AUREN GADO 1-END

AUREN GADO Page 41 to 50

Haka sukayita raha a tsakanin su, ta mike ta wuce kitchen domin shirya musu Abinci, momy tace ” karkiyi aikin wahala kibari mai aiki tayi. ” momy zan iya ai. Yana binta da Kallo tareda shafa kanshi yana tuna duk wani moment nashi da ita tareda hamdala. 

Saida ta wuce momy tace ” khaleel ka kai yarinyar nan gidan su ta gansu tunda tadawo bataje gida ba sai dai su da sukazo duba ni suka ganta. “Zamuje zuwa gobe nasa akawo mata motar ta ma yau zata iso. “Masha Allahu dama yakamata ace Matar ka batada motar kanta, nace cikin motocin Ahmed ka bawa malam daya mana me zakayi da tulin motocin nan daka Tara ka samu wasu kudi ka ware ma ka bada tallafi ga Almajiran da yake koyarwa nasan da Ahmed na nan zai yi hakan. Farin cikin canjin halin momy yakeji sosai yace ” momy duk karshen wata ina ware musu na Abinci, duk wani Almajirin Malam baya bara yanzu ana dafa musu Abinci ana basu suturu da Abubuwan rufa. “Toh Masha Allah Allah ya yi Albarka ya Kara budi ya sauki Naziya lafiya.

A ranar kuwa dalleliyar motar ta ta iso sabuwa dal ja mai duhu, tayi farin ciki sosai har momy saida ta lallaba ta fita tagani tareda tayata godiya, tace ” madallah saura kuma koyon tuki. “Momy ai na koya a can da mukaje bari kigani ta bude ta shiga suna kallon ta, sai murmushi yakeyi yana kallon yanda ta bayyana farin cikin ta a fili, bai taba yin Abinda yajishi ya faranta mai ba kamar y’an da yau yaga fara’ar ta a bayyane, ga Addu’a da take zabgamai da tafi komai dadi a wurin miji, ta tayar tareda d’an tukawa kadan ta kashe tafito tana mai rungume momy saboda farin ciki, yau itace da motar kanta, ” Aa sakeni kije ki rungume Wanda ya siya bani ba. Tafada cikin tsokanar ta, ” kyaleta momy ai tsegumi ne yasa ta tsallakeni ina ware hannu. ” to rasa kunya. Ta juya ta wuce cikin gidan ta tabasu wuri. 

Matsowa yayi ya riko hannun ta “let’s go ayimin godiyar a ciki not here yafada yana daga mata gira tareda cirata sama ba ruwan shi da idanun mai gadi, tako sagalo wuyan kayanta tsab, domin ta shirya biya da kudin da ba aganin su……. ????

“Toh a hankali dai munkusa kai karshen wanna labarim da ikon Allah don haka ina fatan Allah yabani Iko tareda juriya kukuma Allah ya Kara muku hakuri masoya yakaro kauna ya Kara budi ya warware wa kowa matsalolin rayuwar shi Allah masu Aure Allah ya karo d’an kon kauna, wainda basuda miji Allah yabasu nagari????. 

*Matar Soja*

6⃣5⃣ &6⃣6⃣

………….. Alhamdulillah Rayuwar tayi dai dai a wurin wainnan ma’aurata khaleel a kullum cigaba yake samu cikin Naziya ya girma sosai ta shiga wata na tara khaleel kullum cikin shopping din baby yake har online yaga sababbi sai yayi oder daki guda ya ware ya shirya kayan harda painting dakin anyi shi irin na dakin yara gadaje hudu different design itadai tace Abubuwan sunyi yawa momy tace ba ruwan ta tabarshi yayi idan taga wani Abu ma ita ke tunamai ya siya, tace “Momy toh ni ko kyalle bai siyamin ba sai baby. “Dole ne wannan kwantar da hankalin ki. Saidai momyn ta siya miki ina zaki kai kaya wasu ma fa ko kalarsu bazaki iya tunawa ba a cikin akwatin ki madam. “Kaifa akwai Wanda yakai ka tara tsumma ko bazaka saka ba,wainnan na Aure ne ka shirya zaka hada akwatunan haihuwa yaro. “Kai lallai zan hado set biyu kuwa harda na Amarya. Yafada ya gudu domin tsokana don yasan ta tsani kalmar Amaryar nan, “ba ason kayan tom. “Ke dalla har yau baki gano halin shi ba ya gane kina nuna kishin kine shiyasa yake tsokanar ki share shi Amarya sai dai yajira ta Aljannah. , momy kafa ta warke tsab zumunci tsakanin ta dasu inna Abun ba’acewa komai, yanzu ta Ajiye aiki tunda tayi jinya, don haka takan ware lokaci kawai domin fita ziyarar y’an uwan ta, ta dunke sosai da gidan kanin mijinta nata wato Alhaji Muhammadu, Rayuwa ta koya mata darasi mai zurfi harta haddace, da kanta idan taga mai bukatar taimako tana taimaka mai, har gidan su Fauziya taje tabawa iyayen ta hakuri sosai suka ce bakomai ai haka Allah ya tsara, Fauziya na nan na aikin ta tasamu wani Alhaji mai mata daya zasuyi Aure abinsu, don haka Rayuwar ta natafiya y’an da Allah ya tsara mata, ta hakura da Khaleel domin tasan baya ta ita, in akwai mace guda a rayuwar shi to itace Naziya, baya ganin wata mace a suffar mata sai Naziyan shi, 

