AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 31 to 40

Wasu irin hawaye ne da batasan dalilin fitowar suba suka biyo kuncin ta, kalmar I love you daga bakin shi this is not the first time dataji ta, amma bata taba tunanin kalmar is serious ba daga bakin shi sai yau domin ido cikin ido yake aika mata da sakon, kuma tana hango gaskiyar Abinda duk yake fada ta cikin kwayar idanun shi, how she is zata iya bude baki tafada mai yanda takejin shi a cikin zuciyar ta amma Kash batasan kalmar da zata fara da itaba, she is not good in words like him, 

Jin hannun shi akan fuskar ta yana share hawayen yasa ta karkace kai tana mai kallon you are special, yace ” why kuka? Bakyason kalmar? Bazan kuma fada ba, Am sorry, kinji yanzu zantafi Anjima zansa azo nan ayi miki hoto Ina bukatar passport dinki zanyi Amfani dashi. “Inada su amma suna gidan mu baka hana akawo min kayana ba. 

“Wane gidan? Gidan malam. ” kice gidan su Shukrah, ke kinada gidan da ya wuce nawa ne? Sannan me matata zatayi da kayan da tayi rayuwa dasu da wani namijin? Your husband is a rich man baby so chill and enjoy, kinada damar da zakisa akawo miki store guda har gida Mrs khaleel.  

“Hmm you are too proud. Tafada tana kallon shi ta gefen ido, “oh sorry I forget bakyason mai kudi ko? Yana dariya, “by the way thank you, zanje gidan yanzu in karba dama Ina tunanin how zaki tsaya wani ya miki hoto, jini na zai hau. 

Murmushi tayi she is enjoying the moment, komai yayi Abun burgewa ne a wurin ta yanzu, he is such a shinny moon, dake haske filin zuciyar ta, dakyar tasamu yaci Abinci kadan itama ya dura mata, Wanda saida suka kwashe kusan hour biyu tare kafin yace zai tafi dakyar domin yanada Abunyi da yawa, 

A haka kwanakin suke tafiya Wanda wani gefen farin ciki, wani kuma akasin haka, Al amarin salifa da Momy kullum gaba yakeyi domin gaba daya khaleel ya kauracewa gidan saboda ita, sometimes zai Kwana ma a gidan batareda sun sani ba Salifa tayiwa momy tijara harta gaji haka momyn ta, kullum tana hanya, 

Yauma momyn zaune take tana waya da zarah, ” waini bangane kan Al amarin nan ba zarah, kudi nake narkarwa aiki kamar yayi kyau sai kuma komai ya ruguje, ni so nake ma yanzu idan zai raba Auren khaleel ya raba harda na Y’ar banzar nan,  

Fitinanniya yarinya kamar jinin ayu, kullum tana kallon Idona tana fadamin inturo mata Dana ya kwanta da ita. ” ai Aunty kinsa me kikayi tunfarko kinsan Y’ar nan gwara fauziya da ita amma kika nace toh kima gode Allah Khaleel din bai juyuwa da sai kinyi kukan Abun ni yanzu Ina labarin Naziya ne Ance min ana ganin motar shi gidan yayar ta Raliya kinsan muna unguwa daya ne. “Zarah al amarin khaleel yafara bani tsoro yanzu haka Kwana biyu bansashi a Idona ba, kuma manger dinshi yafada min kullum sai yaje office. “Nidai kisa kawai yadawo da ita gidan kila wani wurin yakaita gashi yana yawo gindin Y’ar uwar ta gani nan kanwar uwar shi ko ya kalli kofar gidana, tadawo koma meye kina gani amma wannan jikan matsafan wallahi nan gaba ma shafawa zakiyi ki rasashi baki daya. “Tir da bakinki zarah, ba shegiyar yarinyar da zata rabani da tilon dan da yarage min inaji Ina gani, ni sai Anjima zaki tayar min da hawan jini dama kwanan nan kullum high yakeyi. Ta datse kiran tareda mikewa tana gungunin duk inda yake sai yadawo taji meyake nufi zatagani wacece uwar shi cikin ita da dangin Naziya. 

Gefen khaleel kuwa yayi matukar yin busy, yagama shirin tafiyar su tsab Washe gari jirgin su zai daga zuwa bangkok, batasan komai ba yadai fada mata ta shirya zaizo gobe su tafi, gashi tun ranarda yazo da rigimar sa mata magani bai kuma tsayawa sunyi wata doguwar hiraba, dayazo yake tafiya saboda aikin dake gaban shi, he has a lot of responsibility akanshi yanzu na campanonin su, don haka kanshi yayi zafi. A yau yakeso ya hada duk Abinda zai iya bukata a tafiyar, don haka baiko je wurin Naziya ba duk da tanason ganin shi gashi tana kewar shi sosai, ya saba mata da wasanni yanzu kuma ya dauke ga wutar sonshi data gama ruruwa a zuciyar ta, dama take nema ta baje kolin tarai rayar shi domin ta mallaki kayanta kamar yadda a kullum Aunty Raliya ke bata shawari, ta cire kunya ta zamo magajiya ba karuwa ba a gidan mijinta, 

Taci buri takuma dauki Alwashin bashi mamaki, don haka shirye take tsab da zuwan shi, tana murna da duk inda zasuje she is ready for him, ta tsumu Aunty Raliya ta tsumata ta gyareta sosai tareda taimakon Aunty Aisha,  

