AUREN GADO Page 31 to 40

Yafada tareda gyara zama yana cewa ” call her or mu juya yanzu we have a plight to catch time is going.
Wayarta ta daga domin Allah yagani bataga samu taga rashi ba don haka ta Kira Shukrah tace don Allah takawo mata hijabi tana waje, karbar wayar yayi jin Shukrah na tanbaya wane irin hijabi kuma meke faruwa? ” Shukrah ki kawo mata please muna jira harda nikab please. Dariya Shukrah tayi tareda mikewa tana cewa “Aunty kinyi Aure. saida ta dakko mata kato cikin kayanta nagida sabo tareda nikab domin tanada su tafadawa inna tana zuwa Yaya khaleel nakiranta a waje.
Fitowa tayi tana kunshe dariya harta matso gaban motar ya zuge glass yace ” Shukrah tank you for saving her da bazataga Inna ba yau. Gaidashi Shukrah tayi tareda mika mai ya karba ya mika mata tana tura baki ta zura, gefen ta shukrah ta zagaya tace “Aunty kece da irin wannan shigar yanzu Yaya khaleel ya taimake ki da keda malam ma. ” Shukrah kyaleta saboda tasamun hawan jini yasa takeson fita a haka yanzu. Ya bude motar yafito tareda zagayo wa gefen su harta daura nikab din ya bude mata ta fito, yace “wow koke fa yanzu? Harara ta watsa mai cikin wasa yace “I will pay for that look letter. Yayi gaba yana murmushi, matsowa Shukrah tayi tareda cewa “Aunty wannan irin love, when how? Gaskiya kunfi matching da Yaya khaleel look at him, inama kinki Y’ar da, Dana shige ni. Tafada cikeda tsokana, ta kai mata Dan dukan wasa, har suka isa kofar gidan ta wuce Abunta ciki shikuwa yayi wurin da malam yake da manyan Almajiran shi,
Tana shiga ta kwalawa Inna Kira cikeda doki da kewa, tana zaune tana kulle kullen ta tace “Aa Amare da rana?
Zama tayi suka gaisa Shukrah ta kawo mata zobon Inna mai sanyi tasha tana lumshe idanun ta “I miss this. Inna fuskar ta dauke da walwala da farin ciki, tace “Y’ar nan kina can kinyi shar dake ni Ina nan kullum tunanin ki tunda nasan bakiso wannan Auren ba Naziya, da Alama wannan Khaleel yana kulamin dake tunda har kinsaki jiki kinyi fes, kai Alhamdulillahi. Murmushi kawai tayi tareda dukar da kai saboda kunya, haka suka shigo tareda malam ya gaida Inna cikin girma mawa kafin malam yace “sunzo yimana sallama ne zasuje can kasar waje. Saurin kallon shi tayi Wanda idanun shi na kanta kur ko kunya baiji aganshi, ya kashe mata ido daya, wato tafiya zasuyi shiyasa yake neman hoto,
Wanda duk batasan shirin shi ba,
Sunkai karfe hudu a unguwar barinta ciki yayi shikuma ya fita waje wurin malam saida ya kirata ta mike batareda ta gaji ba tayi missing Inna, Shukrah ta rakata bayan tasha nasihohi wurin Inna da malam, yabawa malam kudi sosai yace akarawa Almajirai Abinci, domin yasan in shi zaibawa bazai karba ba, Shukrah ma yabata yace tasiya kayan kwalliya, wayar hannun Naziya ya karba ya mika mata bayan ya cire layin yace ” kiyi manage kafin inkawo miki sabuwa. Tayi tsalle tana godiya domin ta mugun lora wayar tunda taganta, murmushi Naziya tayi tareda karajin shi cikin zuciyar ta yanda yake sakin jiki da yan uwanta All that ego da take tunanin yanada yau bata gani,
Haka suka tafi fuskar ta kamar gonar Auduga tana Kara daura damara,
Gidan kawu sukaje Wanda ta yaba da karamcin su, sun karbeta hannu biyu, hardai uwar gidan da taji dama haka Momy takeyi da ita. Sunyi mata shatara ta Arziki kafin yace tafito sutafi, kamar karta tafi ga y’an matan da dama sun d’an saba tun lokacin Ahmed.