Cikin gidan na koma tana zaune a tsakiyar falon ta, tayi kiba sosai ta bude ga kyau da shekinta na nan sai ma kar’i, da tayi, cikinta yayi katoto dashi kafafun ta sun kunbura, rigar less ce a jikinta fubu domin yanzu sune suturar ta, sukawai take iya jin dadin su, madara da milo ta kwaba wuri daya tana d’an gwala, 

Momy ce ta shigo dauke da plate din tuwo da miyar shuwaka, tana jin sallamar ta tafara kokarin boye d’an cup din madarar ta, “turus tayi tace ” fito da Abinda kike sha ingani. d’an tura baki tayi tace ” kai momy bafa komai bane madara ce. ” wato bazaki rufawa kanki Asiriba Naziya, anfada miki nauyin babyn nan ya wuce misali ki rage ciye ciyen nan bakyaji. matsowa tayi ta Ajiye tuwon tace ” mikon nan dama nasan tunda najiki shiru anan akwai Abinda kikeyi to nagano ki ai. 

Sallamar shi ne yasa momy tayi shiru tareda juyawa gefen shi ” jinan Ibrahim yarinyar nan zata koma gefe na harta haihu tunda bazaka daina bata Abinda na hanaka ba yazaka rika biye mata kalli y’an da take Kara kunbura kullum. 

“Wallahi ba ruwana momy ni ba Abinda nake bata impact nakwashe duk madarar dake gidan nan nima na hakurada shan shayin. ” ina ta samu wannan tom. Ta nuna mai wadda ke cikeda cup. Murmushi yayi mai kyau ya matso kusada ita ta dunguri kanta ” look baby karkija momy ta rabamu akan wannan Abubuwan da kike yi kinga yanda kika zama kuwa kinkusa biyuna fa, please ayi hakuri da madarar nan. Yafada kamar mai lallashin Y’ar yaye, ” wallahi inban shaba jinake kamar numfashi na zai fita don Allah kubari inrika shan kadan bada yawaba. Kallon momy yayi da fuskar tausayi ” momy ki taimaka mana kinji. 

Tsaki tayi ta tura mata kwanon tuwon “sakko ki mike kafafu kici Wanda zai wanke miki yaro da nono tunkafin ki haihu maza. Tana tura baki ta sakko kasa, 

Ta wuce kitchen din ta domin kawo mata ruwa, yayi saurin zama, ” baby lokacin tashi office baiyi ba fa nadawo. Dago sexy eyes dinta tayi bayan tasa lomar tuwon ta tace ” why? Duk da tasan me ya dawo dashi. “Oh don’t pretend like you don’t know, kwana nawa rabon da kibarni in huta, nakasa hakurine nadawo. Ganin momy yayi shiru, ” kai matsa mata taci abincin ta tunda kai baka lurada taci bataci ba. “Momy nima fa bawanda yadamu da damuwa ta me nadawo yi meke damuna ba Wanda yadamu nazama maraya tun yanzu, toh inta haihu ba mai komawa kaina ma gaba daya. “Ka shirya ma gida zataje wanka tunda ni kun raina ni nafadawa Kulu harma nafara yimata shiri tana haihuwa daga Asibiti sai gidansu sai tayi Arba’in zata dawo. 

Dariya yayi harda jingina a jikin kafadar Naziya kafin ya kalli momy da duk sun zuba mai ido suna kallon dariyar rainin wayan shi, “Amma dai momy wannan story ne kawai ba gaskiya bane? “Tatsuniya ce kaji, zaka gani in lokaci yayi. “Gwara ta zamo ta tsuniya kuwa don bazai yuwuba, ina ban Y’ar da ba wallahi, yaron nawa yazo duniya baza akawomin shi gidan ubanshi ba afaramin yawo dashi ina. Tuwon ta takeci tana kallon y’an da ya hakikance yana zuba rashin kunya akan d’an da baizo duniya ba. Saida taci dayawa momy ta kwashi kwanonin tafita ta kyalesu, yana ganin ta fita ya mike zunbur ya dagata sama daga ita har katon cikinta, yayi cikin dakin su na bacci. 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button