AUREN GADO Page 21 to 30

Wani irin dariya tabashi irin gudun data kwasa kamar ta riko maciji, ya rike tareda bajewa yana kyalkyala dariya…….. ????
*Matar Soja*
3⃣1⃣&3⃣2⃣
08032252760
08175479641contact this numbers for more information
Ya dade zaune yana bin kofar da kallo, “babe that’s our room tunda shi kika zaba mana. Yafada yana murmushi mai kayatarwa saida yaji ya d’an dawo normal ya mike tareda mayarda rigar shi bayan ya kalli yanda taja duk wandon yayi squeeze, cikin gidan ya koma tareda kiran maid yace tazo side din su ta hada musu breakfast idan tagama tayiwa madam magana tafito taci shi ya fita.
Naziya bata kuma fitowa ba saida taji bugun kofar maid tace “Aunty nice kifito ga breakfast. Bude bakinta tayi cikeda kasala tace ” ba kowane a cikin gidan? “Eh Oga ya fita yace ki karya sai ya dawo. Ajiyar zuciya tayi ta mike tareda cewa ” kije nagode. Saida taji ta tafi tafito falon ta dauki d’an kwalinta dake kan kujera ta kalli wurin tareda tuna what ever happened yanzu, mamakin shi takeji halin shi daban ya mugun canjawa kuma she understand know, khaleel bayaji domin ta lurada baiko tsoron kalaman momy like Ahmed dake mugun gudun fushin ta, zama tayi na tsawon lokaci tana tunanin banbancin halin su tareda irin nashi ra’ayin I don’t care, da kuma bin son zuciyar shi,
Sai karfe shadaya ta karya ta kwashe kayan ta nemi kitchen, yanzu ta lura komai na part din sabone bazata manta ba lokacin da Ahmed kenan ba wainnan bane a ciki, wainnan sunfi haduwa ko kitchen din kamar Aljannar duniya bare kuma bedroom din data shiga, kawai jitayi Abun ya burgeta taji tana son taga gidan baki daya, dakunan sunyi matukar burgeta duka sai daya dayafi kowane haduwa da shan ado ga akwatunan ta sunkai saiti shida masu kyau da tsada waldrp din ta bude taga yanda ya tsara komai kayane yan gida da waje birjik kowane side kaya daban harda iners kamar wani small shopping mall, samun fuskar ta tayi da saki ta zauna tareda zubawa ko Ina kallo tana tunanin shi just like that tafara hasaso rayuwar shi, daga jiya zuwa safiyar yau he changed all her thinking, duk wani baki nashi da take gani ya goge sai wasu kyawawan halayen shi dake maye mata gurbin duk wani kiyayya datakeji tashi, me ma yayi mata tunfarko? Takasa tunawa sai wata zuciyar ke fada mata kanin mijinki ne this is not right, girgiza kai tayi tareda tunawa da ya’yan manzon Allah da ya Aurar da ya ta mutu yakuma bashi wata itama ta mutu yace da da wata da zai kuma Kara mai, don haka tasani ba haramci a cikin Auren su sai dai zata dauki dogon lokaci kafin ta iya sakin jikinta dashi, karar wata sabuwar waya taji a gefen gadon ta mike tareda daukar wayar ta zuba mata ido kamar tana tsoro domin wayar nada matukar girma da kuma kyau, saida tayi ringing sau biyu ana uku tayi shahada ta dauka,
Shiru tayi domin batasan wayar waye ba kuma ba suna, “Hmmm madam kinga wayar ki kenan, that’s your phone ita zaki rike madam khaleel, and this is your husband number save it. “Nidai bana son waya inada tawa. Tafada cikin wata irin murya da batasan tafito ba. Ajiyar zuciya yayi yace ” Hmm you are my wife I can buy the whole iPhone company for you if you want, kinfi karfin wannan wayar, ni zanfada miki how wealthy I am, your husband is a rich man take it or leave it, but that the fact, and ki shirya very soon zamuje honey moon domin I have a lot to offer to you madam Ibrahim, I want to fulfill All my brother dreams, kullum so yake yi yaganki cikin farin ciki, bai samu dama ba, ni inada dama what ever you want just tell me I will do it right away, I don’t mind if you call me your savernt.
