AUREN GADO Page 21 to 30

Gyara wurin takeyi tana tunanin ba wannan kudurin ta shigo dashi cikin gidan nan ba, duk Ina tsarin ta da kuma kiyayyar Auren khaleel daga jiya zuwa yau ya zage ta girka mai Abinci, and this wanka, no ba saboda shi bane saboda ta bi maganar iyayen ta dasu Aunty, kuma tana tsoron wutar Allah, banbancin mutum mai ilimi da jahili kenan, Wanda shi kullum idan zai aikata laifi yasan makomar shi amma jahili yi yakeyi batareda tunanin gobe ba, don haka Allah yabamu ikon aikata mai kyau.
Motsin da taji ne yasa tayi saurin Ajiye towel din da take goge goge dashi, a tsaye yake ya nade hannu tareda zuba mata ido kamar zai cinyeta tayi mai matukar kyau ga wani irin Aroma da yayi mai welcome tun shigowar shi falon, dukar da kanta tayi duk ta diririce domin duk ya cika mata ido da kitchen din, ga wani killer smile da yake watso mata Wanda ke Kara hanata tabuka kudurin zuciyar ta. Ganin ta daskare ya bude hannun shi Alamar tazo gareshi ta ki tareda juyawa ta bashi baya. “Ni dole inzo madam bazan iya ba ai. Yafada yana cire hannayen shi a saman kirjin shi ya fara taku a natse har wurin ta bai yi wata wata ba ya zagaye west dinta tareda dora habar shi a wuyanta yana lumshe idanun shi. “Wow wannan kamshin daga cikin gidan ki har kitchen din ki, Hmm I can’t express, you are amazing, you are beautiful adorable and Angel from god Alhamdulillah, kinsan ance wai idan namiji yazo gida ya tarar da Matar shi duk gajiyar shi na bajewa, Amma ni ba haka bane, duk lokacin da zanganki jikina Kara mutuwa yakeyi you are my weakness.
Kalmar tayi matukar tasiri a zuciyar ta, sannan yanda yake magana hucin shi na bugun gefen wuyan ta tuni ya saukarwa da nata jikin kasala, she can swear shine weakness dinta domin duk lokacin da ya matso gareta ta tashi aiki, sun dauki lokaci idanun su a runtse yace “A bani Abinci am hungry. Saurin cire hannayen shi tayi ta matsa tareda daukar tray ta bude firij ta dakko jug dinta ta dora mai komai yana kallon ta har tafita gefen kitchen din da ke daukeda dining ta Ajiye yana biye kamar rakumi, jan kujera yayi ya zauna tareda cewa ” nafa gaji kezaki ciyarda ni da kanki. Dago kanta tayi tace ” Aa ni bazan iya ba.
Kasheta yayi da wani irin salon kallo ya karkace tareda ciro wayar shi yayi dialing number fauziya, ringing daya ta dauka yace ” come to Naziya side now. “Why zanzo side dinta? “Inbazaki zoba karki dameni da surutu you can pack up and leave. Ya datse kiran, ya jingina a jikin kujera ya runtse idanun shi batareda ya kuma ko kallon taba, tunda ya Kira Fauziya fuskar ta ta sauya tuni ya zubawa handsome and well shape face dinshi ido dake dauke da wani irin kyakkyawan saje dayake karamai haiba da haduwa ido, girar idanun shi zaro zaro sunfito, pink lips dinshi, jin shigoqar fauziya yasa tayi saurin waigawa tareda zuba mata ido, mugun kallo ta watsawa Naziya Wanda itama akaron farko taji ta tsane ta. Tareda mayar mata da kallon tayi saurin matsawa zata fara ruwan fada” ke ni sa’ar kice zaki harare ni wallahi…… “Enough banson hayaniya zoki bani Abinci am hungry. Yafada fuskar shi a tamke, tuni kanta yayi wani irin kato tafara kwarkwasa ” OK baby ai badamuwa, matsowa tayi tareda jan kujera dab dashi ta bude Abincin tayi serve ta dauki fake tana zokalo prawns din tana bashi a baki,
Sai wani irin shigewa takeyi cikin jikin shi , shukuwa he is enjoying each and every spoon na favorite food dinshi kamar ita tafi kowace mace iya sarrafa tukunya,
Takasa koda motsi wani irin Abu taji ya danne kirjin ta kamar sanda yana sata jin wani irin kakarin mutuwa ko miyau ta kasa hadiyewa Wanda tarasa dalilin, wasu hot tears da bata shiryasu ba suka biyo kuncin ta, a gefen fuskar shi yake kallon ta Wanda jiyake kamar ya buga tsallen murna is true she is jealous, Amazing.
