AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 21 to 30

Batasan me yasa zuciyar ta ke ingizata zuwa gareshi ba, don’t blame her, domin khaleel ba irin mazan da zuciya ke iya jawa aji bace duk ego din Naziya ya hambarar cikin sauki, Wanda shi a gefen shi yasan ba zata zoba don haka juyi yayita yi kafin ya zabura ya iya watsa ruwa ya dawo dai dai, mommy ce cike da farin ciki ta turo kofar dakin nashi lokacin ya shirya cikin wata dakakkiyar shadda green tana maiko sumar shi yake tajewa, fuskar ta a Washe tace d’an Albarka bazaka fadamin a nan ka Kwana ba? Aida tuntuni an kawo maka breakfast, yanzu zoka ci kaji. Tafada tana ajiyewa a kan gadon, ” good morning mommy. Yafada yana zama gefen ta, ya riko hannun ta, he love her but he hate her ways of thinking, takasa gano illar Auren da zatayi mai, saida yaci yagama tanata tsaro mai zancen Auren tareda cewa “nasan zaka dawo hanya ai don kaima kasan baka kyautawa rayuwar kaba khaleel duk fadin kano an san da arzikin ubanku tun yana raye bare yanzu da kuka Kara bunkasa kuka ginu ace baka Auren Y’ar da duk kano zata dauka asan yes kayi aure nima infita anuna ni ace ga surukar wane kuma uwar wane y’ay’an ka su fita a nuna su ace jikokin wani ne a garin kano ai shine farin ciki. Saida ta gama yasa tissue ya goge bakin shi ya juya dakyau ya kalleta ya riko hannun ta, ” Mommy na meye laifin Naziya? Tana da mugun haline? Gidan su ba tarbiya ne? “Talauci ne banaso kasani bankaunar hada iri da talaka shiyasa nafada maka karka sake ka hadomin jini da talauci. ” Hmmm mommy meye ribar Auren fauziya danayi? Meyasa kike so ki hadani da salifa? Mommy I don’t want to argue with you, banaso kice na bijire miki amma ni har a abroad nasha ganin ta tana yawon banzan ta,…. “Dakata, sunada kudi Ina kakeso ka gansu a Zaure da Almajirai ko suna kulle a gida bayan sunada Abinda zasu huta? ” mommy understand yarinyar nan gwara fauziya da ita you… “Quit Ibrahim Aure dai yau sai andaura kuma yau zata tare yau nake so ka shiga dakinta domin jikoki nake so daga tsatso mai daraja ba gidan malamai ba. 

Mikewa yayi OK sai tazo tayi gadi tareda zaman jiran agama budar kai, ai al Ada ce mai muhimmanci dataja har yayana yabar duniya baisan dadin Aure ba. Ya dauki key ya fita abin shi, yabarta sake da baki, khaleel baya wani ganin girmanta take gani baisan mutuncin taba kamar Ahmed, “Allah ya jikanka yaron Albarka”. Tafada tana share hawayen kewar Ahmed tafita da kayan Abincin da yaci. 

Yana fitowa tana fitowa cikin adon ta mai daukar hankali, tayi matukar tafiya da hankalin shi, saidai ganin mai gadi da masu aiki dake kai kawo yasa yaji wani irin mugun kishin ta tuni ya hade rai yayi saurin cewa ” go back, cikin kausa shashshiyar murya, mai cikeda umarni da tsantsar kishi, yayi saurin rufa mata baya, domin bata tsaya wata wata ba ta juyan saboda yanda fuskar shi ta juye kamar bashi bane dazu yake kwantar da murya a waya, a tsaye ya ganta ya doge daga nesa, ban lamunci ganin adon ki awaje da rana ba bayan kinsan akwai gardawan banza a ko Ina, wallahi zakija musu asara idan kika kuma fita batareda hijabi ba, ke ki nemo nikab kirika sawa if necessary sai kinfita da rana. Ya juya ranshi a bace, by the way, Ina ma zataje? Ya manta y’an da sukayi da ita a waya saboda kishi, 

