AUREN GADO Page 41 to 50

Kudi na musamman tasa khaleel ya ware tareda gina wata babbar makaranta mai suna Ahmed foundation, wadda take taimakawa marayu da basuda karfi suke samun kulawa sosai batareda ko sisin suba,
Momy ta Ajiye aikin ta tuni bata zuwa sai kula da y’an jikokin ta, haka zata zuba Abinta a mota suje ziyara gidajen y’an uwa, har gidan malam sai suje su wuni susha hirar su sai sun ishi inna da barna tace “Hajiya balkisu ki kwashi mazajenki sun isheni da barna suna fama da jajayen kunnuwa. Haka zasuyi ta raha a tsakanin su, haka take zuwa gidan kanin mijin ta ma, ta canja sosai kamar ba itaba,
A cikin wannan satin su Naziya suka shirya fita bangkok kamar duk kowane karshen shekara yanzu saboda kasuwancin shi. A dai dai lokacin Ummul khair nada wata takwas kuma tagano tana daukeda wani cikin don haka ba wani dogon bayani ta cireta tareda Ajiye wa takwarar ta tabi mijinta domin su hole, tuni ta gano cewa Matar so ke gwarne don haka ta daina damun kanta domin duk cikin dazatayi khaleel na farin ciki, toh meye damuwar ta Sai muce Allah ya karo Arziki da zaman lafiya a tsakanin wainnan ma Aurata…… Pen’s ????
Alhamdulillah nagode wa ubangiji da ya nufeni da ganin karshen wannan littafin
Dubun godiya gareku masoya aduk inda kuke, my Real fan’s wato AUREN GADO paid grp one and two, domin kune real fan’s dina domin kun nunamin kauna da soyayya ta hanyar rububin siyan wannan labarin, fatan Alkhairi agareku bazan taba mantawa da Alkharin ku da hakurin ku gareni ba,
Ina rokon Afuwa saboda yanayi na jinkiri da aka samu akan wannan labari, ba son raina bane kana naka Allah na nashi, this is the though time for me saboda situation dina, am sorry duk Wanda na batawa rai a wannan tafiyar, saboda ajizanci na d’an Adam, ku yafemin don girman Allah.
Darasin da na ke son y’an uwa su dauka a wanna lbr shine, kaso mutum don Allah,mucire hassada son zuciya handama mugodewa ubangiji da duk Abinda yabamu a Rayuwa, sannan kuma Muna fatan muyi kyakkyawan karshe irin na momy Allah ka nufemu da gyara kura kuranmu kafin mutuwa. Ayi Amfani da Abinda zai amfane mu a wannan lbr sannan mu watsar da duk Wanda baida Amfani kuskuren da ke ciki Allah ya gafarta min Alkharin dake ciki Allah yasa Al umma su anfana dashi,
Dubun godiya gareku masoya da nake bawa a pc kunada yawa, lallai soyayyar ku babbace a wannan labr da kuma gareni Nafisa na yinku over Allah ya karo Arziki ya kareku daga dukkan sharri.
*TAMMAT BIHAMDILLAH*
[ad_2]