AUREN GADO Page 41 to 50
Ita kanta ta san ya isowa tunbai karaso ba, don haka tuni ta Kara hade fuskar ta tamau domin tayi mugun daukar fushi dashi, tuni ya ji wata natsuwa ta ziyarci zuciyar shi, cikin takun kasaita ya shigo, hade da sallama kasa kasa idanun shi a sama, domin ba Abinda yake buri sama da yayi ido biyu da ita, yayi matukar kewar ta, sai jera Ajiyar zuciya yakeyi tunda ya sauke idanun shi akanta, gangar jikin shi tuni ta amsa gayyatar ganin ta da tayi tank God ma manyan kayane a jikinshi, a bu biyu yanzu zai hanamai rungume ta ya rafe zafi, nafarko Aunty Raliya na biyu momy, don haka ya saita kanshi yayi gyaran murya, tareda gaida Aunty, tamai ya gajiyar hanya da mai jiki, ya Amsa cikeda jin kunyar ta.
Dago kanta tayi ta kalle shi cikin fushi tace ka sakarmin hannu idan kai bakajin kunyar idanun momy ni inaji please let go. “Never ever, if I let you go in zauna da wa? “Your second wife da kakeson kasancewa da ita that’s why ka koreni batareda kama bari na duba lafiyar Momy ba jiya that’s why na koma inda dama ka dakko ni kafin mubar kasar nan, ni nasan matsayina banda wani value a wurinka, kuma am not here because of you, nazo saboda nadamu da lafiyar momy tana warkewa shikenan.
Wani irin kallon what is wrong yake mata, momy feels bad saboda itane duk wannan mis understanding din ita tajawowa d’an ta, kallon Naziya tayi taga ita din dai data raina ita tafi dacewa da d’an nata ga hakuri da tarbiya, don haka taji duk duniya ba Abinda takeso yanzu kamar ta warke ta gyaro kuskuren ta,
Mikewa tayi da cup din ya Kara rikota, ” Naziya please stop it, ko so kike ki dagamin hankali um? Dagowa tayi taga momy ta rufe idanun ta, ta ce “I said let go of me. Shima kallon momy yayi kafin ya Kara matsota cikin rage murya sosai dake dauke da damuwa, “meye nayi kike kokarin horani haka please am sorry koda ni bansan laifina ba kiyafe min but I can’t handle your anger on me.
Fisgewa tayi ta yi bathroom domin dauraye cup din da spoon, ya runtse idanun shi tareda dafe kai ” oh my god khaleel ka boni. Yafada tareda binta cikin sauri, tana kokarin fitowa ya maida ita tareda datse kofar, “kallon shi tayi fuskar ta a tamke “meye haka Aunty Raliya zata iya shigowa kuma kasan momy dai Nagani ko? ” Hmm so what? In zaki yi kokarin horani da irin wannan new attitude din ya kikeso ni inyi behaving, tell me? Look am not use to this, and I can’t take it any longer please forgive me if I wrong you.
Ji tayi yakara tunzura ta wato shi baisan laifin shiba, don haka cikin zafi ta dago tareda cewa ” ba Abinda kayimin kawai bana son damuwa leave me alone OK.
“Hhhhh story, rubbish, you are insane Naziya, leave you alone, ni khaleel? You are dreaming wallahi, ban hakura dakeba tuntuni sai yanzu da kika gama shigewa cikin rayuwata kika yimin dalla dalla, hannun shi yasa cikin sauri ya fisgo kugunta ya hade ta da Kirjin shi, Saida yaji kamar ya shekara bai kusance taba saboda shauki da kewar ta, “Ahhhhhh Hmmmm. Yafada tareda kankameta kamar zai mayarda ita cikin jikin shi, kokarin kwacewa takeyi ya hanata dole tayi lakwas tana sauraran bugawar zuciyar shi tareda rawar da jikin shi keyi kamar bai saba rungume taba” baby banyi bacci ba jiya kinsaba min da yin bacci kina saman kirjina bayan kin shayarda ni zumar ki tareda madarar ki mai rikita kwakwal war mutum, why kike fushi dani why kika barni nikadai jiya why kike son ki gujeni bayan kinsan zuciya da gangan jikina bazasu dauka ba?
