AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 31-40

 

*PAID.*????️==3️⃣1️⃣↪️3️⃣2️⃣

Sarki Chubaɗo cikin fushi ya kalli mutanen da suke wajan ya ce.

“Amma wallahi kun bani mamaki! Kuma kunji kunya! Yanzu akwai masifar da zata samu Magaji wanda har zai sa ku juya masa baya? Idan har ku wa inda ku ka zo bayan shekara ashirin baku san gwagwarmayen da Magaji ya yi ba, to ku wa inda ku ka zo kafin bayan shekara ashirin zaku ce kun manta da wannan halaccin ne? Dayawanku a nan wasunku basu da dangi kaff Banju ya kashesu!

dabadin Magaji ba babu ko da ƙwaro da zai rage a wannan yankin!!” Sarki Chubado ya karasa da tsawa idonsa jajur dan ransa ya b’aci matuka”A ce ina sarkin fulanin yankin kwana amma Jauro ya ja ku ba tare da sanina ba ku zo yiwa Magaji rashin mutunci da dibar albarka! Jauro ne sarkinku!! Na ce Jauroo neee sarkinkuuu!!!?” shuru jama’a suka yi masu zare ido da masu tsilli-tsilli da ido suna yi, Mai Unguwar yankin kwana bayan Sarkin fulanin kwana Chubaɗo ya dasa ayar tasa shima ya karbe da cewa

“Jauro dai mai maganin yankin kwana ne kamar yadda ku ka sani, amma a da kun san waye GARKUWAN YANKIN KWANA KAFIN A ƊORA GARKUWA NA YANZU!! TO GA SHI NAN SHINE DAI! *MAGAJI BAWA!!* kafin ya sauke duk wata baiwa tasa ya binne bayan yasha wahalan kama aljanu da mayu ya kullesu!! Ya sauka ne a kan matsayinsa da yake da shi bayan ya kashe Banju! Amma har kwanan gobe! kai ba ma kwanan gobe kawai ba! HAR GABAN ABADA BABU WANI GARKUWAN FULANIN YANKIN KWANA SAMA DA MAGAJI! SANNAN BABU WANI MAI MAGANI SAMA DA MAGAJI! Har ta Garkuwan fulanin yankin kwana na yanzu da Magaji yake tunkaho”

    Garkuwan fulanin kwana na yanzu ya fito ya ce

“Tabbas hakane, da taimakon Magaji Bawa na zama Garkuwan fulanin kwana shi ya maidani mutum, gaskiya baku kyauta ba” wasu ne jikinsu ya fara sanyi ganin haka yasa Jauro ƙara tattaro sauran munafurcinsa dan shi baya so ace mutane su banzartar da maganarsa idan ba haka ba ba zai cika burinsa ba,baya so yaji sunan Magaji na daukaka! yafi so duk yankuna yadda ake kiran sunan Magaji Bawa! Magaji Bawa! ya kasance shi Jauro Mai Maganin yankin kwana shi ake kira ba wani Magaji Bawa ba, ace shine shahararsa ta kai inda yake so kuma yake bukata, saurin cewa ya yi

“Babu wani borin kunyar da za ayiwa mutane an dai cutar dasu! Wa inda aka kashe musu yara su ce mai? Sannan tunda daɗewa Magaji yasan yaransa Macizai ne amma ya boyewa mutane bai gaya musu dan yanzu yana da mugun nufi a ransa!”

 

       “Magaji baya da masaniya a kan cewa *AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE* taya idan ya sani har zai barsu su yi kisan kai!? Da kake maganar su na kisa Aziza bata taba kisa ba,akasari ma ita dabi’un Magaji ne tattare da ita, ku a tsammaninku da Azima ce har kwa fara yi mata abunda ku ka yiwa Aziza? Inaaa! Da kafin mu iso wlh sai dai gawawwakinku!” cewar Baffa Mandi, jauro ya ce

“Owoohh! Kenan da saninku ma kamar yadda na faɗa! Jama’a kuna dai ji ko? An zalinceku an munafurceku an kashe muku! Kuma ta yadda zaku gane Magaji ya san yaransa Macizai ne shine basu zuwa bikin gargajiya ta al’adun fulani wanda ake gabatarwa duk shekara, sabida sun san a lokacin ana amfanin da magungunan macizai! Sannan……”

       “Ya isheka haka Jauro!!” Baffa ya katse Jauro jikinsa na rawa, ya tako ya zo gabansa ya ce