Yana tuki yana dukan sitiyarin motar shi, saida ya koma gefe ya faka motar ma ya kife kanshi, bai taba tunanin yanada zafin kishiba sai akanta, zuciyar shi har wani tsalle takeyi, kuma gashi dole ya fito da ita ayi mata passport, domin shi kadai yasan shirin shi, dukan iska yayi, Allah yagani bazai kawowa wani katon banza Matar shi ta tsaya yana kallon ta cikin camera ba zai iya shake shi, wayar shi ya ciro tareda kiran manager dinsu yace yaza’ayi asamu mace photographer tazo tayiwa madam a gida? Yace za’asamo mai yau, yayi Ajiyar zuciya tareda kiran ta, kamar jira takeyi dama tunfitar shi take dariya kishin shi ma dariya yabata domin tana tunanin bayau suka saba ganin taba a gidan, wani irin farin ciki takeji a zuciyar ta now she relax domin inda kishi da so, don haka tanaji a jikinta yana sonta domin Abinda yakeyi da ita yafi karfin wasiyyar d’an uwan shi, tanata tunanin moment dinsu dashi taji karar wayar da yabata, mikewa tayi da sauri ta dauka don shikadai ke kiranta da ita, picking tayi tareda yin shiru, saida yaja numfashi yace “am sorry for shouting at you diamond, kin tashi kishin da bansan ma dashi ba do you know, you look very pretty and beautiful? “Sorry ai kai kace inzo insame ka. Tafada cikin Y’ar shagwabar da batasan daga Ina tafito ba, “Hmmm really babe wurina zakizo Yafada jikin shi na rawa saboda farin ciki, yes dole inbi umarnin ka domin Aljannah ta na karkashin kafarka Ina gudun tsinuwar ubangiji. 

Ajiyar zuciya yayi tareda hamdala, ba Abinda yafi ka Auri macen da ta ginu akan addini a rayuwa. ” am coming back home soon my diamond don’t change that dress please zanzo inkalla in more, and am Ina mana wani shiri ne zan d’an dade kadan kidafa min lunch ki jirani a gefen Mommy, bye. Ya katse wayar yana tayar da motar cikin sauri, domin tun baije inda yayi niyya ba jiyake kamar ya koma saboda ya shiga jikinta yayi yanda yake so, yanzu ne zai samu damar da yake mafarki akanta domin tagama sakin jiki dashi sosai, “babe am coming for you get ready. Yafada yana jin yanda jikin shi ya mugun motsawa saboda ya kwadai tu, “control madam you get in don’t worry yourself. Yafada yana murmushi mai cikeda farin cikin da baya iya boyuwa, ko office da yaje kowa mamakin sakewar shi da farin cikin shi yakeyi domin tun rasuwar d’an uwan shi basu kuma ganin fara’ar shiba, fara’ar shi sai yana tareda Naziya, ita din wata bangoce mai yaye mai dukkan damuwa batareda tasan da haka ba, da bata a rayuwar shi ya rasa Ahmed saiya susuce, Ahmed yayan shi ne ubane kuma bango mai muhimmanci, Wanda bai tashi rushewa ba saida ya gina mai Wanda zai jingina yaji sanyi, itace Naziya, haske ce wadda mommy ta kasa hangowa farin cikin yaranta biyu Wanda take wa kallon banza ita ba Y’ar kowa ba, Addu’a yakeyi just once mommy ta gano Naziya itace surukar kwarai, 

Bayan sun gama wayar bata bata lokaci ba ta shiga cikin kitchen tareda zuba tagumi tana tunanin me zata dafamai da zata burge shi yau? Dariya tayi domin tasan me ta shirya a ranta, I will change you I will make you test our food our tradition today d’an China. Tafada tana dariya, don haka ta fara kokarin dora mai tuwon danyar shinkafa da kuma miyar taushe, lafiyayya, domin anzuba mata komai a gefen ta, tundaga kalolin namomi har zuwa kan kayan miya da duk wani Abun amfanin kitchen kamar part din Momy, don haka ta dage ta zage ta yimai lafiyayyan girki da yaji namomi ta kuma hadamai zobo domin ta lura yaji dadin shi ranar nan, cikin hour daya ta kammala ta zuba a new warmers masu kyau, sai tunanin yanda zatayi takai cikin gidan kamar yanda yace, zata jira shi first a nan har yazo ko zai Amince ya shigo cikin part din ta yazo yaci, tana gudun haduwar ta da Momy, batason cin mutuncin ta zagin da take mata yana mata ciwo a kullum don batada y’an da zatayi ne bata koyi yiwa babba rashin kunya ba kuma uwar miji dole ta kawar da idanun ta ta to she kunnen ta domin khaleel yana kokarin taka mata birki ba kamar Ahmed ba, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button