AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 21-30

       Da washe gari bayan sun idar da sallar asuba ana gaggaisawa bayan sun gama gaisawa Malam Shadi ya kalli Baffa sai kuma ya duƙar da kai, Baffa ya yi murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo ya ce

“Malam Shadi karkiji komai gaya min ko ma miye ne,ni musulmi ne kuma nayi imani da kaddara mai kyau da marar kyau, ka gaya min kawai”

      Jinjina kai Malam Shadi ya yi ya ce

“Tabbas ni shaidan hakane Magaji, wato a gaskiya ba zan boye maka ba, samun lafiyar Aziza yana tattare ne da Azima, domin kuwa wanda yake da alhakin abun ya ja Azima basu yankin kwana balle a musu magani, kai ko da Azima bata bar yankin kwana ba da wuya a samu wanda zai yi jahadin taimaka musu” goge gumi Baffa ya yi ya ce

“Malam Shadi ka gaya min kai tsaye kawai zan fi ganewa,dan a yanzu ji nake kamar kirjina zai tsage zuciyata ta faɗo kasa”

      Malam Shadi ya gyara zama ya ce

“Dole sai sunyi aure kafin Banju ya rabu dasu, barin ma Azima ita ce wacce take bukatar taimakon gaggawa, sannan wannan miji da zai auresu sai ya sadu da Azima kafin Banju ya fita a jikin Azima, idan Banju ya bar jikin Azima a cikin kaso dari mun yaƙesa kaso sittin, idan aka yi sa’a idan Banju ya fita a jikin Azima, Aziza zata iya samun lafiya,idan kuma bata samu ba ita ma dole sai wanda ya aureta ya kusanceta kafin makarin sihirin da Banju ya mata na siddabarun maidata macijiya ya karya”

       “Ma’asabamun musibatin Qalu Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Innallahi wa inna ilaihirrajiun! Innalillahi wa inna ilaihirrajiun!” shine abunda Baffa da Baffa Mandi da Arɗo suke iya nanatawa suna fifita da hannunsu,Arɗo ya girgiza kai ya ce

“Tabdijam kawai Allah ya jikan Azima da Aziza, dan kuwa na tabbata babu namijin da zaiji cewa su macizai ne ya taimaka ya auresu har mu sa ran zasu samu lafiya”

      “Kuma dole wanda zai aure su zai fuskanci ƙalubale kafin ya kusancesu,sannan bayan ya kusancesu zai iya kamuwa da mugun ciwo amma ba ina nufin ba zai warke ba amma tabbas zaiji a jikinsa,idan an samu damar hakan zaka iya kara kashe Banju a karo na biyu” hawaye ne Baffa ya hau yi yana kan tasbihi ga Ubangijin talikai, Baffa ya ce

“Tabbas da ace na dinga ganin tashin hankalin nan na b’arna da ta’adin da Azima ke yi da ni da kaina zan kasheta! to amma yanzu tana ina? Me take yi? Su wa da wa zata kashe!? Akwai tambayoyi dayawa a raina wanda babu wanda zai amsamin” Baffa ya hau kuka Arɗo da Baffa Mandi suna rarrashinsa, Baffa Mandi ya kalli Malam Shadi ya ce

“Malam Shadi, yanzu ya maganar raba Aziza da Bahula?” 

      “A gaskiya Mandi ni a ganina a shawarce, kar a raba Aziza da Bahula, tinda bata cutar da ita, sannan ko an raba Aziza da Bahula Aziza fa ba zata taba komawa mutum ba, ni a ganina tunda Banju yana son kanwarsa Bahula sannan yasan cewa tana rayuwa a jikin Aziza dole wata rana zai dawo, karku manta kamar yadda Azima da Aziza suke ‘yan biyu haka ma Banju da Bahula suke ‘yan biyu, zamu iya samun dawowa da Azima gida ta hanyar Bahula dake jikin Aziza,ni a ganina kar a raba Aziza da Bahula a barsu tare idan ya so aka samu wanda zai yi jahadin aurensu bayan an raba Azima da Banju sai a raba Aziza da Bahula”

      “Tashin hankali wanda ba a sa masa rana” cewar Arɗo yana kan rarrashin Baffa dake kuka wi-wi, da kyar suka rarrashi Baffa ya samu ya tsaida hawayen idonsa sannan ya miƙe yana yiwa Malam Shadi godiya ya ce masa zasu wuce yau, Malam Shadi ya ce

“Ba damuwa Magaji,karka damu Allah zai shiga cikin lamarin” Baffa bai iya ya kara cewa kala ba, Malam Shadi ya miƙa masa wani ganyen magani ya ce

“Wannan idan ka je ka haɗawa Aziza,ita kuma Azima Allah ya dawo da ita cikin gaggawa, bari nasa a kira muku Azizan sai ku wuce” su Baffa Mandi da Arɗo suka yiwa Malam Shadi Godiya sannan suka fito a tare,bayan an kira Aziza ta fito Baffa ya kama hannunta idonsa jajur ya ɗorata a kan doki, Aziza tunda ta ga yanayin Baffanta tasan cewa kwai gagarumin matsala, haka sukayi sallama da Malam shadi cikin amince suka kama hanyar yankin kwana.

