AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 1-10

     Aziza na tsaye a gefe da lullubi hawaye ne cike a idonta,ba dan komai ba illa su na zuwa wajan aka fara darewa ana matsawa babu wanda ya tsaya kusa da ita.

   Azima kuwa za ta zo yau ne gobe ne shuru, har aka gama tattaunawar da za ayi Azima bata zo ba.

     Bayan an fara watsewa Arɗo ya kira Baffa gefe ya ce

“Magaji? A gaskiya ba zan boye maka ba, ka binciki yaranka! Barin ma wannan yarinyar taka Azima,jiya an kawo min wani magana a kanta, bana son na tsawaita zargi dan babu kyau, sannan jikokinane kasan dai ba zan so abunda zai cutar dasu ba, amma ya kamata mu san abunyi,kasa ido sosai a kansu, bana so na kirawo Jumala dan duk abinda za a gaya mata ba yarda zatayi ba, sannan bayan sallar isha’i za a zauna ayi tattauna a faɗar mai unguwa, zamu je neman alfarma a yankin tudu” da sauri Baffa ya ce

“Arɗo yankin tudu kuma?”

“E Magaji, yankin tudu bamu da wani mafita wanda ya wuce hakan”

“To amma Arɗo kana ganin anya Sarkin Tudu zai sauraremu? Ko ka manta abunda ya shiga tsakanin yankinmu da nasu ne? Ɗansa yazo ya yi laifi a yankin nan an masa hukunci hakan ne ta haifar da gaba mai tsauri a tsakani, bana tunanin Sarkin yankin tudu zai yarda Iro Mai maganin macizai zai zo taimakonmu, kana gani duk wasu masu kama macizai da muke dasu a yankin nan sun mutu, a gaskiya inajin tsoron abunda zaije ya dawo, kar bamu gama da wani yaƙin ba mu sake kunna wani, a gaskiya bana so duk shawaran da za ayi ace za a bukaci taimakon yankin tudu da yankin ja’i” 

    Nauyayyiyar ajiyar zuciya Arɗo ya sauke ya ce

“To Magaji mai zai hana kai ka maida hannun agogo baya?”

“Bangane ba Arɗo?”

“Ina nufin ka dawo yadda kake a da dan mu taimaki yankinmu, Kayan aikinka da kaje ka binne kaje ka hakosu saboda……” girgiza kai Baffa ya hau yi yana ja da baya, ya ce

“A’a Arɗo na riga da nayi alkawari ba zan sake ba, har kwanan gobe ban manta da kuskuren da na aikata bisa tsautsayi a baya ba, abun shekara ashiri amma a yanzu gani nake yi yanzu abun ya faru, Arɗo ba a son raina na kashe *BANJU* ba, na kashesa ne sabida shafe mutanen yankin nan da ya fara, sannan idan baka manta ba yace zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan! tunda na kashe Banju nayi alkawari na dai na! duk wani abu wanda na gada daga gareka da kakanni! Dan Allah Arɗo a bar wannan maganar”

   ????????????????????

WLH IDAN NAYI POSTING A GRP BAN CIKA BI TA CIKIN GRP DIN BA,AKWAI WASU GRP DIN MA BANA BUDEWA INDAI BA GOGE SAKONNI ZANYI BA, IDAN KINA SON BIYAN KUDIN BOOK DIN NAN KI TUNTUBENI TA LAMBAR WAYATA TA SAMA, IDAN TA ACCT NE KO KATI.

AND PLS&PLS 4 ALLAH’S SAKE, IDAN KIN SAN BA BIYA ZAKIYI BA KARKI KIRANI KI GAYA MIN MAGANAR DA BA HAKA BA, A BOOK DIN NAN DAI BAN CE DARI BIYAR  KO DARI UKU BA,HAR TA DARI BIYU MA BANCE BA, DARI NE NACE DAN MASOYANA,BAN SAKA TA INDA BA ZAKI IYA BIYA BA, SO PLSS A DINGA FAHIMTA,DAN WATA MAGANA JIYA BAI MIN DADI BA SAM.????????

    

MASU KIRA NA DAN KARA MIN ƘWARIN GUIWA NA GODE,NA SAN ZAKU GANI DIK DA BAN SANKU BA AMMA KUNA RAINA????????????

COMMENTS AN SHARE

BY MOMYN AHLAN

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

*JINJINA GAREKI UWA BA DA MAMA, ANTY FAUZAH YAR AMANAR KAINUWA, SHUGABA DAYA TAMKAR DA DUBU,(GWAGGOTA TA KAINA ALLAH YA IYA MIKI.*

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

”'{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}”’

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

   ????????????????????

