AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 41 to 50

Khaleel kuwa bayan ya shirya Saida yaje office dinshi yaga meke tafiya domin baisamu sukunin lekawa ba ya d’an dauki lokaci kafin ya dawo Asibitin, Samun momy yayi da Aunty Zarah da tadawo jiya ta samu labari a wurin Aunty Raliya domin duk ta damu bata samun wayar momyn Kwana biyu, fuskar shi ya tamke ya shigo kamar yaga kashi don Allah yagani ya tsani Matar nan shiyasa ya mugun raina ta, hawaye takeyi tana Sannu aunty Allah ya wulakanta sharefa da zuri’ar ta matsiyata. Sallama yayi ciki ciki ya samu gefe daya ya zauna ta juyo cikin fada ” khaleel Amma wallahi kai bakada kishin mahaifiyar ka, yaza ayi ace Suyi ma Aunty irin wannan Abun Amma ka zuba ido ka kyale su? 

“Zarah kije ke kidauki mataki da kanki dama kece mai babban kaso a duk Abinda yake faruwa a rayuwar gidan mu, don haka karki manta inkin tashi yimusu hukunci ki hada da kanki kema kina bukatar hukuncin. 

“Kingani ko Aunty wallahi Ibrahim ya mugun raina ni sai kace ba kanwar uwar ka nake ba kayita zuba min magan ganu son ranka, wallahi zandauki mataki akanka mtsww. “Hope dai badani kike wannan zancen ba da kuma tsakin, domin Zaki iya fuskantar bacin raina fiyeda tunanin ki, girma na kikayi ko kece kika haifeni da zanbaki girma? Look we don’t need you here just leave, go and fix your life first, don munafunci ina kike lokacin da ita yayar taki ke bukatar taimako? Were are you? Sai bayan ta samu sauki ki debo dogayen kafafunki kizo kina kawo mana sanabe were are all your relatives, sai lokacin da munafunci ya tashi ku cikawa mutane gida, look am not like Ahmed duk wadda tasan ba zumunci zai kawota gidan muba she is not welcome, kowace ta tsaya gidan tsohon mijinta, especially you Amara. 

Tuni Aunty Zarah ta hadiye bala’in ta ganin ya hau yana faman surfa mata that means ajiraye yake da ita, momy ce tace ” khaleel that enough OK. Yace “Sorry Momy were is that girl? “Taje ta yi wanka ta canja tadawo. Dama yasan zatayi hakan wato bazata iya fada mai Abinda take bukata ba sai kawai Tayi Abunda taga dama don taga yana sonta yana lallaba ta, OK zai nuna mata koda yana son mace kuma baya daukar wulakancin ta why take mai yawo da igiyar Aure any how? Haushin ta ne ya saukewa Zarah tass tun ma baiji meya faru ba. 

Komawa yayi kan kujera yana Danna wayar shi fuskar shi kamar hadari, momy ta kalle shi tace ” khaleel bansan me ke ranka ba, Amma na rokeka haukar da kamun yanzu ta iso kar yarinyar nan tadawo ka rufemin ita dafada. 

Shiru kawai yayi domin yakai wuya, zarah kuwa mamaki take ciwon ne ya janyo momy har take damuwa da Naziya haka? 

Kallon ta Tayi tareda yin murmushi kawai. Domin ta Riga tadawo hanya sambal bata fatan ta kuma karkacewa, 

Aunty Raliya tasa aka dawo da ita bayan ta tashi ta shirya cikin kana nan kayanta ta zura katon hijab saboda shigar domin duk native wears dinta na gidan khaleel, harda socks ta sa baki, 

Bayan ta zura after dress a sama saboda koda zata bukaci cire hijabin a Asibiti, 

Wata irin uwar kasala takeji da tashin zuciya, da batasan dalilin shiba don haka duk sai jikinta ya mugun mutuwa, koda ta shigo cikin Asibitin zuciyar ta tashi takeyi sosai musamman kamshin pharmacy dake tashi a Asibitin, 

A cikin natsuwa ta shiga dakin bakinta daukeda sallama yana nan zaune a wuri daya, muryar ta da yaji tuni zuciyar shi ta sauka yaja numfashi tareda zuba mata ido, ta matsa tareda gaida momy da Aunty Zarah da ta zuba mata ido itama tana ganin mugun canji da murjewar da Naziyar Tayi, 

Ta koma kusa dashi ta gaidashi tana yamutsa fuskar ta domin jitake kamar ta koma saboda tashin zuciya,shikuwa kallon al amarin ta yakeyi yana noticing komai duk Tayi sanyi lakwas, tana zama cikin ta ya mugun murdawa Amai ya taso mata, da gudu Tayi bathroom suka bita da Kallo dukan su kafin ya mike yana mamakin ta ko lafiya? 

