da yasan ita din tashi ce zuciyar shi taki convincing dinshi sai ranarda yaga tazamo shi yazamo ita, don haka he is ready to make her his completely. 

Zama yayi tareda yin dariya, this guy is strange, kalli yanda yake reacting itafa ta ma gano shi yanzu kamar yanda yake fada akwai boyayyen Al’amari a kasan zuciyoyin su ita mace ce don haka bazata taba bada kai da sauri ba dole shine zai sauke wannan ego din ya fada mata zuciyar shi, tagano shi fiyeda yanda yake tunani, tana sane da kalaman fauziya akan yaki kusantar ta, ace mace wayayya like her yakasa kulata Amma ita daren farko yanuna mata shifa namiji ne kuma yanada lafiya, Wanda ita sheda ce domin idan ya rikice mata har tsoro takeji. 

Part din Mommy ya nufa Wanda yayi dai dai da shigowar motar kawun su, yayi saurin boye fushin shi ya nufeshi, suka gaisa yace ” muje cikin gidan Ina Hajiya”? Mommy na ciki Ya fada suna tafiya, tana zaune a falon tana kada kafa, suna sallama ta mike tareda cewa ” gwara daka iso domin jini na nagab da hawa saboda bakin cikin khaleel. Kallon ta yayi kawai domin yasan korafinta baya karewa, mommy me nakuma yi kince in Amince da zancen Auren salifa koda bana ra’ayi na Amince now what? Oh fadamai kakeyi nice nasaka khaleel nagode kaji shiyasa nake kukan Rashin Ahmed. Tasa kuka, tareda zama, kawun nasu ma zama yayi ba tare da yace uffan ba, saida sukayi shiru yace ” Toh nidai nasaba da mugayen kalaman ki balkisu ba tun yau ba idan na yanke hukunci akan yarana kice namiki shishigi kuma idan fitinar ki ta tashi sai kin nemo ni kuma kinsan bakina ba shiru zaiyi ba, don haka ni na isa nace khaleel bazai yi irin Auren da ki ka yi wa Ahmed ba, kina maganar nadama Hajiya balkisu har yanzu baki san Annabi ya faku ba, da zaki gano ita wadda kikeso din ranar da kika Aurota aranar ya Kwana asibiti, da Naziya ce da baki kauna da kince itace ta kashe miki yaro, Amma da yake bakya tsoron Allah kinyi mukus, yanzu ko mutuwar Ahmed bai isheki ishara ba, duk bakiga ya dace ki kyale komai ki barwa Allah ikon shi ba, naji kin kashe Auren da kika kulla ba tare da yaro ya Amince ba tun farko, wannan badamuwa ta bace yarage naki Allah ne ke nuna miki komai cikin sauki inda ke mai kwakwalwa ce Amma toshashshiyar madiga……. “Ya isheka Muhammadu”, don bazan ce Alhajin ba, ko ince modu kamar yanda kowa ke kiranka tunda kaki Kama furfurar ka, kuma kuji nan, wallahi in har ban Aurawa khaleel salifa ba sai in ba na numfashi, kuma kai kaji idan baka Aureta ba banyafe maka ba duniya da lahira mu zuba ni da ku shege ka fasa. Ta mike fuuu ta shige dakinta tareda mugayen kud’uri, “kawu kaji me tace? Ya fada cikeda damuwa domin kalmar ta girgiza shi, naji khaleel kuma mahaifiyar kace bamuda yadda zamuyi da ita, sai Addu’a, yanzu dai ya za’ayi? Ko ka Amince ne a daura Auren? “Eh kawu ayi mata yadda takeso ai ba akaina zata zauna ba, 

Yafada tareda ayyana wani kud’uri a zuciyar shi, Wanda shikadai yasan tsiyar da ya shuka, haka ya raka kawun shi tareda zancen zai samu iyayen yarinyar ai shi namiji ne zai iya rikesu duka don haka karya damu, koda kawu ya tafi bai iya komawa part din Naziya ba, dakin shi na nan ya shiga ya canja tareda barin gidan, 

Direct gidan malam yaje………. ????

