AZIZA DA AZIMA 21-30

Bayan Baffa ya dawo daga masallaci tare suka shigo da Ardo da Baffa Mandi, a lokacin Aziza da hajja suna zaune sunyi jingum-jingum, Baffa ya ce
“Aziza ta shi mu tafi, Jumala ke kuma ki tafi gidan Arɗo” ko uhum Hajja bata ce ba tana riƙe da hannun Aziza,fuskokinsu a kumbure,shima Baffa ɗaurewa kawai yake yi baya so ya kara karya musu guiwa amma da zai samu dama da shima ya sha kukan nan ko zai samu mai rarrashinsa, da kyar Aziza ta zare hannunta daga na Hajja ta fice da sauri jin wani kukan na shirin cewa a ba shi hanya, Hajja kuwa tuni ta sake saka wani kuka tasa hannuwanta a fuska, saurin ficewa Baffa ya yi jin hawaye ya fara bin fuskarsa, yana fita babu b’ata lokaci suka hau doki, da Baffa da Baffa Mandi da Arɗo sai Aziza, suna hawa doki suka dauki hanyar yankin ja’o ba tare da bata lokaci ba.
????????????????????
Tun bayan da Azima ta bar yankin kwana take aikin tafiya ba tare da ta gaji ba dan bata jin gajiya a tattare da ita, hakika tana shan tafiya, dan kuwa ace mutum wanda yake ba aljani ba idan zai fita daga yankin kwana zuwa cikin garin kafin ya iske titi a kan doki sai ya shafe sati biyu, shiyasa su haka suke ba a shigo musu su ma kuma basu shiga gari dan nan ne rayuwarsu a kauyensu mai cike da abun burgewa da albarkatun korayen shuke-shuke, a kwana daya Azima ta yi rabin tafiya abunka da ba tafiyar mutane ba.
????????????????
Sai kusan gaff azahar su Baffa suka isa yankin ja’o ba tare da bata lokaci ba aka musu iso izuwa ganawa da Malam Shadi, suna shiga bukkarsa Malam Shadi na haɗa ido da Aziza ya hau salati yana sanar da Ubangiji nan gaban Baffa ya bada dammm! amma ya daure suka zauna ana gaisawa cikin mutunci da mutuntawa, Malam Shadi ya kalli Baffa ya ce
“Ohh Allah Magaji Mazan fama kana raye? Yaushe rabonka da yankin nan? Inaji fa tun sadda wan can muguwar mayyar ta sakamu a gaba kazo ka rabamu da ita ban sake ganinka ba sai dai kayi aike” Baffa ya yi murmushin boye damuwa ya ce
“Wlh kuwa Malam Shadi,tun sadda na daina shige-shige naji komai ya fita a raina”
“Allahu Akbar” cewar Malam Shadi yana kallon Aziza da ta dukar da kai gabanta na faduwa, ya kalli Baffa cike da al’ajabi ya ce
“Magaji Bawa ina ka samo *MACIJIYA!?*” juyawa Baffa ya yi ya kalli Aziza da ta rakube ta dukar da kai kasa kamar ma kuka take yi,sannan ya maida kallonsa ga Malam ya ce
” ‘yata ce Malam, na kawota ne wajanka dan ka duba min ita, Banju da na kashe yace zai dawo shine ya dawo daukar Fansa a kan yarana, yanzu haka dayar ta bar yankin kwana kwata-kwata, ita kuma wannan ka ganta nan, shine nace bari na kawosu wajanka dan a san ta yadda za a rabasu da su,bana so gwagwarmayan da nayi ya shafe yarana”
“Shafa kuma ta nawa magaji? Ai shafa kam an gama shafansu tunda gasu nan a macizai” cewar Arɗo, Malam Shadi ya gya ɗa kai yana fadin
“Ya Hayyu Ya Qayyum Ya Zuljalalu wal’ikram, hakika Banju mugun aljani ne, Banju mugu ne fiye da tunanin me tunani, amma Magaji kai ma zaka iya yiwa yaranka magani ai”
Girgiza kai Baffa ya yi ya ce
“Zan iya sake kashe Banju, amma abunda nake tsoro shine Banju na rayuwa ne a cikin Azima yana tafiya ne da kafafunta, yana aiki ne da hannuwanta,yana gani ne da idanunta,yana motsi ne da motsinta, sannan a binciken da nayi Azima a sume take a jikin Banju, idan har na kashe Banju to tabbas Azima ma ta tafi, na duba na ga ita Aziza rabata da Bahula ba wata damuwa ba ce, amma kuma tashin hankalin a nan shine,ko Bahula ta bar jikin Aziza, Aziza ba zata samu lafiya ba dan Banju ya maidata Macijiya sabida bai samu yadda yake so a jikinta ba” jinjina kai Malam Shadi yayi bayan Baffa ya gama yi masa bayani, Baffa ya kuma cewa
