AZIZA DA AZIMA 31-40

Kuɗi aka fara karba aka zo kanta, ana cewa kawo kuɗinki nan kuwa ta cire ta miƙa ba tare da tayi magana ba ko tasan nawa ta bayar ba,duk da zuciyarta na raya mata da sun isa kanon da zasuje zata kashe mutanen da suke motar!.
Bayan yan wani lokaci ƙalilan mota ta tashi daga tasha ta hau tafiya, inda Azima ta ji ta gaji dan gani take yi motar bata mata sauri,amma ance biyan bukata yafi dogon buri dan haka ta kara rungume hakuri.
Basu da isa kano ba kuwa sai magriba, ganin tsananin girma da faɗi da cikowa irin na garin kano yasa taji ma ta fasa kashe mutanen da tayi niyyar kashesu, ta shagala da kalle-kalle ta ji ana mata magana ta bayanta
“Barka dai ‘yar fulani”
????????????????????????
????????????????
Yau baƙin ciki ne a raina sau biyu ina cin uban typing yana gogewa, Allah dabadin bana son nayi missing update ba da ɗiff zaku jini????
*PAID.*
????️==3️⃣5️⃣↪️3️⃣6️⃣
Cikin gari ya nufa inda ya kaita asibiti mafi kusa, yana shiga ya ce a bata taimakon gaggawa,inda wasu nurses suka hau masa iskanci a kan ba zasu karbeta ba, hannu yasa a aljinun wandonsa ya ciro wallet dinsa ya bude ya ciro ID Card dinsa ya nuna musu, suna gani suka hade gefe suna sorry sir, ya ce
“Baku da tausayi ko kaɗan! haka ku ke yiwa jama’a da haka idan yazo da ƙaran kwana sai marar lafiya ya mutu amma kune sanadi! An san likitoci da tausayi dan haka ku gyara,ina mai wannan asibitin ina son magana da shi idan har yana kusa” jiki na rawa suka ce bari su nuna masa office din, har bakin kofar office ɗin suka kaisa, ya kallesu su biyu ya ce
“Ku fara duba yarinyar nan kar ta mutu ina zuwa bari nayi magana da shi zan zo nayi mata dressing da kaina”
“Ok sir” suka fadi shi kuwa ya shiga ciki da sallama.
Amsawa wanda aka yiwa sallama ya yi, ya kalli wanda ya masa sallamar ya ce
“Bismillah ƙaraso ga waje zauna mana” ƙarasowa ya yi cike da jin kansa ya zauna,sannan ya miƙawa Dr din hannu suka gaisawa, Dr din ya ce
“Amma ban gane ka ba daga ina? sannan baka yi kama da marar lafiya ba” murmushi ya ɗan yi na gefen baki, sannan ya miƙa masa ID dinsa,yana dubawa ya kallesa ya ce
“Doctor?” ya yi murmushi yana gya ɗa kai, tashi ya yi da sauri yana fadin
“Allah dai yasa sa’a ce ta sameni har office zaka fara aiki a hospital dina” shi ma tashi ya yi tsayen ya ce
“A’a ko ɗaya wlh,ai ni ba a nan yola nake da zama ba,ina zama a kd ne akwai aikin da ya kawoni ne,tun jiya ma ya kamata ace na bar yola to ashe tsautsayi ne ya tsayar dani dan na buge wata yarinya ne da mota shine na kawota asibitin,inaso nayi treatment dinta sai mu wuce dan bana so na ƙara kwana a garin nan”
“Ya Subhanallah! tana ina yarinyar? muje sai ka dubata ai ba komai” ba tare da ya sake magana ba ya bi bayan Dr har izuwa dakin da aka kwantar da Aziza, suna shiga ya hau dubata ya ga bata mutu ba, kayan aiki yace a ba shi ya fadi abubuwan da za a ba sa aka kawo masa sannan ya hau dubata,ya mata su allurai ya sakawa kanta bandage ya mata komai sannan ya ɗora mata ruwa, ya duba agogon dake daure a hannunsa ya ga sha ɗaya, ya kalli Dr ya ce
“Tnk u so much Dr on my way” ya faɗi tare da kokarin daukar Aziza, Dr ya ce
“Haba Doctor ka bari mana ko zuwa gobe sai ka wuce idan ta farka,ga shi kace baka santa ba,duk yadda akayi inaji irin fulanin rugan nan ne, yanzu idan ka wuce da ita kd alhali ba yar kd ɗin ba ce fa?” shuru ya yi yana nazarin maganarsa kuma gaskiya ne tunda a nan ya sameta miye hujjarsa na tafiya da ita? Kawai ya barta idan ta farka taji sauki sai su sallameta ta koma inda ta fito, da wannan tunanin ya ce Dr ɗin ya ba shi acct number ya masa transfer’n kuɗi ya kula da ita idan ta warke sai su sallameta,haka kuwa aka yi bayan ya masa transfer ɗin nan ya fito da sauri ya shiga mota ya tayar yaja ya bar asibitin, har ya fara tafiya ya ɗan yi nisa sai yaji hankalinsa bai kwanta ya tafi ya barta ba,ko ba komai shi ya bugeta sannan bata farfaɗo ba ya tafi ya barta anya ya kyauta kuwa? Saurin juya kan motar ya yi ya koma asibitin, yana zuwa ya ce a ba shi ita kawai, Dr ya ce
“Haba Doctor baka yarda damu bane?”
