AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 1-10

Idon Hajja ne ya kawo ruwa ta ma kasa magana, da kyar ta ce

“Mairo idan ke kike aurar wa sai ki zo ki aurar dasu, sannan kuma idan kina canza halitta ki zo ki canza musu” caraf Hadi ta cab’e zancan da cewa

“Wa ye bai sani ba, ba mamaki duk wannan kisan da ake yi a yankin nan Azima da Aziza suke yi, kuma da saninki ke kike daure musu…..”

“YAAAA ISAAAAAAAA!!!” Aziza ta faɗa da kakkausar murya, ganin yadda fuskar Mahaifiyarta ya jiƙu da ruwan hawaye, gaban mahaifiyarta ta tsaya yayinda idonta suka kara rinewa zuwa fari-fari ,yatsarta manuniya ta ɗaga tana nuna Mairo da Hadi cikin gargaɗi ta ce

“Zan iya jure komai! Zan iya shanye komai! Amma kar na ga hawaye a idon MAHAIFIYATA SANYIN IDANIYATA! ku fita tsabgarmu! Mu mutane ne, maganar da kika fada yanzu kuma Inna Hadi ki bar shi a iya nan kawai kar yaje gaba!” Aziza na gama fadi ta kamo hannun Hajja suka bar su Mairo da Hadi jiki na rawa, Hadi ta ce

“Mai….Mai…Mairoo….ban….gaya…miki….da…da..da cewa ba mutane…bane…wollah inaji ko rantsuwa nayi ba zan yi kaffara ba…kalli ki ga lokaci daya yadda idonta ya canza…anya ma ni kuwa ba su bane…..” saurin dakatar da ita Mairo ta yi ta ce

“Hadi ki bar maganar nan a nan dan ban shiryawa mutuwa ba, zo mu tafi” Mairo ta fizgi hannun Hadi.

      @@@@@@

Sun ɗan yi tafiya Hajja ta tsaya, Aziza tasa hannu tana sharewa Hajja hawaye tare da fadin

“Kiyi hakuri Hajja, dan kuka mai ja wa uwa jifa ko Hajja!?” Aziza ta faɗa tana fashewa da kuka, Hajja ta ce

“A’a Aziza, har ga Allah ni har zuciyata ban taba zargin yarana ba, na san ni dai mutane na haifa”

“To me yasa kike kuka Hajja?”

   “Saboda dukkan uwa ta gari ba zata so a dinga sokin yaranta ba! Har raina nake jin zafi” Hajja ta fada tana mai kamo hannun Aziza, wani tausayin mahaifiyarsu ne ya ɗarsu a zuciyar Aziza, duk yadda take tausayawa kanta da yar uwarta tafi tausayin Hajja, ranar da zata gane cewa su din ba mutane bane MACIZAI NE ranar da zata san duk kisan da ake yi Azima ke yi, shin ya dace ta ci gaba da boyewa Hajja cewa su ba mutane bane? Ko dai ta fito ta gayawa Hajja da Baffa gaskiya? Kai amma kuwa gunduwa-gunduwa za ayi dasu, sannan Azima ta ce ko da ta faɗi ba shi zai hanata cika burinta ba! Girgiza kai Aziza ta yi ta sake rungume Hajja tana kuka, Hajja zata yi magana suka ji nishi na tashi ta gefensu wanda yake ciyawa ne kore shar a wajan, saurin maida hankalinsu suka yi, Aziza ta ce

“Hajja kamar fa nishi nake ji?”

“E nima naji Aziza, kamar ta nan yake fitowa zo mu duba mu gani” suka yanki gefen ciyawar, wani yaro suka gani kwance fuskarsa ta koma blue bakinsa sai fitar da farin kumfa yake yi tare da jini, salati Hajja ta saka, da sauri Aziza ta dagosa tana kallonsa tare da jinjigasa, gefen wuyarsa ta kalla ta ga saran maciji, wanda bata raba dayan biyun *AZIMA* ce, girgiza kai ta hau yi cikin tashin hankali, ta buɗe baki, Hajja ta ce

“Aziza me ya faru da shi?”

“Hajja maciji ne ya saresa, bari na gwada yi masa magani” kasancewar lokuta da dama Aziza na gwada wa Hajja kamar tana magani wanda Hajja ke danganta hakan da nasaban Baffa, bata jira Hajja ta yi magana ba ta hura iska a bakinta ta rufe ido gam na wasu daqiqu sannan ta buɗe, yayinda idon ya koma fari sol, hannu tasa a bakinta ta dibo farin yawu ta gogawa yaron a wuyarsa dai-dai shatin saran, sannan ta koma kallonsa, duk fuskarsa ta yi blue, tana saka masa ya hau gurnani yana murkususu sannan ya koma ya yi ɗifff! Hajja ce ta daga hannunsa ta ga ya koma, da sauri ta janye Aziza ta ce

“Aziza zo mu bar nan wajan”

   Kallon Hajja Aziza ta yi cikin damuwa ta ce

“Hajja taya zamu barsa bayan yana buqatar taimako,ki bari na taimaka masa Hajja kar ya mutu”

