AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 41 to 50

Malam ya dade da sanin wasu mutane basuda yadda shiyasa bai hado komai ba yayi wannan agabanta idan taji sauki bakinta ya bude zai iya bata wani, a take Naziya ta yi y’an da malam yace Wanda tunda ake shafa mata a kafafun takejin wani irin sanyi hade da jin jikinta na rage nauyi kamar tace kar Naziya tadaina, a ranta nadama takeyi mara Amfani wasu hawaye take fitarwa na rashin bakin da zatayi godiya, 

Khaleel kamar ya goya su yakeji y’an suka nunamai karamci da kulawa, yana Kara godiya da Allah ya hadashi da surukai nagari, basu dade ba suka tafi, yarage daga shi sai ita, matsowa yayi yace “am hungry madam in baza abani Abincin cikin rigaba abani Abincin da zanci. Yafada yana rage murya tareda kashe mata ido, mikewa tayi ba musu ta zubamai Wanda su Inna suka kawo shinkafa da naman zabbi, 

Ta hado mai da ruwa mai sanyi domin akwai dispenser a dakin ta Ajiye ta juya. 

“Kinsan tun jiya banci komai ba kuma kinsan bana iya cin Abinci nikadai yanzu kizo muci. “Ni ba wannan nakeso ba. Tafada tana tura baki. “Oh lobster or crabs? Yafada cikin mamakin y’an da ta juya cin wainnan Abubuwan. “Ni shrimps nakeso. Iyakar gaskiyar ta tafada, ya fara cin Abincin shi Saida yayi kat yasha ruwa, ya gyara zama, zuwa tayi tadaga plate din ta saka a, basket tadawo tareda tsayamai akai, “yunwa nakeji nima. Tafada cikin fushi domin yasan sarai me takeso, ” bude idanun shi yayi yace ga Abinci nan kici in kuma nine muje sai kin koshi. 

Komawa tayi can kusa da momy ta zauna, Abinta ta share shi, tashi yayi ya fita, Wanda yana fita y’an uwan shi suka shigo daga gidan kawun shi. Haka tayi ta karbar baki bayanan har zuwa magrib ta rage ita kadai, ta kuma shafewa momy jiki da ruwan Addu’ar, anan take shinfida dadduma tayi sallah domin kayanta a yalwace suke, bai shigo ba sai bayan isha’i. 

Ya matsa tareda gaida momy kafin ya ce ta tashi lokacin tafiya yayi su tafi gida don ba akwana anan. “Ba inda zanje inbarta ita kadai intana bukatar wani Abu fa? ” nurse na nan. “Am not going nama fadawa doctor zantsaya kuma ga ruwan maganin ta Anjima zankara shafa mata, kai katafi. 

Kamar ya dora hannun shi a kai ya buga ihu yakeji, “look kinga banason musu kitashi mutafi. Momy naji kuma tana gani so takeyi tayi magana ba dama, 

Tashi ma tayi ta haye gadon dake dakin extra ta kwanta tareda jan net bayan ta saukewa momy nata, tabashi baya. 

Abun ya matukar konamai rai don haka a zuciye yabar Asibitin, yayi gida. 

Inba haka tayi ba bazai taba barinta ta Kwana da Momy ba ita kuma so take ta kula da ita saboda tasan a duniya batada ya’ya sama da Ahmed da shi gas hi ba Ahmed Khaleel kuma namiji ne, kuma bai kamata wata nurse na wani kula da itaba, 

Don haka ta zamo mata ya’ koda bazata godeba zatayi domin Allah. 

Wani irin farin ciki momy keji ganin y’an da Naziya ta jajurce wuni guda tana bata kulawa. Sai dai rashin jituwar su yasa abun ya taba mata zuciya, ba Abinda take buri yanzu sama da ganin farin cikin khaleel da Naziya. 

 

Gida yatafi kai tsaye badon yasan zai iya bacci ba, ya kwanta yanata fushi a kujera ga gidan bakowa cikin shi sai masu aikin shi tsoffi da yadawo dasu, harma da mai gadi bayan ya kora Wanda suka kawo. 

Har karfe goma na dare yakasa natsuwa haka ya canja zuwa kanan kaya ya dauki key din motar shi ya kuma barin gidan. 

