AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 31 to 40

Saida ya kwashi hour guda yadawo, lokacin har tasamu bacci an daura mata drip da Allurai, 

Likita yasamu tace “we need to talk sir” let’s go to my office. 

Saida ya matsa gaban gadon da take kwance, fuskar ta harta fada a dare daya, wani irin tausayin ta yakeji, hakurin ta yayi yawa, a hankali yake fahimtar ita din batada hayaniya tanada hakuri mace ce mai biyayya, Naziya bazai iya hadata da komai ba yanzu a rayuwar shi, Kirjin ta ya shafo ya Fita, 

A zaune doctor din take tana rubuce rubuce, yaja kujera yace ” Any problem doctor? ” yes sir, please kar akuma yimata irin haka, domin taji ciwo ta ciki shiyasa take bleeding, akiyaye gaba arika bi a hankali ba guduwa zaiyi ba you have just started ne, yanzu drip din da na bata zai taimaka mata tasamu karfi, at least tayi two weeks stitches din su warke. “Stitches? Ya tanbaya cikeda damuwa, ” yes ba da yawa bane kadan ne, ka bata two weeks everything will be Aright. “Tank you doctor. Yafada ya Fita tana binshi da kallo, “yarinya dole kiji jiki irin wannan miji naki daga gani kin boni. 

Zama yayi tareda yin tagumi ya zuba mata ido kamar zai cinyeta, ” you deserve to be happy baby, why Mommy ta kasa gano cewa kedin kinfi sauran matan da take so ne , why she hate you? Kyakkyawar fuskar ta ya shafo yayi Ajiyar zuciya, tareda ciro wayar shi a Aljihu ya shiga contact yana searching numbers, ganin number da yake nema yasa yayi dialing, ringing biyu aka dauka, mikewa yayi ya matsa, ” Aunty Ina Kwana. “Khaleel kaine ? Ince ko lafiya? “Lafiya Aunty sai dai muna Asibiti da Naziya yanzu, please inba damuwa inzo in dakko ki? ” Toh meke damun ta haka harda Asibiti?  

Bai taba sanin yanada kunya ba sai yau da yake magana da Aunty Raliya, don haka ya sosa keya yace zazzabi ne kawai. “Toh yanzu Baban yara zai Fita zanbiyo shi, wane Asibiti ne? Yafada mata, tace tana zuwa, yayi godiya tareda Fita yasamu doctor. Yace yana bukatar taimakon ta, “please sister din madam na zuwa you have to explain to her Ina so ta tafi da ita tasamu kulawa kafin in tafi da ita gida, kar asamu matsala gaskiya, two weeks is too much for me. Yafada da zuciyar shi daya, ido kawai ta bishi dashi tace ba matsala, yayi godiya ya tafi………. ????

Not easy for me guys sorry please ???? 

*Matar Soja*

4⃣3⃣&4⃣4⃣

08032252760

08175479641contact this numbers for more information 

………… A gida bayan fitar su da sauri ta fada dakin nashi, taga zani daya a kasa ga nakan gadon ma yayi kaca kaca, wani irin turnuki taji a zuciyar ta, wato khaleel da ace Asibiti ta haifeshi da tace anyi mata canje, ta manta da kana haihuwar Wanda yafika tsaurin ra’ayi, kwalawa mai aiki Kira tayi, ta nuna mata dakin cikin takaici ” clean this mess right away. Ta Fita sai zagaye takeyi tana neman mafita tarasa ta Ina zata bullowa Al amarin khaleel, Zarah ta Kira tunda farar Safiya, ” Aunty lafiya fa safen nan? Tafada cikin tsoro, ” Ina fa lafiya zarah, ni bangane aikin malamin nan ba waya rana yayi wata rana kuma lamari ya barkace. ” meyafaru Aunty? ” khaleel….. Tafada mata komai in details. “Kema Aunty ke keja ki cire idanun ki aiki ai ahankali yake farawa kuma idan kika matsa za ayi biyu don tsab khaleel zai sallami salifa. “Bazaiyi ba don yana tsoron tsinuwa ta shiyasa ko yanzu na fada mai karta dawomin gida inba hakaba banyafe mai ba. “Kash Aunty me kikayi? Kinsan dai bazai sake taba, what up ya nema mata gida daban? Dafe kirji tayi ta tuna da kalmar shi bazai taba sakin Naziya ba, kuma tasan halin Abinta, “zarah kice na bato lamari? “Gaskiya Aunty wata rana bakya shawara kike aikata Abu, bakya yin Abinda ya dace. “Zan janye tsinuwar bari inkirashi in lallaba shi don karya sauke akan salifa. ” zai aikata kinsani sarai bai barin Abu abanza. 

