AZIZA DA AZIMA 31-40

“Hajiya miye shi badorom din?” Zuby ta ce
“Hajiya ƙidahuma ce daga jeji take taya zaki mata turanci,keee Bagidajiya ana nufin daki,nasan bukka ku ke kira a can jejinku” cije baki Azima ta sake yi, jin yadda zuciyarta ke tafasa idan bata tashi ba komai zai iya faruwa,hannunta ta kalla ta ga ya fara sab’ulewa yana zama blue saurin ajiyar zuciya ta koma yi dan zuciyarta ta yi sanyi, Zuby ce ta sake kwalawa Lantana kira ta amsa da ta zo tace mata ta tafi da Azima ta nuna mata yadda zata yi wanka ta bata wasu kaya da turare dan Azima na wari,sannan idan ta nuna mata ta taho ta saka musu turaren wuta, Lantana ta amsa tana kamo Hannun Azima suka shige daki, suna shiga Hajiya ta ce
“To ita haka zata dinga rufewa mutane fuska a gida?”
“Hajiya manta da wannan kin san bata taba shigowa birni ba,dan haka bata waye ba”
“Kuma hakane fa” cewar Hajiya, Zuby ta ce
“Wai ina Munir da Baby suka je ne?”
“Wa ya san musu” share zan can suka yi suka kamo wata hirar, da Lantana suka shiga daki ta kalli Azima ta ce
“Baiwar Allah zauna ki jirani kinji bari naje na saka musu tiraren na dawo” ta fita da sauri, buɗe ido Azima tayi tana fadin
“Babu wanda ya isa ya zageni ya tafi a banza ba tare da nayi masa hukunci ba! Babu shi!” ta faɗa tana lankwasa yatsun hannunta, an dauki mintuna sha biyar kafin Lantana ta shigo, ta ce
“Azima ko?” Azima ta sunkuyar da kai tana fadin
“E” a sanyaye kaman wata ta kwarai, Lantana ta kama hannunta suka shiga bayi,ta haɗa mata ruwan wanka ta dauko soso da sabulu da shampoo dan ta ga tana da ga shi mai tsayi, ta ce
“Na wanke miki kan naki naga gashin naki da tsayi sosai” Azima ta gyaɗa kai, Lantana ta bata fallan zani ta ce ta cire na jikinta ta ɗora, ba musu Azima ta cire kayanta ta ɗora fallan zani lantana ta jiƙa mata kayan a ruwa tace zata wanke mata su, sannan ta bata kujera ta zauna, Lantana na fara kwashe gashin Azima tayi saurin lumshe ido dan bata son Lantana ta ga kwayar idonta.
Shampoo sosai Lantana ta zuba a kan Azima amma ta ga idan har ta juye ba isa wanke mata kai zaiyi ba, haka yasa ta dauke ledar omo sai da ta zuba ya kai kwankwani ɗaya da rabi kafin ta fara dirzan kai Azima wanda yake fitar da datti, sun kai mintuna talatin tana wanke mata kai kafin gashin ya fito baƙi da shi ga tsamtsi yayi fess! Lantana ta yi murmushi ta ce
“To kiyi wanka,bari na baki waje” har Lantana ta kai bakin kofa sai ji tayi Azima na faɗin
“Miyatti Inna” karo na farko da ta fara yima wani ɗan adam godiya a rayuwarta, murmushi Lantana ta yi ta fice, sai a lokacin tunanin ‘yan yankin kwana ya faɗowa Azima a rai,dariya ta hau yi tana fadin
“Ko ina Macijiya Aziza sarkin tausayi oho! Watakila sakaran tana can an kasheta a jeji! Ko da yake ba zasu iya kasheta ba! Amma nasan shanuwar tana can suna jibgarta” ta karasa maganar tana haɗe rai, wanka ta yi sosai ta dirje jikinta ta fito, sai da jikinta ya bushe ta kuma saukowa da gashin kanta kafin ta fito ta samu Lantana ta ajiye mata fallan zani da t-shart da su mai da turare, kayan ta saka, sannan ta dauki kum ta sharce gashin kanta ta zubo da wanda yake rufe masu gefen fuska sabida kar ana ganin kwayar idonsu, gashin ya sauko har ƙirjinta, kallon kanta ta yi a madubi ta ga ta yi kyau,murmushi ta yi, sai ga Lantana ta shigo
“Wa Subhanallahi bi’ahsanul Khaliƙin!” cewar Lantana Azima ta sunkuyar da kai, Lantana ta ce
