AZIZA DA AZIMA 21-30

Baffa na gama ba wa Aziza labari tasa kuka tana fadin
“Kenan yanzu Baffa Fansar da Banju yake dauka a kanmu ne? Innalillahi wa inna ilahirrajiun! Yanzu Baffa kashemu zaka yi?” Baffa ya girgiza kai yana fadin
“A’a Aziza! Kin taba ganin Uban da ya kashe yaransa ne? Amma idan ta kama zan iya Kashe Azima dan tsaida wannan bala’in,idan ba haka ba tabbas ba a fara mutuwa ba, ke rabaki da Bahula ba zai yi wuya ba, amma ko da an rabaki da ita ke Banju ya maidaki Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinki ba sai ta jikin Azima, kuma ni bana da masaniyar makarin abunda Banju ya miki, amma akwai wani Babban Malami mai suna Malam Shadi a can yankin ja’o zamu je wajansa dan ya mana bayani,ki kwantar da hankalinki, amma kafin nan muna da bukatar tsaida Azima mu ɗaureta, ki daina kuka kinji? Tashi mu tafi gida” Aziza ta miƙe tana share hawayenta suka nufi gida, a hanya kafin su karasa Baffa ya haɗu da Salti ɗan gidan Jauro mai maganin kwana aljanu sun bugesa, da sauri Baffa ya yi kansa yana dubasa,girgiza kai ya yi yana fadin
“Sai da nace kar wanda ya fito ai ga irinta nan, taurin kan Salti iri daya ne da na Ubansa Jauro” Baffa ya faɗa yana daukar Salti, gida suka nufa suna isa Baffa bai yi nauyin baki ba ya gaya musu ai Banju ne a jikin Azima, Bahula kuma tana jikin Aziza, sannan ko an raba Aziza da Bahula Banju ya maidata Macijiya, wani kuka mai rikita zuciya Hajja ta kuma sakawa, yayinda Aziza ta faɗa jikinta suka hau yi tare, Baffa Mandi ya ce
“Abun da za ayi yanzu shine, ya kamata muje wajan wannan Malamin wato Malam Shadi na can yankin Ja’o mu je zuwa gobe kawai dan bamu ga ta zama ba, amma kafin nan dan Allah kar a fadawa jama’ar gari dan ba a san me hakan zai haifar ba har sai munje an dawo, mu da muka sani ya tsaya a iya mu kawai” aka amsa da hakane, nan Arɗo ya ce
“Magaji? Ana ta wannan maganar ina Azima?”
????????????????????
COMMENTS BUT PLSS DON’T SHARE BA DAN NI BA DAN ALLAH DA MANZON ALLAH ????????????[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_
????????????????????
*PAID.*
????️==2️⃣7️⃣↪️2️⃣8️⃣
“Azima?” Baffa ya nanata sannan ya kuma cewa
“Tun sadda ta b’ace ban ganta ba” Aziza dake kuka a jikin Hajja ta miƙe tana goge hawaye ta ce
“Baffa bari na dubota na gani tana ina” Baffa ya ce
“To dubota Aziza” rufe ido Aziza ta yi ta shafa hannun damanta da hannun hagunta,amma abun mamaki bata ga Azima ba, saurin bude ido tayi tana fadin “taya hakan zai faru?”
“Menene Aziza?” Arɗo ya tambayeta
“Arɗo bana ganin komai,bana iya ganin Azima amma taya hakan zai kasance?”
