AUREN GADO Page 31 to 40

“Sai na fara konata kafin ni inkone idan bakinta bazai mutuba, kuma ki wuce ki dafa min Abinci ko in karasa ki wallahi in binne ba Wanda zai bincike ki.
Dariya kawayen sukasa harda tafawa, ta mike da kyar taja kafa zuwa kitchen, tana share hawaye ta sai rariya da kudinta. Haka ta baje ta zuba musu girki badon Allah ba, kuka kuwa ai yazama mata sana’a, tanayi tana hakkin ki ne Naziya.
Fitowa tayi domin ta shirya musu Abinci tasame su hade a kasan carpet suna romancing juna kowace da Y’ar uwarta salifa kuwa ko rigarta ta cire tana shan yaji dayar na sha mata nono a tsakiyar falon Momy, tray din dake hannun ta ta saki saboda firgita da tsoro. Yau taga Rayuwa, Innalillahi wa inna ilaihirraji’un. Tayi taslima da karfi, Wanda karar try bai dawo dasu hayyacin suba amma salatin mommy yasa suka juyo, ko a jikin su salifa ta buga mata tsawa ” meye kamar baki taba ganin romance ko shan nono ba bayan kema kinyi da tsohon mijin ki, oh come on ki zo ki bamu Abinci yunwa muke ji. “Babe bari mu koshi mu koma can part din nan akwai sa idawa. Ko momy ta fito sai tayi tofin tsiya kafin tayi shiru.
Duk inda tashin hankali yake yau mommy ta gama ganin shi da jin shi, subuhanallah me ta yayubo a rayuwar ta?
Jikinta na rawa ta tattara su plate din ta koma ta kwaso wasu ta shieya musu komai, wani irin zazzabin tashin hankali ke kamata, takasa koda magana. Tana gama shirya musu Abinci ta koma dakin Ahmed domin dakin ta kawarta ta shiga,
Kafin kace me jinin ta ya mugun hayewa.
Ba waya ba yanda zata iya kiran likitan ta.
Domin har wayar ta sun dauke tana cikin tuminin takabar salifa wai.
Ciwo ya rufeta ba mai kula da ita. Haka take cikin wahala har safe, Wanda su suna cin Abincin su suka bar mata gidan zuwa nasu domin karasa masha’ar su,
Kwana biyu tayi cikin mugun Yanayin dakyar take iya tashi tasha koda ruwa tafita hayyacin ta sosai Wanda a ranar khaleel ya tura manager Wanda yana zuwa yaci karo da sabon mai gadi da ya hanashi shiga gidan, wai Hajiya tasa dokar kar Wanda ya shigo Saida izinin ta,
Wanda dai dai lokacin da kawayen nata suka fito zata rakasu kanta ko d’an kwali tana sanye da wasu matsiyatan kaya na rashin tarbiya mai gadin ya ruga ya wangale musu gate suka fita, haka manager ya saki baki da ido yana kallon salon iskanci, har zata juya ta koma ta gan shi ya zuba mata ido, kare mai kallo tayi, ta yaba gayen very young and handsome ba laifi shima.
Matsowa tayi tana karairaya ” hy handsome me kake nema?
Kallon banza ya watsa mata yace Hajiya nake neman Oga khaleel ya ce inzo induba ta. Yafada kai tsaye, ” kai waye? ” manager dinshi, zan iya shigowa? Hadiye miyau tayi saboda jin sunan khaleel tace ” yeah ofcos shigo.
Shigowa yayi kawai yana kallon gidan duk ya fita hayyacin shi domin ba wasu masu aikin kirki suka kawo ba,
Part din Hajiya ya shiga Wanda a nan ya sameta ta rarrafo da bin bango da kyar tafito domin muguwar yunwa takeji duk da tana cikin ciwo.
Yayi matukar firgita ganin yanda ta fada cikin sati biyu da bai ganta ba, tana ganin shi taji wani irin sanyi da farin ciki don haka ta zaburo, Wanda tuni ta zube Tim a kasa tasa Kara. “Subuhanallahi Hajiya. Ya nufota da gudu domin ya taimaka mata Wanda yana matsawa yaga ta sume.
Cikin gaggawa ya Kira Asibitin da yasan suke zuwa yace likitan yazo domin bazai iya dagata ba Abunka da ba kadan ba.
