AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 21 to 30

Momy nacan tayi busy sai taya kawayen ta takeyi ana tsara gefen salifa, jinta takeyi a cikin farin ciki yau, duk yanda zatayi ta raba khaleel da Naziya sai tayi, haka malanin su yabata tabbacin khaleel bazai taba kusantar Naziya ba muddin tabashi Abinda yabata ta zuba mai a Abinci, kuma tayi nasarar bashi yaci, don haka batada fargaba yanzu target dinta shine yanda zatasa ya kula salifa, saida suka gama tsara gefen y’an da sukeso kafin su koma gefen ta su baje suna tattaunawa itada su Zarah, “Aunty yanzu hankalinki ya kwanta ko? ” eh zarah ai ni nasan banda kanwa kamarki, jini nane banaso ya hadu dana talaka kuma Alhamdulillahi wannan malamin yamun komai. “Toh Aunty idan kika hana khaleel kusantar Naziya kinada tabbacin zai kula salifa? “Kibarni dashi aiba shi ya haifi kanshi ba, ni zansa yaje gareta. ” Aunty khaleel ba Ahmed bane kinsani. ” eh kinsan ya akayi ya A mince da zancen Auren salifar? Toh kiyimin shiru zakiga mai zai faru. Rungume ta tayi tana dariya ” yayi Auntyn mu na Y’ar da dake. 

Yana hanyar shi ta komawa gida malam ya kirashi a waya, Wanda shine karon farko da yataba daga waya ya kirashi, yayi mamaki sosai saida ya faka ya kirashi back, suka gaisa cikin mutunci yace ” kazo gidana yanzu idan baka komai, muna tareda kawun ka yanzu haka. dafe goshi yayi ya manta ma da zancen Aure yasan kan maganar ne suke neman shi, don haka baida zabi haka ya burkita ya nufi hanyar gidan malam din, 

A zaune suke cikeda Almajiran malam manya, ya parker daga nesa ya karasa Wanda kamshi da haibar shi kawai zaifada maka shi din wani ne, kawun shi na gefe suna magana, ya tsuguna ya gaida su kafin ya zauna a tabarma, kanshi akasa, “Alhamdulillahi Ibrahim yanzu muka dawo daga daura Auren ka, Wanda nayi kokarin kiranka tun lokacin Alhaji Muhammadu yace inbarka kanada uzuri, Toh yanzu dai nauyi ya hau wuyan ka, mata biyu, sai kayi kokarin kwatanta Adalci, Allah ya tayaka riko. Wani irin bugawa kirjin shi yayi tunda Malam yafara magana, Allah yagani ya tsani salifar nan fiyeda ma fauziya, Adalci Hmm. Yafada a ranshi, yanaji har sukayi suka gama doguwar nasihar su, kawun shi ya mike yace shi yatafi gida sai sunyi waya, Malam ya kalleshi yace ” Ibrahim me yasa ku matasa yanzu kuke sakaci akan Addu’a, bakwa neman tsarin ubangiji tareda kariya a tareda ku, bayan kunsan akwai makiya da mahassada atareda ku a kowane lokaci zasu iya kawo maku hari, karkayi wani tunani ba Abinda ya sameka kawai ka rike Azkar ka kuma dage da sallar dare, Allah ya Kara tsare ku yakuma bada zaman lafiya. “Amen yace kamar dole sukayi sallama 

Yana wucewa malam ya Kira Amintattun Almajiran shi yace suzo zasuyimai sauka yanzu, ya tashi ya shiga cikin gidan yasa Inna ta girka musu Abinci mai yawa, harda kaji yasa aka Kama yace ayi miya, 

Inna tasan Indai malam yayi irin hakan to karya sihiri zaiyi Wanda tasaba, kuma ba ruwanta da bincike aikinta kawai takeyi don haka ta dage ta tado Shukrah suka fara aikin su………. ????

*Matar Soja*

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button