AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 31 to 40

Dakyar sukayi wanka suka fito bayan dauro alwala.bayan sun idar yace tayi bacci yanzu, ” kinsan kinci bashi dayawa zaki biya duka. ” wane irin bashi naci? Tafada tana kwanciya akan gadon,, ” kinsan lokacin da nake zuwa gidan Aunty Raliya hakuri kawai nakeyi nake dawowa batareda na danne kiba a falon ta shiyasa na rage zuwa kar inyi abin kunya gidan surukai, to yau kuma dole Kibiya. ” Nagaji fa kaima ka gaji don Allah kayi hakuri nan da sati biyu. Wani irin kallo ya watsa mata tareda Y’ar harar wasa, ” Saboda gani sakarai ko, toh hakurin da nayi a baya yanzu bazanyi ba yarinya ki saba kawai, waya fada miki ma ana gajiya a harkar nan, nidai bazan taba gajiya ba ko yanzu don inada Abinda zanyi ne dana Kara, ko inzo ne only five minutes. Yafada yana kashe mata ido, kifewa tayi tareda juya mai baya domin bacci takeji kuma batada amsar bashi tunda shi bayajin kunya. 

 Dariya yayi ya fita yana sosa kai, bacci tayi sosai har zuwa magrib, shikuwa fita yayi yayo mata shopping kamar hauka, tareda duk Abinda yasan zata bukata a gidan na Abinda zata iya ci,sai a lokacin ya tashe. Tana cikin jin dadin bacci taji ana hura mata iska a idanun ta mai dumi, a hankali ta bude, nata suka sauka cikin nashi ” hy sleeping beauty lokacin magrib yayi wake up . yafada yana dagata, duk jikinta ya mutu tayi salati tareda direwa kawai tana murza idanun ta, ya bita da kallon burgewa komai tayi burgeshi takeyi, matsawa yayi tareda rungume ta gam, ” kije kiyi wanka ko in yimiki ne? Girgiza kai tayi tace ” zanyi bansan lokaci ya tafi har haka ba. Tafada tana yin gaba bayan yasaketa, 

Shiga bathroom din tayi ta kwabe tareda fara yin wanka, turo kofar yayi ya shigo dai dai tana dauraye jikin ta, tayi saurin kallon shi tareda kwabe fuska ya zubawa ko Ina na jikinta da kallo yana hadiye miyau, saurin karasawa tayi ta janyo towel tana harar shi ” meyasa ka shigo baka bari na gama ba? tafada cikin shagwaba, matsowa yayi jikin shi kamar Wanda kwai yafashewa yariko west dinta yana jan numfashi ” why nida halalina? Yafada yana kokarin kwance towel din ta rike tareda fisgewa tayi waje da gudu tana dariya, Saida ya zauna kan sink na d’an lokaci ya dawo cikin hayyacin shi kafin ya sosa kai shima ya tube zuwa wanka. 

Da kanta ta koma kitchen domin muguwar yunwa takeji rabon ta da Abinci tun rana, store din tagani da su spaghetti da shinkafa irin nacan shiru tayi nadan lokaci kafin tayi tunanin mezatayi, shinkafa fara ta dafa ta hada stew da naman kaza, bayan ya idar da sallah ya dauki wayar shi ya fara kiran manager domin jin ko yakai sakon shi yace mai yakai suka dade suna tattaunawa a tsakanin su kafin ya Kira kawun shi, shima sundauki dogon lokaci yana mai nasiha akan idan ya d’an dai daita Al amuran shi a can ya dawo domin hakkin mahaifiyar shi da kuma Matar da yabari tunda akwai igiyar Auren shi akanta. 

Sai da gaban shi yafadi da ya tunada akwai wata salifa wai, momy kan dama dole ya nemeta saboda uwa uwace Kuma so kawai yake ta fahimci kuskuren da ta tafka tundaga farko. 

Shiyasa bai san me takeyi ba har ta kammala ta shigo, Saida sukayi isha’i yace “suje restaurant akwai Wanda ake dafa Abincin da zata iya ci, tace ta dafa musu Abinci ai. Ta mike tareda fitowa yabita da kallon mamaki, ya tashi ya bita falon, harta fara serving nashi, kamshi nayimai welcome, ya shaka tareda matsawa ya rungume ta “yaushe duk kikayi wnn aikin madam? Murmushi tayi kawai tace” let eat karya huce. Tafada tana cire hannayen shi a jikin ta, ya zauna fuskar shi tuni ta cikada walwala da Annuri farin cikin, zama yayi ya kwashi dadi tareda hamdala, 

Ya za ayi yaso wata mace yanzu bayan ta hada komai, kyau ilimi hakuri uwa uba ga tarin Zuma. Yanaci yana kallon ta, itama taci sosai saboda yunwa dazu ba wani koshi tayi ba yana kallon yanda takecin kaza yagane tana kaunar chicken, Wanda ita kanta tarasa dalilin dataci wannan naman da yawa haka. 

