AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 31 to 40

Duba time yayi yaga karfe hudu na yamma a kasar yace let me check in akwai available plight mu tafi yau kawai. 

Yafada yana dubawa a wayar shi. 

Tausayi yabata sosai domin duk kokarin shi na ganin ya daure abun yaki yuwuwa domin damuwar a bayyane take a fili. 

Ita ta shirya musu kayan da zasu bukata, 

Kafin ya shigo cikin sauri ” let get ready akwai jirgi mai sauka Abuja. Yafada yana shigewa bathroom. Tashi tayi itama ta bishi har yafara wanka ta tsaya daga nesa tareda zuba mai ido cikin hanzari yake Abinda yakeyi, domin duk hankalin shi ya koma gida. Hmm khaleel ne zata biyoshi bathroom ya share? Lallai a dame yake, don haka bata matsa ba Saida ya gama ya matsota ” quickly baby. Ya fita, tayi Ajiyar zuciya ta fara itama. 

Ten minutes ta shirya domin ta lura a hanzarce yake, mai aikin shi da yabawa hutu ya Kira yace tadawo kan aikin ta na kulada gidan zai koma 9ja. 

Sai zuwa tsakiyar dare jirgin su ya daga, 

Like you know is a very long journey, don haka ko yanzu Saida suka Kwana a hanya da sassafe jirgin su ya sauke su a filin jirgin na babban birnin tarayya. Tayi matukar gajiya, fiyema da tafiyar su domin jikin ta mugun kasala takeji da batasan Ina ta samo asali ba. Domin ita batada ganda ko kadan, 

Cikin doguwar Riga take maroon tayi matukar murjewa tareda Kara kyau, kafarta cikin low pass baki mai kyau sai Y’ar Karamar Jakarta data rataya, 

All eyes on her, gayu sai baza ido sukeyi sunga mai zafi, ya ankare don haka tuni ya matso tareda rungume kayan shi a kafadar shi saboda kuraye,

Sai da tayi dariya domin ta gano shi yace “what? “Bakomai. “Hmm I don’t know why kikayi irin wannan kwalliyar? 

Bafa kwalliya a fuska ta. Yes yakamata kisaka katon hijab kinga nan ba can bane sunayin kamar su dauke min ke bazan iya ba zaki dawo da saka hijab malama,

OK malam, Tafada tana jin dadi tareda dariya, plight ya Kuma sama musu zuwa kano, Wanda ba Wanda ya fadawa ya shigo 9ja, har Saida suka sauka a kano ya Kira manager yace ya sa akawo musu mota suna Aminu kano airport. 

Jikin shi na rawa yace gashi nan zuwa, da kanshi ya zo tarbar su. 

Sun d’an jirashi a reception kafin ya iso, 

Ya musu barka da Zuwa kafin ya dauki kayan su ya zuba a motar, suna tafe yana tanbayar shi jikin Mommy, yace tana Asibiti har yanzu su wuce ne kai tsaye? ” no bari muyi dropping madam dina a gida first sai mutafi. ” A’a mu wuce kawai ban gajiba nima inaso in ganta. 

D’an hararar ta yayi kadan, yace toh su tafi. Tanbayar shi tayi da ido what? Ya share. Saida suka isa hospital din ya fito itama zata fito yace kidaina magana a gaban wani ke bakisan yanda muryar ki take ba ko? Oh shine matsalar? Sorry Zauji. Don’t repeat that. cikin bada doka ya fada. Suka jero kamar taurari, 

Adakin mommy ce kawai kwance sanye da na urorin dake taimaka wa jikinta, su kawu modu da uwar gidan shi suna zaune a waje domin dokar Asibitin. Suka iso, sunyi matukar mamakin ganin su haka da sauri, Dama ka taso Ibrahim? eh kawu ya mai jikin? Toh tana ciki kaje kaga likitan first. Wucewa yayi yabarta a wurin, ta gaidasu cikin girma, mama uwar gidan kawu ta rungume ta kamar Y’ar ta cikin jin dadi sannu Y’ar Albarka. 

A zaune yake doctor na yimai bayanin basu gane kan Al amarin nan ba yau jiya da aka kawota da Alamar improvement amma yau jikin ya Kara nauyi bayan duk na urorin dake taimaka mata. Dafe kai yayi yace, Zan iya zuwa in ganta? Yafada idanun shi sunyi ja tun baiganta ba, likitan yace “yeah sure muje…….. ????