Sai misalin karfe takwas ya shigo gidan, ko ciki bai shiga ba nan part din Naziya ya tsaya saida ya hada y’an kayan shi ya yi wanka ya saka kana nan kaya yayi part din Salifa, tana zaune tana layi kamar wadda tasha maye, toshe hancin shi yayi domin if he is not mistaken warin giya yakeji, jin yayi karo da kwalba yasa yaji wani irin mugun takaici cikin tsananin zuciya ya juya domin no need ya tsaya yimata magana bata cikin hayyacin ta. Gidan Momy ya shiga a zafafe, tana zaune tana aikin wayar da zarah, sallama yayi ciki ciki ya shigo, tayi saurin kashe wayar tareda zuba mai na mujiya, ganin yanda yake haki kamar Wanda yayi gudu kan iska. 

“Kai lafiya, Ina kashiga Kwana biyu? Yanzu kafadomin gida kana cika kana batsewa, khaleel dai dai nake dakai Indai nice uwar da na haifeka zan nuna maka na isa, wato saboda nasa kafitar min da wannan jinin matsafan shine zaka dauke kafarka ka manta da hakkina na uwa ka tare gindin d’an gin malamai ko khaleel?    

Cikin takaici ya dago kai, ” haba Momy yanzu wannan yarinyar da kika nace sai kin lika mana tafi Naziya a idonki momy go and see that girl, she is drinking in my own house, wace irin macece Y’ar musulma tasha giya cikin gidan Auren ta, bazan zauna da ita ba gaskiya zan saket….. “Akul khaleel karka fara sakin ta sai kafara sallamar wannan Mayyar kafin ka saki salifa no matter what tafimin Y’ar gidan matsafa da ke neman rabani dakai. 

“Momy haka zakice bayan ga gaskiya a bayyane? Ok am leaving bazan dawo ba saikin rabani da wannan Auren domin wallahi momy koda zaki tsine min inbi duniya bazan zauna in hada jikina da na wannan kazamar ba. Ya juya da sauri tana kiranshi yayi waje. Tana biye tana Kira yaki waigowa saida ya shige cikin gidan shi tayi gefen salifa, ” bari inga Y’ar banzar nan, wannan wannan yarinyar bazata shiryu ba. 

Koda ta shiga tana kwance ta kelaya Amai, haka ta toshe hancin ta tareda fita da sauri kar itama tayi tana tsinewa Salifa “wannan ya’ akwai Y’ar banzar wallahi bari inkira uwar ki ita ta dauki mataki. 

Ganin motar shi taji sanyi tasan bazai tafiba ta koma cikin gida….. ????

“Insha Allah gobe ma zanyi kokari inyi posting saboda baku samu update ba sosai wnn satin kuma naso typing din yayi tsawo yau Amma Allah yakaimu da rai da lfy kuna raina masoya Allah ya Kara mana hakuri baki daya. Amen 

*Matar Soja *

4⃣9⃣&5⃣0⃣

08032252760

08175479641contact this numbers for more information 

……….. Ko waya bai iya kiran Naziya ba wadda ta cika tayi fam saboda yanda baida wani lokacin ta yanzu bayan yamata sabo mai wahalar mantawa, she is missing him, salon shi mai rikita ta Mata kwakwal wa da gangar jikinta, duk lokacin da ta tuna dashi sai taji tsigar jikin ta na tashi, Kwana tayi juyi har garin Allah ya waye, Wanda gefen shi kuwa da bakin ciki da takaici ya Kwana, a afarko yana dayasanin shirya tafiya ya bar Momy ita kadai, Amma yanzu baida wani choice sai na yabar musu garin kawai kowa ya huta he is going batareda wani regret ba, yana son jin muryar ta Amma yasan zata gano yana cikin damuwa domin zafin da yakeji bazai iya boye shiba zata gano shiyasa kawai ya hakura, Amma baiyi bacci ba Sam, sallah yayi tareda yiwa d’an uwan shi Addu’a har Asuba, jirgin su sai karfe shida na yamma zai tashi don haka bai fita da wuriba sai kusan karfe takwas, ya kirata lokacin tagama kunbura, saida ya Kira sau uku tayi picking tareda yin shiru kamar ruwa ya cinye ta, ” yau jan Aji akeyimin bama gaisuwar? ” Ina Kwana, tafada ciki ciki, “lafiya gimbiya jiya ko a kirani? “Kai meya hana ka kirana? Kuma yanzu ma kalla sai karfe takwas kake kirana. Cikin shagwaba tareda narkewa take mai maganar, ” are you waiting for my call my diamond? Wow Ashe ni d’an gata ne a wurinki baby. Numfashi yaja tareda yin Ajiyar zuciya, yace ” get ready karfe shabiyu zanzo muje gidan malam muyi musu sallama. Shiru tayi kadan tana tunanin Ina zasuje? Bata tanbaya ba domin bincike ba aikin tabane don haka amsawa kawai tayi yace zai wuce office letter, kashe wayar yayi, tabi da kallo, when zata samu dama itada mijinta? Yaushe ne zasu kasance atare batareda ya matsa ko nan da can ba, me nayi miki momy meye laifina, talauci aibu ne? 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button