“Ai ya riga da ya mutu Aziza! Ki zo muje kar ace kece kika masa wani abun” 

Suman tsaye Aziza tayi tun sadda Hajja tace ai ya riga da ya mutu, kallon yaron kawai take yi, hannu Hajja tasa ta ja Aziza da sauri suka bar wajan basu tsaya ko ina ba sai gida, suna shiga gida Aziza ta shige bukkansu bata ga Azima ba, duk yadda akayi tana rafin jimulo, hannu tasa ta goge hawayenta tare da daukar mayafinta, Hajja ta juyo zata bata ruwa ta ga ta fice a gidan da sauri Hajja ta bi bayanta tana fadin

“Aziza! Ke Aziza!? Azi…” Hajja bata karasa ba sakamakon dakatar da ita da Aziza ta yi, ta rufe mata ido ta hura mata iska, haka kawai Hajja ta tsinci kanta da komawa gida, Aziza kuma hanya ta yanka ta yi rafin jimulo, a yadda take tafiya zaka gane cewa ba mutum ba ce, haqiqa yau Azima ta kai ta karshe! Me wannan karamin yaron ya mata da zata kashesa!.

Tana isa rafin ta kwala kiran sunan Azima.

“AZIMAAAAA!” sulalowa Azima ta yi hannunta dauke da mangoro fuskarta wasai, ganin fuskar Aziza ya sakata sakin baki dan bata taba ganin fuskarta a haka ba

“MACIJIYA AZIZA LAFIYA!” Azima ta fada cikin halin ko in kula.

“AZIMA ME YARON DA KIKA KASHE YA MIKI!?” 

kyalkyalewa da dariya ta yi ta ce

“Sabida ya cancanci ya mutun ne, saboda ya ganoni, kuma yace sai ya faɗa kin ga kuwa dole na kashe sa tunda….” dauketa da mari Aziza ta yi, tana dagowa ta sake kai mata wani marin, ran Azima ya tunbatsa nan ta riƙiɗe ta koma macijiya,in da ita ma Aziza yau ta rikiɗe ta zama macijiya fara sol, nan dambe ya kaceme.

    ????????????????

WAI YAU MACIZAI NA FAƊA,NAYI NAN????????♀️????????♀️????????♀️

A lallaba chaji wala????????♀️????????♀️????????♀️

COMMENTS AN SHARE

*FREE..*

????️==9️⃣↪️????

Dambe suke yi sosai a tsakaninsu ba ji ba gani, yayinda Azima ta yanki Aziza a gefen wuya,nan ta koma mutun ta faɗi kasa, ita ma Azimar rabi mutum rabi Macijiya ta zama tana kallon Aziza ranta a haɗe idonta ya kara rinewa zuwa blue, a hankali Aziza ta miƙe tsaye tasa hannu ta karkaɗe jikinta ta juya baya,ta sa hannu a gefen wuyanta inda yake zubar da jini ta lumshe ido, kamar ƙiftawar ido da bismillah ta shafe wajan, sannan ta daga hannunta sama ta haɗa wani guguwa mai karfin gaske ta turawa Azima, Azima bata ankara ba taji anyi sama-sama da ita, sai da taje can sama kafin ta faɗo timm! Da kasa nan ta koma mutum, a hankali Aziza ta juyo tana kallonta yau fuskarta babu fara’a, haqiqa dan faɗa su na faɗa amma basu taba dambe ba, bar su a cacan baki.

    Saurin tashi Azima ta yi ta sake komawa macijiya ta yi hajijiya ta tada ƙura ta yi kan Aziza, da sauri Aziza ita ma ta sake zama macijiya suka haɗe aka hau dambe, da jelarta na maciji ta nannaɗe wuyar Azima ta shaƙeta sosai, murkususu Azima ta hau yi tana son kwacewa daga hannun Aziza amma ta kasa, inda karfinta ya fara karewa dan duk muguntarta bata kai Aziza karfin dafi ba.

    Nan numfashinta ya fara yin sama inda a karshen jikinta ya sub’ale ta koma mutum sumammiya, ganin haka yasa Aziza sakinta ta wullata kusa da rafin ita ma ta koma mutum sannan tasa hannu ta dibo ruwa ta watsa mata a fuska, wani wawan ajiyar zuciya Azima ta sauke alaman ta sha wuya, da tari ta farka tana yunkurin tashi ta ce

“Duk abun da zakiyi Aziza kema kin sani ba zaki iya kasheni ba!”

   

    

   Kafadarta Aziza ta kama hawaye cike a idonta ta ce

“Nima bana fatar kasheki! Har na bar duniya bana fata na kashe ko da tururuwa! Azima kisan ya yi yawa! Azima me kikeson zama ne! Ga shi yau kin sani na aikata abunda bana son aikatawa wanda ban ma taba aikatawa ba! meyasa Azima! Me yasa! Me yasa!” Aziza ta karasa tana sakin kuka mai cike da ruɗani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button