“Ki sake dubawa Aziza” Baffa ya faɗa Aziza ta gya ɗa kai tana fadin to Baffa, ta sake rintae ido amma wayam, sake buɗe ido ta yi ta ce
“Wlh bana ganinta, Baffa ya ce zan duba da kaina amma sai bayan munyi sallar magriba fatana dai daya kar ace Azima taje ta yi wani ɗanyen aiki”
“In sha Allahu ma ba zata yi ba” cewar Baffa Mandi, kamar yadda Baffa ya faɗa bayan sallar magriba ya hau duba inda Azima take amma abunda bincikensa ya nuna masa shine kwata-kwata Azima bata yankin kwana ta fice gabadaya daga wannan sassanin, a firgice Baffa ke furta kalman “INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN! ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATIHI WA AKHLIFNI KAIRAN MINHA!” da gudu Hajja da Aziza suka shigo suna tambayar Baffa menene? “Azima bata yankin nan kwata-kwata,bata wannan al’ƙaryan! ta bar wannan sassanin, Banju ya ja min ‘ya sun bar wannan yankin!” cewar Baffa hankalinsa a matuƙar tashe, Aziza ta ɗora hannu a kai tana fadin
“Wlh Baffa ta sha fadin tana son shiga cikin inda yake da mutane da yawa ta tarwatsasu,kenan ina Azima ta nufa!? Duk inda zata je dai ba alkhairi zata shuka ba,dan nasha gaya mata shiganta mutane ba alkairi bane, yanzu miye abun yi Baffa?” girgiza kai Baffa ya yi ya ce
“Ban sani ba Aziza! Allah ya kaimu gobe asubanci zamuyi mu tafi yankin ja’o dan zuwa wajan Malam Shadi” Aziza ta juya tana kallon Hajja wacce ta kasa tsayar da hawayen da ke zuba a idonta, a hankali Aziza ta fice a bukkar tana sharan hawayen tausayin iyayenta, Aziza na fita Baffa ya matso kusa da Hajja dake hawaye tun tana kuka mai sauti har ta koma kukan baya fita sai ambaliyar hawaye, cikin sigar rarrashi Baffa ya ce
“Jumala kiyi hakuri! Ki dage da addua muna kai wa Allah kukanmu! Dan Allah ki daina wannan kukan kar ya jawo miki ciwo, kinji!?” dago jajayen idonta Hajja ta yi ta watsasu a cikin na Baffa wanda tun tahirin aurensu bata taba kallon tsakiyar idonsa ba sai yau, muryarta a dashe ta ce
“Ciwo? Ciwo fa ka ce Baffan yan biyu? Wani irin ciwo ne ya fi na zuciya? Shin kasan ya nake ji a raina?”
“Ko ma ya kike ji ki yawaita nanata kalman Innalillahi wa inna ilahirrjiun! ya zaki dinga jin sassauci a ranki, sannan…..”
“Don Allah Baffan ‘yan biyu!” Hajja ta kasa Baffa ba tare da ya idasa maganarsa ba, cikin zafafan hawaye ta dago ta ce
“Ni dai kawai abunda nake bukata a wajanka shine ka dawo min da yarana! Ka dawo mini da Azima da Azizana, ni dai ban haifi macizai ba! mutane na haifa,idan wani abu ya samu Azima da Aziza hakika zan iya mutuwa kawai ka dawo min da yarana!” ta tashi ta fice da gudu a bukkan, Aziza dake maqale a jikin bukkan tana sauraronsu ta riƙe bakinta gam tana kuka itama da gudu ta fice a gida ta yi rafin jimulo, taje ta ci kukanta har ta godewa Allah kafin ta dawo gida, bukkar Hajja ta shige ta sameta zaune ta zauna kusa da ita ta ɗora kanta a kan cinyar Hajja ta ce
“Hajjana! Inaji a jikina kamar na kusan barinki! Ba wai ina gaya miki dan na tashi hankalinki bane, duk duniya babu abunda na tsana kamar na ganki ke da Baffa cikin tashin hankali,abunda yasa nake gaya miki Hajja dan na nemi yafiyarki ne! Hajja ki yafe min idan har nayi miki wani abu a zaman da muka yi dake! Kowa da kalar kaddararsa amma mu wannan shi ne namu kaddara! Ba mu kasance cikin mutane da zamu yi rayuwa dake ba Hajja,dan Allah ki yafeni! Ki yafemini!!” Aziza ta karasa da sakin kuka mai ban tausayi da karya zuciya,tana sa kukan Hajja ta rungumeta tana bubbuga bayanta dan tama kasa magana ko tace zatayi maganar ma muryarta ba zai fito ba dan ya dashe!” su na nan suna kuka har dare ya tsaga kafin Baffa ya shigo ya musu umarni da suyi alwala suyi sallah, hakan kuwa ta kasance, Baffa ne yaja su sallah suna gayawa Ubangiji, da haka har asuba ta yi basu rintsa ba.