       ????????????????????

Sai da lokacin sallar azahar ya gauta kafin suka iso yankin kwana kai tsaye gidan Arɗo suka nufa, Hajja na zaune tayi zugum Yawuro ta ajiye mata kwaryan nono a gabanta amma haka nonon ke kallonta, Yawuro ke fadin

“Haba Jumala! Dan Allah ki sa wani abu a cikinki mana, ga jikinki da zafi, kiyi hakuri mana haba dan Allah” hawaye Hajja ta goge ba tare da ta cewa Yawuro Uffan ba, sallamarsu Baffa ne yasa Hajja ta dago da sauri ta sauke idonta a kan Aziza da ta shigo kanta a sunkuye, duk irin kunya na Hajja amma da sauri ta tashi ta rungume Aziza wacce itama ta saki kuka take ji a ranta da ace kisan kai ba haramun bane babu abinda zai hanata bata sha guba ta kashe kanta ba, kuka sukeyi sosai sai da Inna wuro ta dakatar dasu, sannan Inna wuro ta hau tambayarsu ya suka yi a can yankin ja’o ɗin, Baffa Mandi ya ce “babu amfanin a boye muku, gwara a gaya muku gaskiya” Ardo ya ce “tabbas dan wannan ba abun boyewa bane” nan Arɗo ya kwashe yadda suka yi da Malam Shadi ya gaya musu, wani mahaukacin zare ido Aziza ta yi jin bala’in da suke ciki wai sai sunyi aure an sadu dasu kafin su warke! Wa ma zai auri macizai!? Barin ma wanda zai auri Azima ya ji labarin kisan da Banju ya yi tayi a jikinta ai ma babu mai aurensu,in kuwa dole sai hakane sun zama annoba a cikin jama’a barin ma yanzu da Azima bata nan.

       Sallallami su Inna wuro da Yawuro suke yi suna tafa hannuwa yayinda Hajja ke girgiza kai tana fadin ita a maido mata da yaranta tana wani irin kuka, Arɗo da Baffa Mandi suka ce Baffa yazo su je wajan Sarki Chubado da mai Unguwa Ori su gaya musu halin da ake ciki,    a tare suka fita aka bar Hajja da kuka ita da Aziza, su Inna Wuro suna rarrashinsu.

@@@@@@

        Bayani dalla-dalla suka yiwa su Sarki Chubaɗo da mai unguwa Ori yadda Malam Shadi ya shaida musu, Sarki Chubado ya ce

“Tashin hankali, gaskiya Banju ya mana illa dayawa, amma ina da shawara mai zai hana a gayawa mutanen gari halin da ake ciki, idan ya so sai a nemi wanda zai auresu ko da ba zai zauna dasu ba dai da sun samu lafiya sai ya sake su!”

      “Nima na fara wannan tunanin a raina ranka ya dade,amma abun dubawan a nan shine wa zai auresu?” cewar mai unguwa Ori, tattaunawa suke yi sosai ta yadda za a shawo kan matsalar amma duk inda aka dafa babu mafita, su na nan suna kan shawara sai ga Sanda da mugun gudu kamar wanda yake gudu a iska yana zuwa gabansu sarki Chubaɗo ya zube yana haki, Sanda jika ne ga Yawuro, Arɗo ya ce

“Sanda mahaukacin ina ne kai? Wannan gudu da ka zo a haka sai kace an kawo mana farmakin yaƙi miye haka? Meke faruwa?” kasa magana Sanda ya yi illa hanyar gida da yake nunawa da kyar ya furta “ADDA AZIZAAA!!” da sauri Baffa ya ce

“Me ya samu Azizan?” ya fada yana miƙewa tsaye, Sanda ya ce

“Baffa Jauro ne ya gayyo duka mutanen yankin nan wai zasu kashe Adda Azima da Adda Aziza wai macizai ne sune suka dinga kashe-kashe sune suka kashe su Ilu mai maganin Maciji dasu Jarman Macizai da Innu Maciji, yanzu haka ma sun saka wuta a gidan Arɗo ƙarami” da sauri su Chubado suka miƙe suna salati tare da al’ajabin ina Jauro yaji wannan maganar? Baffa Mandi ya ce

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button