Juyawa tayi tabar falon gudun karma yaga metakeyi ta shige dakin tabarsu anan, tana shigewa ya karfi fake din yana wani irin murmushi mai kyau ” tank you dear, Yafada cikeda nishadi tareda saka mata abaki ta bude ta karba jinta takeyi a sama yau.
Saida yaci yayi kat ya janyo jug dinta ya tsiyaya zoban da kanshi, kamshi ya bugi hancin shi nasu cucumber da abarba, kurba daya yaji wani irin kuzarin shi duk yadawo, best juice ever, yana gamawa ya ce “I need to bath muje can dakin ki hadamin ruwa, ya nuna mata wani daki daban, jikinta na rawa ta mike tayi dakin ta hada mai ruwan ya shigo tareda kwabewa ya rage dagashi sai boxer ya ce ta nemo mai kaya kana na ya shige fuskar shi a tamke yanzu domin bayaso ta shigemai.
A dakin Naziya kuwa samun kanta tayi da kasa sukuni taji Sam bata gamsu da shigowar ta dakiba, kukan me takeyi to ai Matar shi ce kuma tare tagansu meye nadamuwa? Toh me ya hana ita ta dafa mai da kanta sai yaci fuskar ta? Wayar ta ta janyo ta Kira Aunty Raliya, tana dauka tace “Alhamdulillahi Naziya kin Kira duk hankali na natashe haka Inna Ina gudun injiki cikin matsala hope ba wata matsala ko? ” Aunty ba komai. “Kifadamin ba matsala keda Abokiyar zamanki koda mijinki ko uwar mijin ki? ” Ina gefena yanzu ta shigo. tafada wani kuka na kufce mata na rashin dalili, “Innalillahi, me tayi miki, ni Raliya, Abinda nake tsoro kenan wallahi. Saurin hadiye kukan ta tayi jin Aunty Raliya ta rude, ” Aunty batayimin komai ba shine yakirata. Anan dai dole ta war ware mata komai tareda fada mata duk Abinda zai iya faduwa a tsakanin su. Ajiyar zuciya Aunty Raliya tayi tace “Alhamdulillah, kingani ko Naziya, insha Allahu zakiyi farin ciki, a tsaye khaleel yake inada labarin shi saidai yanzu matsalar na wurinki ki gane kishiya gareki duk wata muguwar akidar ki da hango haramci da kikeyi ki cireshi ki dage ki mallaki mijinki zaman ku bamai karewa bane don inaji akwai Abinda Allah ya boye a Al’amarin ku. Ta dade tana bata shawar wari kafin su katse, Ajiyar zuciya tayi tareda sawa zuciyar ta kwatan tawa batason tayi kuskuren baya, zaman ta da Ahmed wannan ce damar ta,
Sai da la’asr ta fito, suna zaune a falon, fauziya ansamu sake ta wani dora kanta a cinyar shi tana bacci Wanda haryagaji saboda neman magana yana gab da tureta yaji fitowar ta, wani irin saurin dora tafin hannun shi yayi akan fauziya yana wani shafawq kamar mai lallashin kwai, turus tayi kadan kafin tayi saurin danne ranta, domin ta canjo salo, ta matso fuskar ta a sake tace “me zakaci a dinner ko zata dafa maka ne? Wani mugun kallo ya watsa mata ba haka yake soba shi fadan ta yake kwadayin gani da sunan kishin shi that’s means he is mistaken, don haka cikeda takaici yace bazanci komai ba, ya ture kan fauziya ya mike, zabura tayi yace ” zoki wuce part din ki malama, daukar dankwalinta tayi tace” muje tom. Har zai kuma gwaleta ya dai bita waje Wanda daga nan yayi mosque ko lekawa baiyi ba, cikin gidan momy ta shiga da gudu saboda takai gulma, tana zaune tana faman wayar tafado kanta cikeda farin ciki, ” momy aiki yafara kyau, yau yakirani har agaban ta ya nata jidani kuma naga harda kuka tayi, “kai Y’ar Albarka, kice dole mukara wa Malam kudi irin wannan zafin aiki kamar yankan wuka, bari kiga mai zai faru ma nan gaba dani take zancen, tashi kije ki shirya mai dinner ki caba ado ki baza kamshi yau zakiga mai zai faru. “Kinfa san ban iya girki ba, uhm ki hadoni da mai aiki muje ta mun gyara. “Toh ke a haka zaki Kama mijin yakama ta ki gano halin khaleel Abinci yafi bukatar girkina tunda kina nan ki koya kamar wannan yarinyar rana daya ta iya dafa Abincin shi. “Nidai kidaina min kwatance da ita ni bantashi a wahala ba ita kuwa jikinta ya horu, nidai turon mai aikin muje. Tayi gaba abunta. Momy ta bita da kallo Sam bata ganin girman ta fauziya magana gatsau gatsau take fada mata.