*Matar Soja*

5⃣7⃣&5⃣8⃣

…………… Tunda ya shiga ya hango ta a zube a gadon ya shiga tashin hankali, idanun ta ta bude a karon farko ta zuba mai idanu, so take ta motsa jikinta amma bazata iya ba, bakinta takeso ta bude bazata iya ba, domin har d’an karkacewa yayi kadan, ta rame a cikin Kwana kadan, wasu irin hawaye ne masu zafi suka biyo kumatun shi, for the first time yana regret na bijirewa umarnin ta koda zai mutu, saboda soyayyar uwa da d’a sai Allah, da kyar yaja jiki ya matsa wurin ta tareda dafata yasa kuka mai ciwo, “Am sorry mommy na am sorry”, nasan da yaya Ahmed ne bazai taba barinki a cikin wannan halin ba, gashi ni na barki mommy, am not a good Son mommy am sorry. 

So take ta lallashe shi tare da nuna mai baida laifi amma bazata iya ba, sai hawaye da kebin kuncin ta itama, dagowa yayi cikin sauri, ya share mata hawayen ” please don’t cry momy”, zanfita dake ko ma wacce kasa ce zaki warke da izinin Allah. Yayi saurin tashi ya koma wurin likitan. 

“Doctor zan iya tafiya da ita China kai tsaye ba wata matsala? eh babu saidai mun dorata akan medication na tsawon sati daya, muna so muga ni idan maganin ya karbeta nan da Kwana uku munga cigaba basai ka Fita da ita ba, so have some patience sir khaleel. 

Haka ya fito a sanyaye idanun shi sunyi jawur, tundaga nesa taji ba dadi tana ganin Yanayin shi tasan ba lafiya, 

Har ya matso tareda bawa manager umurni kai tsaye fuskar shi ba walwala, “take my wife home” 

Ya juya yana Kara yiwa kawu bayani, jikinta yayi mugun sanyi y’an da yaki ko kallon ta kuma tana ganin damuwa karara a fuskar shi, daga dawowar su mommy tafara shiga tsakanin su ne ko kuma ciwon tane yasa ya shiga wannan mood din? 

Kasa tafiya tayi ta matsa ina dakin inganta kafin in tafi? Tafada cikin kwantar da murya, 

“Kije gida no need, batada lafiya banason Abinda zai daga mata hankali kuma. 

Kallon tuhuma take mai ba tare da ta gano manufar shi ba ta juya cikeda sanyin jiki domin batada zabi, 

“Hajiya ina zan sauke ki? Shiru tayi kadan tana tuna ai ba a gidan shi ya dauketa ba don haka ko yanzu gidan Aunty Raliya tace suje domin batasan me zata fada ba in taje gidan malam. 

Tunanin Yanayin shi takeyi a zuciyar ta, they are just fine kafin suzo Asibiti, meya faru? Haka take ta tunani har suka isa gidan Aunty, akwatin ta ta cire tace yaje da nashi kawai. 

Aunty Raliya tayi matukar mamakin ganin ta kamar daga sama Saida ta tsorata. 

“Naziya saukar yaushe? “Yanzu muka shigo”… Tayi mata bayanin mommy ce ba lafiya tabar shi a Asibiti, “to ke meyasa baki wuce gidan kiba? 

“Aunty ba anan ya daukeni ba da zamu tafi ko kin manta meya faru? toh Naziya naga kuna lafiya kalau da mijin ki me zaisa ki dawo gidana? ” ko in tafi gidan malam ne ? Tafada cikin fushi kadan da ya hadu dana khaleel ga tanbayoyin Aunty Raliya ga wata irin anger da takeji a zuciyar ta, “Aunty Matar shi na cikin gidan wadda akeso ya Aura mezan je inyi a can? 

A’a kanwata duk dai haka bata tasoba, welcome back little sister, irin wannan fushi daga ganin ki kinyo mana tsarabar d’an China ne ko bangkok? 

Kinga y’an da kika koma kamar atabaki jini ya fito jikin ki kamar wadda aka saka a engine, ai da badon nayi miki kyakkyawan sani ba bangane ki Naziya. 

D’an murmushi tayi kadan, duk da haka zuciyar ta nakan khaleel, Sai da ta huta, Aunty Raliya ta bata Abinci taci kadan ta watsa ruwa, Aunty Raliya ta zauna gefen ta “Naziya akwai matsala na lura, meke faruwa ne meke damunki? Shiru tayi da kamar bazata yi magana ba Amma bata iya boyewa Aunty damuwar ta, da in ina tafada mata Abinda ke damunta. 

“Mtsww kin dagamin hankali a banza, kika sani ko ciwon nata yayi zafine shiyasa kika ganshi haka, banson shirme ni banga Abun damuwa a cikiba. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button