Kashe wayar tayi ta fara neman shi jiki na rawa. Lokacin ya fito daga Asibiti domin duk hankalin shi na cikin dakin yanda yabarshi yasan momy bazata gyara ba, yaji karar wayar ta, dauka yayi kamar nothing happened, ” khaleel Ina kakai yarinyar nan? Shine tanbayar da tafara yimai, yayi shiru kadan yace ” Ina hanyar dawowa am close, ya kashe wayar. 

Yana dukan sitiyarin yana fesar da numfashi, ” I will fight this battle alone Yaya Ahmed, Allah ya jikan ka ya biyaka da Aljannah. Yafada yana jin duk wani damuwar sa ta gushe da ya tuna da cikin ni’ima da farin cikin da ya Kwana, Aure dadi, Naziya karshe ce a cikin mata, tuni yafara kewar ta yaji kamar ya juya ya koma ya rungume ta, jin kanshi yakeyi a sama, koda ya shiga gidan ya parking, masu aiki na gaishe shi yana amsawa cikin fara’a da wani irin Annuri. Gefen momy ya wuce, tana tsaye tana zagaye taja doguwar Ajiyar zuciya ganin shi, ta tashi, matsowa yayi fuskar shi a sake ya zauna a gefen ta ” momy good morning, dazu na Fita ba a natse ba. Kallon fuskar shi tayi tana hango sheki da Annuri tareda kwantaccen farin ciki a fuskar shi,  

“Khaleel Ina ka kai ta? Answer me? ” Momy in her condition Ina yakamata inkaita inba hospital ba? And forgive me if I did anything wrong to you, Ina so inyi miki biyayya momy nima one day kiyi min Addu’a exactly yanda kikewa Yaya na, idan nabata miki rai, forgive me bakin ki guba ne dafi ne, fushin ki damuwa ne, Ina sonki mama na, please ki tayani son Abinda nake so, Momy kin tanbaye ni why I marry Naziya without rejection? How can I reject the woman I love more than my life? Momy Ina son Naziya tun Yaya na na Auren ta batareda nasan zan mallake taba, kince karta dawo cikin gidan nan, bazan dawo da ita ba, insha Allahu I will obey you Momy. Ya zabura ya kama hanyar dakin shi takasa cewa komai, sometimes sai zuciyar ta taso tausar ta saita kasa so take ta bashi hakuri Amma tunanin Alkawarin da tayiwa kawarta da kuma ego dinta ya hanata tana kallo harya shige dakin lokacin maid din na kokarin shinfida mai wani bedsheets, wani irin tsawa ya buga mata ” ke uban waye yace ki taba min kaya? Get out.  

Jikinta na rawa ta fice, ya kwashe zanin gadon masu stain ya kwabe ya shiga bathroom da kanshi ya wanke su tas Abinda bai tabayi ba wanki irin wannan, 

Saida ya gama ya dawo cikin dakin ya canja bedsheets da kanshi, ya daura towel ya shiga bathroom saida ya hada ruwa mai zafi ya shiga ciki shima domin shikan shi yana bukatar su, kwanciya yayi yana wani irin murmushi mai cikeda da ma’anoni, “baby this is your work fa, kinsani gashi, all my joint are paining me, what a sugar. Yafada yana sude lips domin he can still feels her sweetness, 

Imagine yake idan ta warke how he is going to spoil her, yanda bazata iya rayuwa batareda shiba, ” we are going far away from all this problems. Ya dauki dogon lokaci a cikin ruwan kafin ya fito, zama yayi gaban mirror ya fara kalkale ko Ina na jikinshi, kafin ya fito dakin, saida ya gama nazari kafin ya fito da wata farar shadda, ” am ango today. Ya zura harda hula ya ciro agogon shi ya daura tareda katon Azurfan shi, 

Kamar ka sace shi ka gudu, haka ya baza kamshi, ya kwashi wayoyin shi ya fito harda nata, 

Yana fitowa tana sawo kai cikin karai raya da sanabe, lokacin da tayi arba dashi saida ta kusa zubewa saboda ya tafi da imanin ta, ” wow is he really my husband? Oh my gosh. Kamar invisible haka ya ganta, ya fito da wayar shi dake Kara ya yi saurin picking, “Aunty kinzo ne? OK gani nan zuwa. Yafada yana wuce ta cikin sauri. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button