“No ba haka bane ba wai ban yarda daku bane,kawai ban yarda da shawaran da zuciyata ta bani bane na in tafi in barta alhali ban san a wani condition zata farka ba that’s why, amma yanzu zan tafi da ita,idan ta farka lafiya taji sauki zan sa a maidata gidansu” da haka yasa hannu ya dauketa tare da drip ɗin da ya ɗora mata, har yanzu tana bacci, ya gyara bayan motarsa ya kwantar da ita ya ajiye drip ɗin a gefenta yana duba agogo tare da auna tym din da ruwan zai ƙare” da sauri yaja motar yanayi yana duba tym.
????????????????
Horn ta yi a wani madaidaicin gate da sauri gateman ya zo ya buɗe yana zuba mata kirari, hannu ta daga masa sannan ta danna hancin motar cikin gidan,tana parking ta fito tana fitowa ita kam ma ta manta da ta saka mutum a bayan both cikin gida ta wuce tun kafin ta shiga take kwalawa Lantana kira, da gudu wata ‘yar dattijuwar mata ta fito ta zube a gabanta ta ce “gani *Hajiya Zubaida*”
“Oh dan iskanci dama kinaji ina ta faman kwala miki kira amma ba zaki iya amsawa ba sai dai ki wani fito da mugun gudu sai kace ana gasan tsaren karnuka, ki fa kiyayeni kiyi hankali!, ina Hajiya?”
“Tana ciki”
“Hajiya! Hajiya! Hajiya!” ta hau kwalawa Hajiyan kira.
An ɗau kusan mintuna uku kafin Hajiyar ta fito tana hamma tana matsa ido alamun bacci take yi kiran Zubaida ne ya tayar da ita
“Zuby me ya faru?”
Zama ta yi tana fadin
“Wlh Hajiya sai na ci uban baban mai aikin nan, kin san wai har da kai karar mu police station wai mun yi ‘yarsa duka a bi masa kadi”
“To yanzu ya aka kare?” Hajiya tana tambaya tana zama kusa da inda Zubaidan ta zauna,ta ce
“Na basu kudi nayi gaba abina,kee! Lantana kawo min ruwa mai sanyi” tashi tayi da sauri tana fadin to, sannan Zubaidan itama ta tashi ta shige wani daki wanda yake nuni da nata ne, kaya ta shiga canzawa ta ga ko gyara mata dakin ba a yi ba, da sauri ta cire na jikinta ta watsar dan haka dabi’unta yake, ta saka wani riga iyakarsa guiwarta sannan ta fito tana masifa tana zama
“Haba Hajiya ashe ba a gyara min bedroom dina ba?”
“To Zuby wa zai gyara? Masu aikin duk sun gudu sai Lantana ce kawai ita kuma aiki ya mata yawa” tsaki ta ja tana shirin faɗin yanzu wa zai gyara mata daki sai ta tuno da ta sa mutum a bayan mota, tashi tayi da ɗan sauri tana fadin
“Wayyo na manta da wan can bagidajiyar bafulatanan” a haka ta fita riga iya guiwa kai babu ɗan kwali sai uban attachment, Azima kuwa tana kwance a both a macijiya hankalinta kwance tana bacci, jin kara ne ya sakata buɗe ido tayi saurin komawa mutum,tana zama mutum tana bude both din ta kalleta a wulakance ta ce
“Fito” a hankali Azima ta fito tana gyara mayafinta tana tafiya tana lankwasa kamar yadda take tafiya a yankin kwana.
Shiga parlourn sukayi, Zuby ta ce
“Hajiya naji dama kina neman mai aiki to gata nan, a hanya na tsinceta, sai ta ɗora da aikin da Kuluwa ke yi” Hajiya ta kalleta tana toshe hanci ta ce
“Ya sunanki?”
“AZIMAA!” ta faɗa da kaushin murya dan duk tana kula da yatsine fuska da toshe hancin da Hajiya ke yi.
“To dubu biyar zamu dinga baki a duk wata, zaki dinga share-share da goge-goge,inada yara guda uku, ga Zuby nan akwai Yayarta mai suna Baby sai kuma Babban ɗana namiji yayansu kenan, sunansa Munir dik basu nan sun fita idan suka dawo zaki gansu, ke ce zaki dinga gyara musu bedroom dinsu!” Azima dake duƙe ta ce