K’ak’arin Aman da takeyi yasa momy ta daka mai tsawa ” kabi yarinyar nan kataimaka mata ka tsaya k’ik’am kamar sabon soja. Jefa wayar shi Aljihu yayi tana rikeda washing hand basin sai kwara Amai takeyi ya karaso tareda dafata yana mata sannu, yitakeyi kamar zata Amaye y’an hanjinta dama tea kawai ta karasha bayan ta tashi baccin, Saida ya bata ruwa ta wanke bakinta ya fito da ita, momy jitake kamar ta mike ta taimaka mata da kanta, kwantar da ita yayi akan extra bed din tana maida numfashi, ya zare mata hijabin, “ka Kira likita ya dubata ka tsaya nan kana kallon ta banson shirme. Momy ta fada, duk da zuciyar ta tagama fada mata damuwar bataso Tayi farin ciki saita tabbatar, inko cikine da tafi kowa farin ciki. Yana fita Zarah tace “Aunty ai wanna dagani ba tanbaya ciki ne da ita, don ni tun shigowar ta naga yellow din da Tayi nasan juna biyu ne. “Allah ya Y’ar da da zancen nan Zarah. Momy tafada tana shafa hannun ta mai lafiya, 

Likita ya biyoshi ya shigo tareda nurse, yafara tsokanar ta ” mai jinya ta koma patient. Jinin ta ya deba yabawa nurse yace taje takai lab ayi P T test. 

Bayan minti talatin ta dawo da result, 

Khaleel na zaune ya na mamakin what is wrong with her, ta rufe jikinta da hijabinta ta juya mai baya domin kamshin jikinshi ma is killing her, likitan ne ya shigo fuskar shi a sake, ya mikawa khaleel hannu “congratulations sir, a zuciye ya mike kamar mai jiran a taboshi “my wife is sick and you are congratulating me? “Relax Sir Ibrahim, your wife is pregnant. 

Yafada yana Kara Washe baki, saurin juyowa Tayi idanun ta a waje “pregnant? Ciki kenan fa? Ita keda ciki? Ciki fa??. 

Momy dake jingine ta gyara zama kamar ta sakko takeji ta daga Naziya ta goya sai kabbara takeyi, zata samu Karin zuri’a, zataga jikan ta Wayyo dad’i. 

Khaleel kuwa d’askarewa yayi kamar Wanda ya suma, bai taba imagining ciki ba a Auren su yanzu bawai don baiso ba no sai don Abubuwan daketa faruwa da shi na farko rashin Ahmed nabiyu rigin gimun momy, 

Yakasa koda motsi yanzu shine keda cikin jikin Naziya? That means he is going to be a Dad? Allahu Akbar. Yayi sujud shukhur, batareda ya duba inda yake ba. Kafin ya tashi ya rungume likita “likita da gaske am going to be a dad? Ya juya wurin momy da gudu ya rungume ta “momy Zaki zama granny. Wasu irin hawayen farin ciki ne suka zubo musu su duka itada khaleel din, Aunty Zarah Tayi dariya tace ” congrats Son Allah ya inganta. Sakin momy yayi ya dawo tareda rike hannun Aunty Zarah “Sorry Aunty for all the trouble tank you for your prayers Amen Allah ya inganta min. 

“Oh mun shiga uku khaleel bako kunya cikin farko? Koda yake kalli Aunty ma jikan Fari harda hawayen murna lallai zamusha Kallo. Tafada cikeda tsokana, ” eh bakomai kifada duk Abinda zakice. 

Naziya kuwa reaction din su ya taba mata zuciya sosai har batasan lokacin da itama hawaye ya zubo mata ba, ita bata tabaji ko ganin dokin ciki irin nata ba ace har momy na kukan murna wannan ciki ai Alkhairi ne a gareta, Allah sarki Ahmed Ashe bashi bane uban ya’yan ta Allah mai yadda yaso. 

Matsowa yayi cikeda farin ciki yaganta tana hawaye. Da mugun sauri jikin shi na rawa ya karaso “Innalillahi baby ya Zaki fara kuka bayan kinada ciki please don’t hurt my baby stop it. Hannun shi akan marar ta yasha yanajin wani irin farin ciki, ya dago kanshi “baby cikina na nan please ki kulamin dashi kidaina yawo ki natsu basai kinyi komai ba ko wanka zanrika yimiki kinji no need ki wahalar min da yarinya. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button