AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 21-30

“Aziza muje gida” girgiza kai Aziza ta yi ta ce

“Baffa ba zan je gida ba har sai ka gaya min waye Banju da Bahula” Baffa ya ce

“Yanzu kuwa zan gaya miki Aziza, yau zan baki labari”

      ????????????????????

*Tabb cakwakiya! Shin ya zata kaya ne? Idan Baffa ya ba wa Aziza labari taya za a rabasu da wannan bala’in? Ga shi Azima ta bar yankin kwana ta do shi hanyar shiga gari,Dukkan wasu manya tambayoyi yana sauran shafuka da suka rage a gaba, naira darinki ya isheki! Idan kuma kika jira cmplt dari uku.

Karku bari ayi babu ku.*

  COMMENTS AND SHARE

BY MOMYN AHLAN

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   ????????????????????

GODIYA TA MUSAMMAN GA DAUKACIN YAN PAID GRP DIN AZIMA DA AZIZA MACIZAI NE, HAKIKA SHARHINKU YANA KARA MIN ƘARSASHI, KAUNA CE TASA KUKA KASANCE A PAID GRP DINA, DAN HAKA NIMA INA KAUNARKU????, KU MORE KUJI DADINKU.

*PAID.*

????️==2️⃣5️⃣↪️2️⃣6️⃣

Gyara zama Aziza ta yi ta naɗe kafarta sannan ta ce

“Ina sauraronka Baffana!” miƙewa tsaye Baffa ya yi ya juya baya gami da maida hannunwansa baya ya yi tsayuwar da jaruman maza ke yi wanda suka yarda da kansu ya koma ainahin asalin MAGAJI BAWANSA sannan ya ce

“Aziza! a da an yi wani mutum jarumi! sadauki! jajircacce! tsayayye! marar tsoro da fargaba!, da tare dukkan wani faɗa! kin san ana cewa ba a faɗa da aljani ko? to wannan mutumin yana yi! wanda a yanzu shike tsaye a gabanki! Wanda wannan mutumin mahaifi ne gareki da kuma ‘yar uwarki Azima, kamar yadda kika sani Ardo mahaifina ne wato kakanku! Inna wuro mahaifiyata ce! wasu daga mutanen yankuna suna fadin cewa nayo gadon Arɗo a lokacin yana saurayi, amma kin san me Arɗo ya ce?” Aziza da ta ƙurawa Baffanta ido tana yi masa kallo kamar bata taba ganinsa ba dan gani ta yi gabadaya ya canza mata ya tashi daga Baffanta da ta sani ya koma wani mutum daban ta girgiza kai alamun a’a, Baffa ya ɗora da cewa

“Arɗo cewa ya yi ni daya ne tak a wannan yankin dama sauran yankuna babu na biyuna! domin kuwa baiwata daga Allah ne, tun ina yaro nake mu’alama da aljanu sannan nake taimako! a taimakon da nakeyi ba iyakar mutane ba har ma da aljanun,a lokacin na shiga yankuna da dama dan kai wa wasu dauki! Yankin kwana ta shahara ta yi suna ta sanadina, tun a lokacin nake cin karo da abokan gaba da maƙiya wa inda basu sona sabida farin jinin da nayi a wajan yan mata a lokacin babu wani kyakkyawan jarumi ka ma na, shiyasa na kara yin baƙin jini, mahaifiyarku kamar yadda ku ka sani ‘ya ce ga Ƙanwar Arɗo wanda suke uwa daya uba daya, Jumala yarinya ce mai kunya da natsuwa da hankali da sanin ya kamata, tun ranar da naje gidan Inna Kab’o na ganta naji na kamu da sonta amma ban san taya zan bayyana mata ba, Jumala ta ta so ne a babban gida wanda suke da tarin iyalai masu yawa, wanda a yanzu Jumala ita daya ce tal ta rage a danginta duk Banju ya kashesu!”

     Kasa hakuri Aziza ta yi ta ce

“Baffa miye dalilin Banju na kashe mutane? Sannan naji Baffa Mandi ma ya ce shi ya kashe   masa ahalinsa! Sannan wanene shi Bahula din?”

