AZIZA DA AZIMA 21-30

Aziza bata tsaya ba wa Hajja amsa ba illa randar kasa da ta nufa ta dibo ruwa mai sanyi ta watsawa Baffa nan ya sauke ajiyar zuciya yana ji kamar numfashinsa zai dauke, ruwan Aziza ta ba shi da kyar ya karba ya sha sannan ya dafe kansa, sannu suke jera masa ba tsayawa, sai zuwa can Hajja ta ce
“Wai ni kam Aziza kamar dazu na ga shigarki bukka,amma tayaya kika fita a gidan ban gani ba? Ko b’acewa kika yi?” Hajja ta tambayi Aziza ne kawai amma ga mamakinta sai ji ta yi Aziza ta ce “e Hajja b’acewa nayi, sabida bazan iya bi ta bakin kofa ba, Baffa ya zuba furen surfa!” zaro ido Hajja tayi bama Hajja ba harta Baffa da bai gama dawowa dai-dai ba ya ɗaga kai yana kallon Aziza wacce ta miƙe tsaye tana ja da baya tana girgiza kai tare da hawaye mai ban tausayi tana fadin
“Gwanda ayita ta kare, yau zaku san wani irin yara ku ka haifa, Hajja Baffa kuyi hakuri hakika baku haifi mutane ba, Baffa na san da hannunka zaka kashemu bayan kasan mu ɗin su waye! Na san ka gama gane Azima nice kawai baka gane ba,bazan iya munafurtanka ba Baffa!” da sauri Hajja ta miƙe tana fadin
“Me kika faɗi ne haka Aziza!”
“KARKI MATSO INDA NAKE!!” Aziza ta fada da karfi, Hajja ta ce
“Sabida me Aziza? Nifa mahaifiyarki ce!” tana fada tana kara tunkaro Aziza dake matsawa baya, rintse ido Aziza ta yi ta buɗe ta haɗe rai cikin daga murya ta ce
” *SABIDA NI MACIJIYA CE! AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE!*” Aziza ta faɗi tare da komawa Macijiya! Wani mahaukacin kara Hajja ta saka tare da yin baya-baya ta faɗi timmm! A kasa, ganin haka yasa Aziza komawa mutum ta yi kan Hajja tana jijjigata tare da ambatar sunanta,amma ina Hajja bata motsi numfashi ya tsaya cak, cikin kuka Aziza ta ce
“Hajja ba dai hadiye zuciya kikayi ba!? Na shiga ukuna Baffa!!” Aziza ta fada tare da juyowa wajan Baffa nan ta ga ashe shima ya suma! Randar ruwan kasar gabadaya Aziza ta dauka ta juye a kan iyayenta, da kyar suka saki ajiyar zuciya, suna dawowa Aziza ta ce
“Baffa waye su *BANJU DA BAHULA!!!?*” wani zabura Baffa ya yi yana kallon Aziza, da sauri ya miƙe tsaye ya ce
“Dole kafin nasan abunda ke yawo a jikinku saina haƙo abunda bana son haƙowa, Aziza na fahimci ke ba kamar Azima ba ce, da ace ke kamar Azima ce yadda muka suma da kin kashemu! Na sha zargin Azima na son kasheni amma naki ba wa shaidan damar da zai saka min waswasi a zuciyata a kan ‘yar da na haifa ta cikina! Dan haka zan gaya miki waye Banju da Bahula da abunda ya shiga tsakanina dasu, amma kafin nan zo muje jejin firi”
Saurin riƙe hannun Aziza Hajja tayi idonta jajur ta ce
“Ya isa haka Baffan yan biyu! Ka sha saka rayuwarka a hatsari ga shi yanzu ta shafi yarana!” Hajja ta fashe da wani matsinacin kuka tana zuba guiwowinta a kasa, da sauri Aziza ta kama hannunta, ko kaɗan Hajja bata ji tsoron Aziza ba, cikin kuka ta ce
“Macizai! Macizai! Macizai! Ni Jamila na haifi Macizai! Inaaa ba zai yu ba ni kawai a dawo min da yarana!” Hajja ta kuma sa kuka bai tab’a zuciyar mai sauraro, rungumeta Aziza ta yi cikin tausayawa domin kuwa Hajja abun tausayi ce ita da Baffa, fita Baffa ya yi yaje ya kirawo Arɗo da Yawuro, da Inna Wuro, da kuma tsohon sarkin kwana wato Baffa Mandi, bai boye musu komai ba ya gaya musu komai, hakika hantar cikinsu ya kaɗa fiye da tsammani, Arɗo ya ce
“Lallai kuwa idan har Banju ne ya dawo daukar Fansa! Kisa bai ma yi komai ba kenan! Ashe kuwa idan ba a dakatar da Banju ba idan har shine sunanmu toka” Baffa ya ce
“Bazan bari hakan ta faru ba, yanzu daga nan jejin firi zamuje nida Aziza, zanje na haƙo kayana dan nasan taya zan taimaki yankina da kuma yarana” Baffa Mandi ya ce
“Magaji!? Hakowa fa kace? Aljanu da mayu ayi yaya dasu?” Arɗo yace
“Buhun bala’in Banju gwanda haƙo aljanu da mayun da Magaji ya kulle, dan ba karamin babban shaidani bane Banju! Ko ka manta b’arnan da Banju ya yi kafin Magaji ya kashesa?”