Yadai taimaka ya jata saman kujera Saida likita yazo suka kaita dakinta da taimakon nurses da aka zo dasu, Abunka da kudi tuni aka fara bata kulawa cikin gaggawa, sun dade akanta kafin likitan ya fito yasamu manager, ya zare glass din idanun shi, ” Ina me gidanka yake yakamata ya fita da ita kawai kai tsaye idan yana son ta samu kulawa domin da Alamun tasamu mutuwar barin jiki sakamakon hawan da jinin ta yayi sosai.
Hankalin shi ya tashi domin bai san ta Ina ma zai fara wannan fadawa khaleel ba halin da ake ciki,
Don haka ya Kira kawun su ya fadamai komai yayi salati yace gashi nan zuwa yanzu.
Saida ya dauki uwar gidan shi kafin ya tafi shima,
Halin da suka sameta a ciki ya mugun daga musu hankali, cikin gaggawa kawu modu ya ce a mayarda ita Asibiti zaifi kafin a Fita da ita. Fita yayi yana neman wayar khaleel, Wanda yayi dai dai da fitowar Hajiya shaeefa da salifa domin ganin meke faruwa a gefen mommy da manager yazo, basu taba zaton khaleel zai waiwayo taba sai sukaci karo da kawu modu yana saka waya a kunne, kallon shi sukayi a tsorace domin basuda gaskiya, aiki ya lalace bayan su sunyi farraku a tsakanin ta da duk wani Wanda zai taimake ta, how yanzu ba aje ko Ina ba ga modu a gidan… Murya kasa kasa salifa tace ” mommy meye nake gani me Alhaji yazo yi nan? Aikin ya karye ne? Mun shiga uku. ” ke don Allah yimin shiru wa ya isa ya karya aikin boka ai ko ita ban barta haka ba bare khaleel bari kigani bazai zoba ya Riga ya tafi shikuma wannan me ruwan mu dashi.
Ajiyar zuciya tayi, “Hmm har na ji tsoro domin nafara jin kamshin dollar’s din da zan mallaka. Fitowar da akayi da ita ne yasa suka bisu da kallo , ba Wanda ya koma kansu har sukabar gidan da ita,
Juyawa tayi cikin gidan ta momyn ta bita, sai zagaye takeyi, ” kingani Ashe batada lafiya ne wallahi khaleel zai zo mommy ni tsoro nakeji. ” relax baby me zai faru idan yazo? Bare bazai zoba wannan nadewar da kikaga tayi bazata kuma mikewa ba bakin ta bazai taba budewa ba bare tafada mai me yafaru, don haka Ina zuwa bani jakata in fita yanzu.
Itadai tafara tsorata domin khaleel ba namijin da za ayi wa iskanci a kwashe lafiya bane.
Saida suka bata special room a Asibiti kafin kawun ya Kira manager yace bani number da yake kiranka da ita.
Lokacin suna zaune a falon su suna kallon season film na Philippines tana lafe a jikin shi kamar mage shikuma hannun shi na cikin wuyan shimin jikin ta, yaga kiran manager dama jira yakeyi, saurin tashi yayi ya gyara zama tareda ciro hannun shi cikin rigarta, yayi cutting call din ya kira shi, ya akayi ne? Lafiya kalau ga Alhaji. Ya bashi wayar, gaisawa sukayi kafin yace ” khaleel kazo fa domin Hajiya jinin ta ya hau yanzu haka tana Asibiti anyi admitting dinta, jikin yayi tsauri wannan karon kayi kokarin dawowa ko a turota can.
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un, Ina zuwa kawu insha Allahu. Ya kashe wayar hankalin shi tashe, ya dafe kai, jin yake bai kyauta ba Sam na barinta da yayi, dafashi tayi ” me ya faru ne? Dago idanun shi yayi, ” we’re going back to Nigeria mommy ba lafiya tana hospital. Yafada cikeda damuwa, “Subuhanallah, Allah ya bata lafiya, bari in shirya mana kayan mu tom. Tafada tana mikewa, ya riketa, ta tsaya, ” ki zauna inje indawo mana.” no ni dai zan je kuma kaga bamusan Yanayin jikinta ba gwara mutafi gaba daya, koda zamu dawo tareda ita zamu dawo.
Rungume ta yayi ” bakya tsoron me zatayi? ” me zatayi? Uwace fa ta isa ne kuma kome takeyi tana yi ne saboda tana son mu don haka muje mu fara shiri. Kara damke ta yayi yana mai kisin din wuyan ta, har Saida taji tsigar jikin ta na tashi tayi saurin janyewa ” karka hanamu shiryawa Malam let’s go. Tafada tana dariya tareda ruko shi tana janshi yabita yana murmushin karfin hali, daurewa yakeyi karta ga tashin hankalin shi, amma a dame yake.