Naziya Saida ta kuma shafe momy tsab da ruwan Addu’ar ta kunna musu waya tasa kira’ar sudais cikin suratul bakara tareda Ajiyewa kusa da gadon momy ta koma nata ta kwanta bayan taja mata bargo, murmushi kawai momy keyi najin dadi ya’ daga sama wadda tafi ma d’an ta damuwa da ita, haka tayi baccin ta mai nauyi cikin salama tareda jin duk wasu igiyoyin da suka daure jikin ta suna kwancewa a hankali. Ita kanta Naziya tana bukatar hutawar domin d’an baccin ma da takeyi na rana yau bai samuba don haka tana kwanciya yayi awon gaba da ita, 

Kamar a mafarki takejin hannun mutum a Kirjin ta tareda jin nishi kasa kasa, wai don ma yana controling kanshi karya samata ihu a Asibiti. Jin jikinta na canjawa yasa tayi saurin bude idanun ta, dayake akwai d’an duhu sai hasken dake shigowa kadan daga window domin tayi switching light din, mugun tsorata tayi jin mutum laulaye da ita gaba daya hannayen shi damke da kirjinta gam, sanin zata iya samai ihu yayi saurin rife bakinta yana rage murya tareda cewa ” it’s me baby. 

“Hmmmm tayi saurin dafe kirjin ta ta zabura tana sauke rigar ta daya kwashe mata. Matsowa yayi ya janyota tareda zaunar da ita saman kafafun shi ” hey relaxed, kinga fushina ba inda zaije nadawo because I can’t sleep, the house is too big for me, please baby I really needs you kinsan bazan iya hakurin da nayi a bayaba, karki yimin irin wannan horon. 

Y’an da yake magana ya mugun bata tausayi don haka ta d’an natsu a jikinshi, 

“Kai wai bakajin kunyar idanun momy ne in taganka fa? Ni dai kayi hakuri inna dawo gida kabari momy ta warke.  

“I said I can’t why don’t you understand? 

Yafada cikin tsawa da fada, “you are my wife ya zaki rika garani saikace ba halalina ba how many times kikeso in lallaba ki? 

Momy Saida ta farka saboda tsawar da ya bugawa Naziya, cikin ikon Allah ta bude bakinta tace “khaleel! Kamar daga sama sukaji muryar ta duk da maganar bawai ta bude sosai bane, da gudunsu suka matsa kusa da ita, Naziya tayi saurin gyara kanta ta kunna wutar dakin suka ganta tana kokarin mikewa, wani irin farin ciki ne yasa ya ji duk wani bacin ranshi ya kau ya rikota tareda cewa “momy you talk, kuna kintashi zaune? Cikin so much excitement, itama ta matso kusa da ita tace “sannu momy tana boye hawayen idanun ta domin tsoro biyu ne ya hadu mata, ga fushin khaleel ga tsoron Abinda Momy zata yimata tunda kuma daga gani sauki yazo, kallon ta tayi kafin ta kalli khaleel dayayi kicin kicin tace “meya miki kike kuka? Khaleel meyasa bakada hakuri da daren nan kana yiwa yarinya ihu duk da gajiyar da tayi.. 

Wani irin hawayen farin ciki ne ya Kara shatatowa daga idanun ta, batayi zaton haka daga momy ba, shikan shi yaji mugun dadi don haka yace ” tanbaye ta ni ba Abinda nayi mata impact in kukane ma nine yakamata inyi ba itaba, do you know momy tundazu nake lallabata muje gida ta nace ita nan zata Kwana tare dake saboda taurin kai. 

Hannun ta datakeji ya saku sosai guda daya ta mika tareda riko hannun Naziya zuwa kusa da ita, ” Zo kinji daina kuka inbakya son zuwa ba mai matsa miki kinji, Amma in saboda nine kitafi gida ki huta kinga am OK zan iya gyara kwanciya ta zan iya tashi hannu na dayan nan ne da kafar hagun nan nakejin su a rike, Alhamdulillah nagode wa Allah nagode miki keda iyayen ki Naziya Allah yasa ki gama da duniya lafiya. “Amen Amen Sukace, farin cikin su baya misaltuwa a wannan lokacin, tace “in kina son binshi kije da safe kya dawo. 

“Banason zuwa momy ni ina nan. Tafada batareda ta kalli khaleel ba, 

Fuskar shi ya tamke yayi banza da ita, 

Tace “kije kiyi kwanciyarki kinji kibarni dashi nasan kin gaji. 

Wannan canjin na momy yafi komai faranta mata zuciya don haka bataso tayi Abinda zata bata mata rai har su koma Y’ar gidan jiya don haka ba musu ta wuce Abinta, momy tace ya tashi ya kashe hasken ya kunna musu na wayar shi magana zata yi dashi kar hasken ya damu Naziya zatayi bacci. “Ya tashi cikin murnar ganin momy taji sauki ga kuma canjin hali da ya lura tayi tuni ya goge mai duk wani fushi da yakeyi ya hakura da Abin da ya kawoshi ya zauna tareda gyara mata zama don tace ta gaji da kwanciyar jikinta na ciwo, 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button