*JINJINA GAREKI HAJIYA MAMAN YUSUF MAI KAYAN MATA???? SAFIYAR YAU KECE KIKA FARA SAKANI DARIYA???? DAN HAKA GA KYAUTAR PAGE HAJIYA JIRGIN DANƘARO*????

*MAMIE’S CLUB HAKIKA SHARHINKU YA TAFI DA RUHINA, A KODAYAUSHE KUNA NUNA MIN E KU ƊIN YAN AMANA NE NA GASKEN-GASKE, AZIMA DA AZIZA FANS GRP, WLH KARKU YARDA A ZO GARINKU A FI KU RAWA AHA TO????, DAN ARADU YAN MAMIE’S SUN CE BA ZAKU KAMO SU A SHARHI BA,KUMA NA YABA????????, A KAFTA*????????♀️

*ALHAMDULILLAH! ALLAH NA GODE MAKA, YA ALLAH KA KARAWA SHUGABA JA GABA ANNABI MUHAMMADU SALLALLAHU ALAIHI WASALLAM DARAJA! DA IYALAN GIDANSA DA SAHABBANSA DA MAGOYA BAYA HAR IZUWA RANAR SAKAMAKO! HAKIKA AZIMA DA AZIZA YA YI FARIN JINI FIYE DA TUNANINA! ALHAMDULILLAH! MASOYA A CI GABA DA NUNA MIN ƘAUNA TA HANYAR SIYAN BOOK DIN NAN CIKIN FARASHI MAI RAHUSA, ƊARI KACAL*????????

FREE..*

????️==7️⃣↪️8️⃣

Shuru Arɗo ya yi yana kallon Baffa na wasu lokuta kafin ya ce

“Shike nan Magaji, ba zan takura maka ba, amma ban yi tsammanin zaka tsorata da maganar Banju haka ba”

“Ba tsorata nayi da maganar Banju ba a lokacin da ya faɗi, amma a halin yanzu ina cikin zullumi na maganar Banju, dan idan baka manta ba ya ce zamu gani ko ba jima ko ba daɗe sannan kuma zai dawo daukar fansa a kaina da mutanen yankin nan, abunda yake faruwa a halin yanzu abun a duba ne, sannan bamu san wani martani sarkin fulanin yankin jimo zai maidowa mutanen da suka je ban hakuri garesu ba, ba kowa bane zai lamunci hakan, munyi aiken neman taimako anzo dan a taimaka mana amma kuma sai a mai da musu da kaya ace an kashesa! Innalillahi wa inna ilayhirrajiun!” Baffa ya faɗa fuskarsa dauke da zallar damuwar da yake ciki, Arɗo yaja ajiyar zuciya ya ce

“Ko ma miye ne idan suka dawo ma ji, yanzu dai ka je amma ka tabbatar bayan sallan isha’i ka halacci fadar mai unguwa”

“In sha Allahu zan zo” daga haka suka yi sallama, Baffa ba hanyar gida ya yi ba dan ba gidan zai koma ba illa cewa da ya yi su Hajja da Aziza su koma gida, ina Azima bata zo ba? Aziza ta ce

“Eh Baffa bata zo ba” girgiza kai kawai ya yi ba tare da ya yi magana ba, Hajja da Aziza suka dauki hanyar komawa gida, su na tafiya su na hira, Hajja ta ce

“Ohh Allah ni Jumala, ko me ya hana Azima zuwa? Ita kullum ta fi so ku ta zama a bakin zargi”

“Ai ko basu zauna a bakin zargi ba, ba lallai bane yaranki su kasance mutane ne!” da sauri Hajja da Aziza suka juya su na kallon Mairo da Hadi wanda suka riƙe ƙugu sai kace zasu dake su, Hajja ta ce

“Mairo me kike nufi?”

“Oho miki kuma! Kin fi kowa sanin abunda nake nufi, yara ko ma dai nace iyayen yara! Ace kamar su Azima da Aziza a wannan yankin gote-gote dasu amma babu aure! Sannan suna tafiya jiki na lankwasa! Daga mai idon mage (wato Aziza kenan) sai mai ido ruwan ganye(Azima kenan) taya kuwa zasu zama mutane, ga shegen kyau! Duk da lokacin da muka yi yan matanci dake duk yankin nan babu mai kyawunki sannan babu jarumi sama da Magaji, ba wai hakan yana nufin zaku haifi yara masu kama da mutanen wani duniya daban bane ehe! Ko ki so ko karki so Azima da Aziza dai ba mutane bane!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button