“Da ace da sanina yarana macizai ne da tuni na dauki mataki wani zancan 7ake yi yanzu ba wannan ba, a da nace maka muddun ka gano yarana macizai ne nina maka lamuni ka kashesu! Amma tunda na gano cewa ku ɗin ba mutane bane dabbobi ne wanda shanu ma sun fiku hankali ko da Azima da Aziza sun dawo yankin kwana duk wanda ya yi gigin taba min yara a lokacin zan basu umarni su kashe min koma waye!! Sannan ka zuba ido ka gani, zan maida yarana mutane ko da kuwa hakan zaiyi sanadiyar mutuwata, a yau kuna zaginsu macizai kuna ci min mutunci, amma ku sani ko nace kai jauro ko sani, MAGAJI BAWA KAFIN ALLAH NE BA KAFIN MUTUM BA! KO DA ACE MISALI BANA RAYE! AZIMA DA AZIZA SAI SUNANSU YA BUGA TAMBARI A YANKUNA BA MA IYAKAR YANKIN KWANA BA! KAMAR YADDA NA MAHAIFINSU NI MAGAJI BAWA NAYI! NA MAKA WANNAN ALKAWARI! BAIWA DA FARIN JININMU DAGA ALLAH NE KA ZUBA IDO KA GANI JAURO!!!” Baffa na gama faɗi ya bar wajan tare da daukar Hajja suka yi gida yana tunanin tashin hankalin da Hajja zata farka da shi, da fari yara macizai yanzu kuma babu su ma kwata-kwata, amma ya zata yi dole su rungumi kaddara.

         Bayan Baffa ya bar wajan Sarki Chubaɗo ya kalli Jauro ya ce

“Ka dai ji kunya wlh! Da ace nima tsoron kar nayi abun kunya ba wlh da yau a yanzu na koreka daga yankin kwana, ku kuma idan dai Jauro ne gaku ga shi,in dai ba a mutu ba to ba shakka ba a daina kallo ba, ba fata nake muku ba amma na tabbata akwai jarabawa,sannan Allah ba azzalumin bawansa bane, duk wani abunda ya sameku karku sake kuce zakuje wajan Magaji ya taimaka muku! kuje wajan Jauro ya taimaka muku, wannan umarnina ne a matsayina na sarkin wannan yankin!! Idan kuma na ga akasin abunda nace mutum zai fuskanci mugun hukunci!” Chubaɗo na gama faɗi ya yi gaba ya bar su a tsaye a wajan, wasu jikinsu yayi sanyi inda nadama ta kamasu wasu kuwa zuciyarsu kamar busashshen itace!.

      ????????????????????????

Azima kwananta biyu tana tafiya kafin ta fito bakin titi, tana fitowa wani guɗa ta yi da dogon harshenta, duniya sabuwa! Tana nan tsaye a kan titi da lullubi tana tunanin hanyar da zata fara dosa, nan ta yanke shawara kawai ta bi dogon titi ta ga iyakar karewarsa, haka ta hau tafiya a tsakiyar titi tana murmushi, kamar daga sama sai ga wani mota ta yanko da gudu amma sai ganin yarinya ya yi tana tafiya akan titi sai horn yake danna mata amma a banza! Azima kuwa tunda farkon fitowarta kenan ba fahimta tayi ba, da kyar mutumin ya taka burki ya fito a motar gami da daka mata tsawa “keeeeeeee!!” wani tsayuwa Azima tayi tare da ware blue eye dinta, babu wanda ya taba mata irin wannan ihun, a hankali ta kara jan mayafinta ta rufe fuska sannan ta juya a hankali kanta a duke, mutumin kallon sama da kasa ya mata yana yatsine fuska dan ya ganta da shigar fulani ba mamaki irin kidahuman nan ne na jeji dan haka cikin izgilanci ya hau ta da zagi.

“Ke wace iriyar bagidajiya ce da ana miki horn amma da shike kin fito a cikin jeji baki ganewa kwakwalwarki a toshe yake kina tafiya a kan titi banza ballagaza daƙiƙiya ƙidahuma tunkiya!!” hakika zagin ya soki zuciyar Azima, zaro ido ta yi tare da yaye mayafinta rai b’ace cikin hausar da babu sosai a kan harshenta ta ce

“Ba dai tunkiya ba, sai dai *MACIJIYA!????**” ta faɗi tare da komawa macijiya ba ta jira ya gama firgita ba ta kai masa sara a wuya nan ya fadi kasa yana shure-shure,komawa mutum ta yi tana dariya ta ce

“Kaina mutum na farko da na fara kashewa daga fitowata,hakan na nufin cewa zan sha jini da yawa kenan sabida mutanen cikin gari basu da ɗa’a,ni kuwa AZIMA MACIJIYA bana daukar wargi!” ta faɗi tana murmushin gefen baki ta leƙa cikin motar ta wargaza ta ga kuɗi ta kwashe duk da bata san amfanin me zasu mata ba, ta ci gaba da tafiya, ta yi tafiya sosai inda ta iske tasha wanda yake cike yake da jama’a a hankali ta ƙutsa kanta cikinsu tana ji ana ambatar sunayen garurruka, garin da taji ya mata masauki a kunneta shine *KANO TUMBIN GIWA KO DA MAI KA ZO AN FIKA!* murmushi ta yi ta kara nanata KANO  ranta, sannan ta afka mota ta nemi can baya ta zauna tana murmushi yau burinta ya cika ta bar yankin kwana.

1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button