Tsakiyar falon ya koma bayan sun kwashe komai lokacin misalin karfe tara na dare akasar bangkok Wanda yayi dai dai da karfe daya na daren kasar mu Nigeria, domin banbancin awoyi, wanka taje tayi tareda duba wurin waldrp din dake dakin tana duba trolley din su taga bata wurin, budewa tayi taga ya shirya mata sababbin kaya makil tundaga dogayen riguna riga da sket su jeans passion na mata har zuwa kan kayan bacci masu matukar kyau da daukar hankali, wani iri taji, wato tana bacci yayi duk wannan Abubuwan bata sani ba. Wani irin tausayin shi taji domin tasan duk Abinda yakeyi yanayi ne domin yafaran tamata, wani nazari tayi na d’an lokaci akan Rayuwar shi, yanada murdadden hali shiyasa baida tsoro halin shi daban dana Ahmed shiyasa yazama jarumi tsayayye. 

Wata riga ta zabo guntuwa iya guiwa ja rigar tayi mata kyau sosai daga ita sai d’an pant mai irin v shape din nan, gaban rigar nada kokon brah da yakamata dam, rigar ta haskata sosai ta gyara sumar ta tareda feshe jikinta da kamshi ta kalli mirror tagan y’an da ta fito kamar ka saceta ka gudu. Motsin da taji ne yasa tayi saurin juyowa, ya tsaya a bakin kofar ya nade hannu yana kare mata kallo tundaga kasa har sama, bazai iya magana ba sai ido, ganin yanda yake kallon ta tasan ya yaba don haka cikeda yanga domin daukar hankalin shi ta matso kusa dashi tace ” naga kaya nagode sunyi sosai Allah ya Kara budi da Arziki, wato Ina bacci kafita har kayi wannan aikin bansani ba? Lallai nayi bacci sosai, muje muyi kallon KO? 

Kur ya mata ko kiftawa bayayi, ” she hardly talk, don haka duk lokacin da take magana Abin yake matukar dauke mai hankali, domin muryar ta shape din lips dinta, yanda take magana, yana tafiya da zuciyar shi baki daya, bare yau ga wanna shigar data mugun rikita shi, fisgota yayi cikin sauri zuwa kirjin shi domin yasamu saukin Al amarin, muryar shi a sarke yace ” ba wani kallo bayan kin cikamin ciki da Abinci kuma yanzu kinzo kin rudani what you expect from me now? 

Wani irin daukar Amare yayi mata tareda switching light yana cewa ” let watch each other babe….. Suka shige blanket domin farantawa juna rai tareda manta duk wata damuwa da suka baro a 9ja. 

Sati biyu suka kwashe suna murza soyayyar su, ta murje tayi bulbul da ita, kullum cikin kwaso mata kayan gayu yake , a cikin garin kuwa ba inda bai zagaya da ita ba, wasa wasa itama tafara cin cimar shi ta mutanen sinawa, har tanaso ta fishi zakewa, yana matukar mamakin tama yanzu, gashi duk matsin da yake ganin yana yimata bata nuna gajiya warta, sunyi matukar shakuwa, soyayyar su suke sha sosai, koda yaushe suna like da juna, kusan kullum sai tayi waya dasu Aunty Raliya harma dasu malam domin ya d’an karo mata wata sabuwar wayar ta yayi, gashi d’an zaman nan yana ta koya mata tuki idan sun d’an fita, ko Ina suka wuce kallon su akeyi, shikuwa haka zai kwakume abarshi gam yace ” baby da zaki Y’ar da da kin rika zama a gida ko ki saka nikab kafin jini na ya hau ko mu daina fita. 

Dariya kawai takeyi tace ka cika kishi Zaauji. Sunan dake matukar faranta mai zuciyar shi. 

Yau basuje ko Ina ba kwance take tana cin roasted lobster taji yaji, yanzu tafishi sanin dadin sea food, daga ita sai wani arnen guntun wando passion na mata da shimin shi data kamata dam, tazama Y’ar gari don baya kaunar ganin ta cikin manyan kaya, kamar baby doll, ya shigo cikin kanan kaya ya murje yayi kyau sosai yana tafe yana waya da manager dinshi na Nigeria, ” kaje gidan ka dubamin lafiyar Momy na nakira wayar ta bata shiga. Yafada cikeda damuwa domin haka kawai yaji yana son yaji muryar ta domin yasan a duniya Momy nason ya’yan ta gashi ba Ahmed shima ya mata yaji, kuma yasan no matter what dole ya sauke hakkin uwar nan, kallon shi takeyi kamar ta lashe shi takeji, saboda kyau da kuma cikar haiba ga iya soyayya ta kowanne fanni don haka yayi nasarar sace zuciyar ta baki daya, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button