“Bahula mace ce ba namiji bane Aziza! Saurin me kikayi Aziza? Zaki san komai a yau! duk wani jeji babu wanda bana shigansa da ikon Allah sannan na fito lafiya ba tare da wani abu ya sameni ba, domin nayi imani da Allah da ANNABI MANZON ALLAH S,A,W, nayi karatuna a wajan wani Babban malami a nan yankin kwana mai suna MALAM SHAINI wanda shima ahalin yanzu baya raye Banju ya kashesa! shi da iyalansa!”

      “Kenan Baffa yawancin mutane Banju ya kashesu?”

     Juyowa Baffa ya yi ya kalli Aziza sannan ya yi wani murmushi ya ce

“Kisan da Banju ya yi ba zai kirgu ba, dan zan iya ce miki a cikin kashi dari na mutanen yankin kwana Banju ya kashe kashi arba’in! Banju mugu ne, na kasance ina shiga jeji dan nemo ganyayyaki na haɗa magani, akwai wani jeji mai sunan jejin ‘Bingel, hakika har kwanan gobe ban kara shiga jejin ‘bingel ba”

     “Kenan Baffa akwai jeji mai suna jejin ‘bingel?”

    Baffa ya gyaɗa kai

“E Aziza, akwai a wannan jejin ne na tafka babban kuskuren da ban taba yi ba a rayuwata, ko kuma nace ya haɗu min har da tsautsayi! dan a wannan jejin ne tsautsayi ta haɗani da Banju, a da ban san wani abu mai suna tsoro ba a rayuwata! Banju shine mutum na farko da ya fara shuka min tsoro a zuciyata, ba dan komai ba sai dan ikirarin da ya yi a kaina da mutanen yankina a sadda zan kashesa! ba dan komai na tsorata da Banju ba illa ta’adi da b’arnan da ya yi a yankin nan”

        “Ranar wata laraba ba zan taba mantawa ba naje jejin ‘bingel dan nemo wani ganyen magani da zan haɗawa Inna Kab’o mahaifiya ga Jumala Hajjarku ciwon kafa ya sakata a gaba, a lokacin kuma an gano cewa ina son Jumala ita ma kuma tana sona har an fara maganar haɗamu aure, na shiga jejin ‘bingel har na tsinƙe ganyayyakina zan fita, da shike duk inda zanje ina tare da addana kin san fulani da takwabinsu suke yawo ni kuwa harda kifiya nake yawo, kifiyata kuma tana da guba a jiki, sabida shige-shigen da nake yi na saka rayuwata a hatsari dole na dinga tafiya da kariya duk da nasan ni Allah shike kareni, kifiyata ba mutum ba duk wani abu da zan harba da shi sai ya mutu walau na harbi aljanu ko mayu ko wani dabba ko ma me da kika sani, na juyo zan bar jejin bingel ban ankara ba na hangi wani zureren ???? jelar maciji mai cike da ban tsoro, dama kafin nan a kwanaki muna samun koke-koke daga maƙotan yankuna a kan saren maciji wanda nike zuwa dubawa,saren macijin kuma ya fita daban da saren macizan da na sani, to ganin wannan macijin ke da zuwa ban tsaya dogon tunani ba sabida na ɗan firgita na ciro kifiyata har uku na saita macijin na harba, kin san wane harba?” da sauri Aziza ta girgiza kai