Samu tayi ta fisge haka kawai taji yanaso ya tayar mata da feelings a Asibiti a banza yabarta da Abin kunya, tana juyawa ya kuma hade jikin shi da bayanta yasa hannu ya rungumo Dukiyar fulanin ta tareda matsawa kadan yana gwama numfashi, “Am honey, kinji let go home yanzu zamu dawo please baby. Yafada yana goga mata jikinshi, she can feel how hard he is, tayi saurin bude kofar domin takai gab ta fisge ta gudu.
Matsawa yayi baya kadan ya dafe bango tareda runtse idanun shi ya dade a wurin kafin ya d’an dawo hayyacin shi,
Ta gyarawa momy kwanciya tareda komawa gefe taja kujera ta zauna, Aunty Raliya tashigo, Wanda har lokacin bai fitoba, tace “ni zantafi nabar yara Allah yakara lafiya Ina khaleel din? ” gani Aunty yafada kanshi kasa domin yasan for sure yadago fuskar shi zata ga canjawar idanun shi, yace “bari muje in sauke ki tom, “Aa Wallahi ga mota nan megidana ya aiko yaron shi Allah ya bata lafiya.
Godiya yayi mata Naziya ta rakata ya zauna tareda bin bayanta da Kallo yana tausaya wa kanshi, Saida Auntyn ta tafi tadawo,
Still fuskar ba walwala, ya kalleta cikin da tausayin kanshi yace ” muje ne? Banza tayi mai ta dauki Jakarta karama ta ciro wayar ta ta kunna.
Tafara game, karkace kai yayi yana kare mata Kallo tundaga fuskar ta har zuwa kirjinta har kafafunta data zame takalmin ta dora daya kan daya, jajur dasu mulmul, ya hadiyi miyau Kut a zuciyar shi yace ” kinada Abinda duk zakija min aji yarinya is your time. Haka suke zaman kurame Wanda har doctor ya shigo tareda duba momy yafita, suka cigaba da zaman haka badon zuciyar shi nasoba sai dan baida yanda zaiyi, idanun ta akan su momyn khaleel din ma kebata tausayi yanzu da tanada baki da ta lallashi Naziya domin ta rikemata yaro hankalin shi ya kwanta,
Sallamar su Shukrah da malam harma da Inna da sadiq ne yasa ta zabura cikin matukar murna ta nufesu, shima mikewa yayi cikin girma mawa ya gaida surukan nashi, malam yace yamai jikin? Sukace Alhamdulillahi.
Matsawa tayi zata rungume Inna tace ” ke bani wuri ingaida mai jinya mara kunya. Shukrah tayi dariya tace Aunty nidai Rungume ni nayi kewar ki. Suka rungume juna yana kallon duk wani motsinta kamar ya sace ta ya gudu yakeji, ganin ta yakeyi kamar ma bai taba Rayuwa da itaba,
Komawa sukayi gefe itada Shukrah su kuma suka matsa jikin gadon suka fara gaida ita, “Sannu Hajiya Allah yasa kaffara ne. Inji Inna da sai yau suka hadu da juna ido da ido, kallon iyayen Naziya takeyi tana hango tsantsar datti jantaka a fuskokin su, malam yace “kulu ciromin Ruwan zam zam din nan da kunnen magaryar. Yafada yana zama gaban gadon, a wurin ya balle Y’ar Karamar robar Inna tabashi cup ya juye ya fara Addu’a a ciki tareda mutsika ganyen magarya yace Naziya zo ki karba ki juye a gora kuna shafa mata a hannu da kafafun ta har fuska sau uku a yau.