“Zo muje na nuna miki ayyukanki” Azima ba ta kuma magana ba ta bi Lantana a baya, nunnuna mata komai Lantana ta yi har da dakin Baby da dakin Munir, Azima ta ce ta gane, sannan Lantana ta ce
“Yanzu ki fara gyara dakin Munir dan bai da mutunci ko kaɗan duk wulakanci Baby da Zuby suna bin bayan Munir ne, idan ya dawo ba a gyara masa daki ba ya ganki ba zaiyi la’akari da cewa ke sabuwar zuwa bace ya yi ta kwallo dake”
“DA KUWA KO ƘASHINSA BA ZAN RAGE BA!” Lantana ta ce
“Iyeeee!!?” sauri saita kanta Azima ta yi ta ce
“Inna je ki kawai zan gyara yanzu” fita Lantana ta yi,Lantana na fita Azima ta bi lafiyar gado ta kwanta dan tayi wanka mai dadin da bata bata yi ba taji bacci takeji.
????????????????
Karfe sha daya saura ya shigo kd bai wuce gida ba ya wuce asibitinsa da ita, har yanzu kuma bata farka ba,bai damu ba tunda ya mata alluran bacci mai karfi ne, bayan ya mata komai ya ba wasu nurse mutum biyu kula da ita wanda zasu yi nyt duty, kafin ya wuce gida.
A wani katafaren gate yayi horn da sauri aka zo aka buɗe masa, ya shiga ya yi parking din motarsa, da fari ji ya yi kamar ya shige part dinsa dan ya gaji,amma kuma gwanda ya shiga ya yiwa Mom sai da safe, da wannan tunani ya yi babbar parlon nasu da sallama,kanwarsa Sultana tana zaune wacce ba zata wuce 18 ba tana kallon wani horror seris film tana jin sallama ta miƙe da gudu tana fadin
“Oyoyoo *BROS NAWAZZ!”*
????????????????
MOMYN AHLAN????
[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
???? *AZIMA DA AZIZA*????
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*
*????KAINUWA WRITERS???? ASSOCIATION*????????
“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????
https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*MARUBUCIYAR.*
1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._
2- _GUDU A JEJI._
3- _SHUHADA._
4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._
5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._
6- _COLONEL UBAIDULLAH._
7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._
8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._
9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._
10- _DA NA SANI NA._
11- _BADAWIYYAH_
12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_
Now
13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_
_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_
????????????????????
*INA GAISHEKU KYAUTA YAN PAID GRP MASOYAN……..BAN DAI KARESA BA KU KARASA DA KANKU*
*PAID.*
????️==
Saurin juyowa Azima ta yi ba tare da ta dago ba
Ya yi murmushi ya CE
“Yan mata magana nakeyi fa” da sauri ta matsa gefe ta hau tafiya tana sake rufe fuskarta, shi kuwa binta ya hauyi yana kan yi mata magana,da ya ga ba zata tsaya ba ya sha gabanta, cije baki Azima ta yi tana hade rai,babu abunda ta tsana kamar a sha gabanta,Cikin murya da yake nuna taji haushin takura mata da yayi tace
“Malam wai lafiya?”
Dariya ya hau yi jin yadda kalar Hausar ta ta ke fita, a ransa yake fadin “wow! Wannan daga ganinta bagidajiya ce daga jeji take,bari nayi mata wayo, ko Allah zai sa na shana da ita daga dawowata!”
“Amm yi hakuri ba nufina na ɓata miki rai ba,naga yadda kika ta kalle-kalle ne kamar baki san kowa ba, shine nake so na taimaka miki” ya karasa maganarsa yana murmushi, itama Azima murmushin ta yi ta ce
“To taimakona da me? ko nazo nace da kai inada bukatar taimako ne iyee!!? Na ce maka ina da bukatar taimako ne?”