*Matar Soja*

3⃣7⃣&3⃣8⃣

08032252760

08175479641 contact this numbers for more information 

……….. Sun dade suna tattaunawa da malam akan rayuwa Kafin ya koromai zancen Karin Auren da Momy keson yi mai, Sai da yayi shiru malam yace “yanzu meye matsalar ka? Baka da muhalli ne, ko baka iya daukar nauyin mata biyu ne? Kuma meye dalilin sakin ita dayar Matar taka ba akan ka’ida ba? Yanzu dai nasan ba mata hudu ba Kanada karfin da zaka ciyar da Unguwa guda ma, sannan lafiya kana da ita, sauran ka Adalci, karike Amanar su tsakanin ka da Allah kabi umarnin mahaifiyar ka kasamu tsira kamar d’an uwan ka. Haka suka dade sai karfe kusan biyar yabar unguwar, tun fitar shi take jin ba dadi domin ta saba dashi yanzu tafara sanin dadin Aure zaman ta da khaleel, shine ya nuna mata ita mace ce mai daraja da lafiya a tareda ita, domin duk lokacin da ya kusanto jikinta bata iya misalta dadin da takeji hade da nishad’i, kewar shi ta dameta sosai har waya ta dauka sau ba adadi’ tana dubawa tareda tunanin kiran shi sai takasa, to me zatace mai inta Kira? Ganin zata damu da yawa yasa ta janyo wayarta ta fara karatun littafin ta, y’ay’an gata yasata cikin nishadi’ sosai, saida taga yamma yayi ta mike ta shiga kitchen, ta shirya mai dinner lafiyayya irin wadda tasan yakeso, Kafin tayi wanka, duk Abinda takeyi a yanzu bin zuciyar ta ne domin tana samun farin ciki ba tare da tayi tsammanin samun shi ba a cikin wannan Rayuwar Auren. 

Yana tafe a hanya yana duba waya, wato ba zata iya neman shi ba koda zai shekara baya gidan? Don haka saida yayi magrib ya shigo cikin part din, lokacin tayi wanka ta saka simple gown tana zaune tana lazimin ta, ya yi sallama ciki ciki, tareda wucewa gefen gadon ya zube rigin gine, nasihar malam ta ratsa shi Amma baya jin kudurin shi zai canja sai dai ya kiyaye fadawa halaka Wanda yasan duk ta inda zai bullo ma Al’ amarin, saida ta kammala ta mike tareda juyowa tace sannu da zuwa. Bai amsa ba bai bude idanun shi ba, harta juya tafita, saida ta juya yabita da kallo tareda sauke Ajiyar zuciya, ya tashi zaune yana shakar kamshin da tabar mai, 

Shigowa tayi dauke da tray, binta yayi da ido kur harta Ajiye akasan gadon kan small carpet, baice uffan ba, tace ” ga Abinci. ba tare da ta kalle shiba, “come here”. Yafada cikin bada umarni fuskar shi a hade, ta dago kai, kallon da yake aika mata kamar yana Amfani da igiya yana janyo ta ne, ba musu ta mike, remove that hijab. Ba musu ta cire tareda ninkewa ta juya ta Ajiye inda take Ajewa, duk yana binta da kallo wani irin nishadi yake jinshi a ciki a duk lokacin da suke tare, dawowa tayi zata koma kasa ya riko hannun ta tareda janyo ta ya dora kan kafar shi, ” kina wahalar da ni da yawa fa” Ya fada yana mai dora hancin shi a wuyan ta, kamshin ta mugun rikita shi yakeyi, 

Nafita baki damu ba, nadawo kin nuna baki yi kewa ta ba, bayan rabin zuciya ta na nan tunfita na, Ina tunanin ki nadawo ba hug ba welcome back kiss umm why kike horani? Never mind gobe zakiga Amarya ta am getting married again. Yafada tare da dago idanun shi ya na kallon kwayar na ta idon domin yaga reaction dinta, Wanda Sai da taji zuciyar ta tayi wani irin tsalle kamar zata fito, kalmar ta caketa fiye da tunani, kallon are you serious? take mai, Wanda ya ganota domin yana karantar kowane movement dinta saboda ya gano ainihin meke ranta, ” am serious, am getting married, Salifa zan Aura gobe insha Allahu, ai badamuwa ko? Tunda kinga yanda Auren ki yazo ba shiri haka nata ma All this romance karki damu I can handle but for you. Wani irin zamewa tayi ta sauka kasa tareda fasa kuka mai karfi ba tare da ta shirya ba, jitakeyi idan batayi ba zuciyar ta zata fashe, zancen romance da wata, kwakwalwar ta bazata iya dauka ba, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button