“Ina da bukatar taimako dan bana so na salwantar da rayuwar yarana! Jumala ba zata yafemini ba,sannan nima bazan yafewa kaina ba Malam Shadi”
“Matso nan kusa dani Aziza karki ji tsoro” Malam Shadi ya fada yana kallon Aziza, a hankali ta taso ta matso kusa da shi ta duka, wani magani ya ɗiba a kasko ya watsa mata a fuska,ihu Aziza ta saka tana furta “Ya Allah! Ya Allah! Ya Allah! Baffana zafii!!” abun tausayi, hawaye ne ya cika a idon Baffa yana ji kamar ya tashi ya fita amma ina ba hali, Malam Shadi yasa hannu ya damƙi goshin Aziza da karfi, murkususu ta hauyi tana son kwacewa amma ta kasa,rintse idonsa ya yi yana gane-gane da hange-hange, ya dau lokaci yana riƙe da goshin Aziza wacce ke murkususun azaba har sai da ta suma kafin Malam Shadi ya saketa, Baffa ya yi saurin taro ‘yarsa ta fada jikinsa,jikinsa na rawa hawaye na zuba a idonsa ya d’ago ya kalli Malam Shadi yana fadin
“Malam me ya sameta?”
“Haba Magaji! Sai kace baka san yanayin aiki ba,ka kwantar da hankalinka zata farfado, amma gaskiya akwai babbar matsala wanda ba zan iya ce muku komai a kai ba, akwai aikin da nake so nayi cikin dare ina so na bincika na ga taya za a rabasu da mugun nan Banju, sannan Babban tashin hankalin shine ‘yar uwarta Banju ya jata sun bar al’ƙaryan nan,ina take? Ina za a ganta? Duk babu wanda ya sani” Arɗo da Baffa Mandi suka sharo zufar tashin hankali, Malam Shadi ya ɗora da cewa
“Babban damuwar shine abunda Banju zai ja Azima ta aikata,amma zanyi bincike a kai yau In sha Allah,ina dai a nan zaku kwana?” Baffa suka amsa da eh, sannan Malam Shadi ya kira wani almajirinsa yace ya kawo masa tarbama wanda yake na kara ne, bayan an kawo ya ce a shinfiɗe Aziza a kai, bayan Baffa ya kwantar da Aziza Malam Shadi ya kunna mata hayaki, sannan suka fita waje suka zauna suna tattauna yadda zasu yi a kan lamarin.
????????????????
Sarki Chubado ne da mai unguwan kwana ori suke tattaunawa a kan batun Azima da Aziza Macizai ne,suna ta alhinin lamarin, su biyu suke magana a kan cewa suna tausayawa Baffa, a garin yaya sai ga Salti ɗan gidan Jauro mai maganin yankin kwana yazo wucewa caraf a kunnensa, dan Salti ba dai gulma ba,nan yaji duk wani tattaunawa da Sarki Chubado da Ori ke yi a kan lamarin har da tafiyar da su Baffa suka yi yankin ja’o, da gudu Salti ya kwasa yana fadin zai je ya gayawa Baffansa dan yasan zai yi farin ciki da wannan labarin da zai kai ma sa.
????????????????????
Comments
Ko da Salti ya isa gida ya kwashe kaff yadda yaji su Sarki Chubaɗo da mai Unguwa Ori suka tattauna ya gayawa Baffansa, a hankali Jauro ya mike yana murmushi ya ce
“Salti,tun da kake kwaso gulma baka taba kwaso mai amfani ba sai yau, jeka dole nayi maka kyautar shanuwa daya” da sauri Salti ya miƙe yana murna ya fice,Jauro ya dungule hannu yana dukar iska ya ce
“Lokaci ya yi da zan fatattaki Magaji Bawa, ka fi ni a komai kyau,martaba,baiwa,kyakkyawar mata Jumala,ga kuma yara kyawawa! kai kana gani ka fi kowa ne! zargin da nake yiwa yaranka ya tabbata, wato ma har b’oye-b’oye ake yiwa mutane ana munafurtarsu kar a gaya musu gaskiya, to ni nan zan bayyanawa jama’a su waye Azima da Aziza!” ya faɗa yana murmushin mugunta.
????????????????
Kamar yadda Malam Shadi ya faɗa da daddare ne ya yi bincike mai zurfi dangane da matsalar su Azima da Aziza,inda ya hangi gagaramin matsala mai rikitarwa inda tausayin yaran ya kamasa dan kuwa da wuya a samu maganin warakarsu.