Kalaman shi sunyi matukar tasiri a zuciyar ta saidai kalma daya data tsaya mata da tasa ta bude baki batareda ta shirya ba, ” kanayin komai saboda Ahmed? Shiru yayi na d’an lokaci kafin yace “yes shine ya bani umarnin Aurenki, and bazan iya tsallake wa ba koda bana so zan iya takura rayuwa ta for my brother happiness. Kalmar batayi mata dadi ba taji wani iri Abun ya tabata wato saboda Alfarmar Ahmed yake Auren ta? “Me yasa zaka takura kanka kayi Auren da bazai taba Baka farin ciki ba? Ni baso nakeyi ba da kabarni na Auri Wanda nakeso. Wani irin d’aci yaji a kirjin shi, “Wanda take so? ” oh wannan Almajirin ko I no it, but last warning daga yau tunda igiyoyina na wuyan ki kar inkuma jin irin wannan maganar a kunne na, bazan dauka ba, any way is nice talking to you on phone, bazan dawo da wuri ba aiki ya rikeni daga lekawa office kinsan Yaya na keyin komai yanzu responsibilities sun hau wuyana da yawa,mata biyu gida uku Momy na office our business zaki taimaka min ai ko? “Mata biyu? Ta samu kanta da tanbaya batareda ta shirya ba kalmar ta fito, “yes two wife’s idan naga da hali salifa ma zata dawo kuzama ku uku but kafin nan zangina muku gidan da yafi wannan yanda kowacce zata wala.
Sauke wayar tayi, taji she can’t talk anymore just like that ta datse ta Ajiye,
Wayar shi ya bi da ido tareda cewa “what? Idanun shi a waje domin he can believe it, kishi takeyi batason kishiya? Or what? Tafara sonshi ne daga small touch daya bata daga jiya zuwa yau or what? Ko kawai ta gaji da magana dashi ne? So much question da yake bukatar Amsar su, dafe goshi yayi tareda cewa “babe if you are really jealous saboda ni I swear I will divorce fauzy I promise you, but I will find out first. Jinshi yakeyi kamar yayi tsuntsuwa ya bar office yagan shi agida this is very hard time for him he needs time saboda ita,
Ta dade rikeda wayar tana tunanin meke faruwa daga jiya zuwa yau, takasa kamo bakin zaren mikewa tayi tareda kwabewa ta daura towel domin tayi wanka kafin lokacin sallah, katon mirror din dake bathroom din ta zubawa jikinta ido tana kallon kirjin ta da yayi wani irin ja saboda murza, Ahmed ta tuna dayayi mafarkin tabasu har yabar duniya, tace you miss my Ahmed you really missed. Tuna yanda ya kafa soft lips dinshi akansu taji wani iri Abu nabin jikinta, yanda yake squeezen dinsu ta tuna, namiji baida kunya domin ita a irin zaman su za amutu bazata iya koda rike hannun shi ba Amma shi daga zuwan ta first night ya murjeta tsab a gado yanda yake so ko a kwalar rigar shi.
Saida ta kwashe kusan hour guda kafin ta fito ta samu kanta da murje ko Ina najikin ta da kamshi da mayuka masu tsadar gaske da gyara fata, ta fito zuwa cikin dakin, inda tasamu kanta da zabo wata doguwar rigar Abaya Baka mai d’an kwali kato ta ciro Iner wears ta saka masu kyau bakake suma ta zura rigar ta shafa powder da wet lips saboda ita irin matan nan ne masu natural beauty ba saida make up ba.
Nade gyalen tayi kamar balarabiya, fadin kyau da tayi bata bakine, hijabi ta dora a kai tayi sallah, ta dade kafin taji karar wayar ta, dauka tayi tasan shine domin ba Wanda zai kirata, ” madam nagaji kuma inajin yunwa, please set food for me and water for bath I will be home in fifteen minutes insha Allah. Batace komai ba ya datse kiran. Tashi kawai tayi ta nade daddumar ta fito zuwa cikin kitchen, ko Baka ra’ayi zakayi sha’awar yin girki a cikin wannan kitchen din, don haka ta baje tareda hadamai lafiyayyan dishes din da yakeci, Wanda gidan ya cika da mugun aroma, ganin zobo dasu Abarba taji tana son ta hada, domin ko a gidan su sana’ar inna ce, cikin minti shabiyar ta hada komai ta zuba kankara tareda zubawa cikin lafiyayyan jug ta saka a firij,