” *BAHULA* wanda ƘANWA take a wajan Banju, wanda yake haukan sonta yake ji da ita, ban taba sanin suna rayuwa a wannan jejin ba, sannan ban san da cewa aljanun macizai bane,ni dai na ga Babban maciji kuma na harba, ina harbinta nan naga abunda ban taba gani ba, wato nan ta rikiɗe ta zama mutum kifiyar da ma harbeta da shi daya a kirji daya a juya daya a baya, kafin na farga da abunda na aikata nan naji ihun Banju yana furta “BAHULAAAAA!!” wanda sai da jejin bingel ya girgiza, a lokacin da Banju ya zo ga Kanwarsa Bahula ina tsaye ina kallon Ikon Allah, yayinda lokaci daya naji jikina na rawa, ko a lokacin da Bahula zata mutu sai da ta cewa Banju Dan Allah ya gyara halinsa na mugunta bata so a sake koransa a wannan jejin kamar yadda ya buwayi asalin garin da suke a jejin aka koresu ta hanyar yi musu turaren barkono dan tun asalin Banju mugu ne fiye da misali, a lokacin da na ga haka na matso kusa ina bai wa Bahula hakuri, murmushi ta min bakinta na fitar da baƙin jini ta ce min ba komai tasan ba da gangan nayi ba, sannan ta roƙi alfarma a kan cewa na bar ɗan uwanta Banju yayi rayuwarsa a jejin bingel, sun taso tare kamar yadda aka haifesu tare dan su ma yan biyu ne, a hannun Banju Bahula ta cika, Bahula tana mutuwa Banju ya hau kuka ina basa hakuri dan babu taimakon da zan iya yiwa Bahula dan guba ya shigeta,hakika nima nayi kukan kuskuren da na aikata, nan na dinga ba wa Banju hakuri, amma abunda ya ce min shine, shi *BAYA MANTUWA,KUMA BAYA YAFIYA* a lokacin Banju ya yi yunkurin kasheni amma ya kasa, yayinda ni kuma na gudu,ina zuwa gida banyi nauyin baki wajan faɗawa mutane abunda ya faru ba,tabbas a lokacin mutanen kwana sun tsorata matuka,inda aka yi cincirindo aka je aka ba wa Banju hakuri amma ya nuna sam ba zai hakura ba, bayan kwana biyu da faruwan haka nan yankin kwana ta koma mace-mace na hanyar kisan maciji ko kuma kisan gilla ta sanadin wani gurb’ataccen guba wanda Banju ne ke yi, a kwana biyu Banju ya kashe mutane sama da dari a yankin kwana, nan fa zaman lafiya da kwanciyar hankali ya kare mana, ba mu sake yin kasa a guiwa ba muka sake zuwa wajan Banju basa hakuri amma kamar mun sake zugasa ne muna tunzura shi, ba zan iya ƙayyace miki mutanen da Banju ya kashe ba Aziza, haka ya bi dangin Jumala mahaifiyarku ya kashesu ita daya kawai ta tsira, a lokacin Arɗo ya dauketa ya kaita gidansa sannan ya daura mana aure da ita, a lokacin Baffa Mandi shi ne sarkin fulanin kwana, haka shima iyayensa matansa yaransa da duk wani danginsa sai da Banju ya kashesu! a lokacin ko yaro aka haifa yau Banju ya samu zai kashe, babu kalar farmakin da Banju bai kawo min, akwai sadda yankin kwana ya koma zallar ƙura ne ke tashi tare da jinin mutanen da basuji ba basu gani ba,nan nayi tattaki naje na samu Banju nace masa daukar Fansansa a kaina ne meyasa yake so ya shafe yankina, ina nine na masa laifi to ya kasheni ya kyale jama’a amma nan yace min ko da ya kasheni ya min alkawari babu wanda zai rage a raye a mutanen yankin kwana sai ya kashe kowa! ko da kuwa ɗan da yake ciki ne sai ya kashesa! a lokacin nayi niyyar na miƙa wuyata ga Banju amma na fahimcesa kamar yadda ya faɗi ba zai kyale kowa ba, nan jama’ar kwana aka hadu aka yi tattaunawa inda kowa ya kawo shawara a kan na kashe Banju dan abun nasa yayi yawa,da fari naqi amincewa sai daga baya na amince, a lokacin da zamu gwabza na fahimci ba zan iya kashe Banju kai tsaye ba,kamar yadda shima ba zai iya kasheni kai tsaye ba, a lokacin ne na tafi jejin lore aka bani zare mafi hatsarin gaske, wato zaren saƙar dana, a wajan yanki muka gwabza da Banju gaban dukkan  mutanen yankin kwana, kin ga wannan takwabi da shi na kashe Banju bayan na saƙa zaren saƙar dana na naɗe a jiki na sokesa da takwabin a ciki, nan ya fadi yana aman jini amma jinin ba ja bane kore ne, kafin ya fadi kasa shine ya mana alkawarin cewa zai dawo daukar fansa a kaina ta ko wace hanya dani da mutanen yankin nan, to kinji abunda ya shiga tsakanina da Banju!”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button