Karfe biyar da rabi suka isa ainihin kofar gidan su Wanda bai shiga ciki ba yace ta jirashi ya dakko kaya, ido tabishi da shi, har ya shiga katon gate din, bai wani dauki lokaciba ya fito dauke da akwati madai daiciya, ya saka a bayan motar, “nakira Aunty nafada mata sai mundawo jirgin mu yakusa tashi.
Yafada yana tayarda motar, tareda kiran manager dinsu yace su hadu Aminu kano Airport yanzu,
Abun kamar wasa taganta a filin jirgin Wanda all her life bata taba mafarkin zuwa ba, yau gata wai jirgi zata hau zuwa wata kasa, ta zubawa sarautar Allah ido, suna isa manager na isowa, yace “naso muyi wanka before going Amma har anfara announcing, hanata fitowa yayi ya bashi envelope ya kaiwa momy gobe da key din motar if he needs him zai kirashi. Saida yaji ana Kara Announcing yace ta fito baida yanda zaiyi,
Fitowa tayi still da katon hijab dinta saidai ta cire nikab din yanzu domin tagaji, suka gaisa da shi sama sama kafin ya sallameshi ya rike hannun ta suka wuce.
Wai yau ita naziya ce zaune a cikin jirgi first class seat tunda jirgin na y’an kasuwa ne, yana zaune a gefen ta ba wasu mutane sosai a wurin ya daura mata belt tareda d’an saka hannu ya rungume ta domin supporting dinta don yasan karon ta nafarko kenan, Wanda tayi matukar kokari wajen natsa kanta da dauriya karta nuna kauyancin ta,
Sai gasu a sararin samaniya, jirginsu ya daga, taso tayi sallama da Aunty Raliya Amma yabawa Shukrah wayarta, sai muyi musu fatan sauka lafiya…….. ????
Me kuke ganin zaifaru da rayuwar momy masoya, ga khaleel ya tsallake ta batareda tasani ba ya dauki Y’ar da bataso ya bar kasar, ga momy nan dauke da sabon shirin kashe Auren shi tareda nemo mai wata Matar, muje zuwa dai ankusa isa, inda nakeson kaiku da Yar dar Allah.
*Matar Soja*
5⃣1⃣&5⃣2⃣
*Alhamdulillah naga masoya na Asali, naga kuma masu mugun gajen hakuri, yau ba bawa mai hankali da zaiyi wa kanshi fatan ciwo, tsawon lokacin da nafara rubutu inba wani kwakkwran dalili ba bana kaunar infara typing in tsaya, na rubuta littafi bakwai wnn ne na takwas hakan bai taba faruwa ba, nafada nakuma nafada nabada hakuri mutanen da sukasan halin da nake ciki sunfito sunyi bayani, Amma wai duk da haka wasu zasu rika daukar waya suna tanbaya ta Ina posting dinmu Ina update sister kin ajiyemu kin kyale mu, kuma abin mamaki masu complain din duk wainda suka biya dari biyar ne, Allah sarki akwai sister da tabiya dubu uku Ana bata prvt wlh tun ranar da ta tanbaya nafada mata banda lfy bata kuma bina tace update ba, haka akwai masu dubu biyu dubu daya duk ba wadda tayi complain saboda lfy itace komai idan ba lfy ba Abinda bawa zai iya yi a rayuwa, kuma ciwo inba na Ajali bane yanada iyaka don haka masoya nagode sosai da sosai masu complain kuma Allah ya baku hakuri bazance komai ba*
08032252760
08175479641contact this numbers for more information
……………Bacci tasha sosai a kafadar shi, Wanda ya raba dare yana kare mata kallo, wani irin farin ciki yake jin shi a ciki, finally zai kasance tare da ita, zasu rayu su biyu ba wani shamaki ba Wanda zai hanasu sakewa.
Washe gari tunda safe sakon shi ya iso wurin Momy lokacin ta shirya fita aiki, cikin adonta na manyan mata, taci karo da manager din khaleel, yace “ga sako inji mai gida Hajiya. Ya shigo da motar tana sake da baki ya faka wajen Ajiyar motocin su, saurin bude takardar tayi taga Atm din Ahmed da nashi na gida tareda takardun gidan dana company, wani irin faduwa gabanta yayi, me wannan sakon ke nufi? Saurin kiran manager tayi ganin zai fita tace ” kai zo Ina mai gidan naka da yabaka wannan sakon?
“Hajiya ai tunjiya yabar Nigeria bai fadamin inda zaije ba tareda madam dinshi. Ya fita Abinshi domin shidai ya isar da sakon.