“Taya kuwa zan manta Arɗo? Bayan dukka ahalina Banju ne ya kashesu!”
Baffa wanda ke goge gumi ya ce
“Aziza tana tare dani, dan haka yanzu a gayawa su sarki Chubaɗo halin da ake ciki, sannan a cewa yara da manya kar wanda ya fito ko da kofar gida ne, domin kasan aljanun da aka ɗaure duk wanda ya samu damar guduwa zai fito ne da haushi da b’acin rai na dauresa da akayi na tsawon shekaru, dan haka duk wa inda suka samu zasu bugesu ne, Yawuro, Inna Wuro ku kula da Jumala, Aziza muje” Aziza ta amsa da to Baffa a sanyaye abun tausayi, zasu fita Hajja ta kuma sa kuka tana salati dan ita kadai tasan abunda yake damunta, su Yawuro da Inna Wuro suna dannarta, yayinda Arɗo yace bari yaje wajan Chubaɗo su zanta a kan lamarin.
????????????????
B’acewar Azima jejin hayi ta nufa tana kan ihu fatar jikinta na mata zafi sosai,zubewa tayi a kasa tare da furta “KARYANKA! NACE KAYI KARYA MAGAJI! FANSA NE DAI SAI NA DAUKA! AMMA NA RASA MEYASA KAKE GALABA A KAINA TUN TSAWON SHEKARA ASHRIN! YANZU MA SO KAKEYI KA SAKE KASHENI! INA HAKAN BA ZAI YU BA, DOLE NA MAKA MUGUN TABO! TA HANYAR CI GABA DA RAYUWA A GANGAR JIKIN ‘YARKA AZIMAAA!!”
Wannan murya na gama fitowa ta b’alli gashin kanta tasa a baki nan taji sauƙin raɗaɗin, sannan ba tare da bata lokaci ko dogon tunani ba Azima ta dauki hanyar barin Al’karyan yankin kwana dan ta shiga cikin gari ta cika burinta na tarwatsa jama’a da hanasu kwanciyar hankali.
????????????????
Baffa da Aziza suna isa jejin firi ba bata lokaci Baffa ya fara haƙo abunda ya binne, yana gaff da gama cirowa ya kalli Aziza ya ce
“Kin shirya?” Aziza ta gya ɗa kai gami da cewa “e Baffa a shirya nake”
“Fara” Baffa ya faɗa,yayinda Aziza ta daga hannu sama ta fara haɗa wani baƙin guguwa mai cike da rami dan tare mayu da aljanu ya kasance ko da zasu gudu kaɗan ne, da karfi Baffa ya fizgi wani abu kamar irin akwatin karfe na tun tsawon wasu shekaru, yana fizgowa take wani mahaukacin guɗa ya tashi, wanda ba iyakar jejin firi ba dukkan jeji sai da ya amsa tare da dukkan mutanen yankin kwana babu wanda bai ji wannan gudar ba, Aziza na tsaye sai haɗa zufa takeyi yayinda take riƙe da wannan baƙin guguwar wanda ta riƙe aljanu da mayu, ganin halin da take ciki da sauri Baffa ya buɗe akwatin wanda da ka gani kasan ya daɗe ya dauki guru da layarsa ya maida (Allahu Akbar Baffa an tuno baya) duk wani abu da Baffa ke amfani da shi sai da ya dauka,na ɗaurawa ya ɗaura na sakawa ya saka, na mannawa ya manna, ya fiddo wani tulu mai murfi, yana fiddowa ya sake kama wasu aljanu da mayun ya rufe yayinda wasu suka gudu, Aziza na sakewa ta zube sumammiya, Baffa bai damu da sumar da tayi ba dan na hucin gadi ne, ta ma yi namajin kokari, dan ko shi iyakar abunda zaiyi kenan,kuma dabadin ita ba da yana haƙo abun nan ba tare da an rikesu ba bala’in da zata kunno yankin kwana sai Allah.
Baffa na ciro kayansa ya haɗa wasu taurari guda biyu wanda suke kamar dutse mulmulen laka, sunan Azima da Aziza ya rubuta a kai, nan wani haske ya bayyana, na Azima ya fara gani, nan ya hangi Banju a gangar jikinta, Azima a sume take, wasu hawaye masu zafi ne suka wanke wa Baffa fuska, sannan ya duba taurarin jikin Aziza, nan ya ga Bahula ce ke rayuwa a jikinta, sannan ita an maidata Macijiya ba wani ke rayuwa a jikinta kamar Azima ba, cikin ruɗu da tashin hankali Baffa ya watsawa Aziza wani farin kasa nan take ta sauke ajiyar zuciya ta farka, ya ce