AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 31-40

“Allah ya huci zuciyarki sarauniyar kyawawa, Kano gari ce mai girman gaske da faɗi kuma ke naga alama kamar baƙuwa ce, dan haka ki yarda na taimaka miki naga ke mace ce,ki zo muje gidanmu” mutuwa da mamaki Azima ta yi ko me ta tuna ta yi murmushi ta ce

“Na gode da taimako muje”

“Ina kayan ki?”

“Wala!”

Ta ba shi amsa hankalinta yana can wajan kalle-kalle, jakarsa da ledarsa ya dauka ya ce

“Muje” ya yi gaba ta bisa a baya, kekenapep ya tare musu suka shiga, wani farin ciki ne ke mamaye zuciyar Azima sai magana yake mata amma ina hankalinta ya yi ƙololuwa wajan ganin girma da faɗi da cikowa irin na NA DABO TUMBIN GIWA, ana cikin tafiya sai ji ta yi kekenapep din ya tsaya sai a lokacin ta maido da dubanta ga wani ƙazamin gida wanda ko bukkarsu na yankin kwana ya fi sa kyawun gani, bata damu ba, yayinda ya ce mata ta fito a keken, ba musu kuwa ta fito tana kallon mutanen da suke zaune a kofar gidan masu caca da masu shan wiwi da sigari har ma da masu shan giya, jin yadda ta hadiyi hayakin sigari da wiwi yasa ta hau tari kadan-kaɗan tana yamutse fuska, mai kekenapep ya biya sannan ya kalleta ya ce

“Mu shiga ciki ko?” ya yi gaba ta bisa a baya mutane sai kallonsu suke yi har suka shiga,suna shigewa a cikin wa inda suke zaune a kofar gidan wata mace tayi shigar riga da wando,duk da babu mai kayan mutunci a cikinsu, tab’o dayar dake kusa da ita ta yi ta ce

“Kee Bariki Dadi, baki ga Hoge ya wuce da wata bafulatana ba?” wacce aka kira da sunan Bariki dadi tana riƙe da sigari a hannunta tana zuga suna buga caca ta ce

“Hoge dai? Yaushe ya dawo?”

“Ba mamaki dawowarsa kenan dan na gansa da kayansa” miƙewa tayi da sauri ta ƙudundumo wani ashar sannan ta yi cikin gidan da sauri wa inda suke zaune a tare suka hau zugata suna fadin “idan kinje kici uwarta da ubanta! Bariki dadi! Baki da kyau baki da dadi!” suna fadi suna ihu,ita kuwa fuuuu tayi ciki,a lokacin Hoge har ya buɗe a kulkin dakinsa ya kalli Azima ya ce

“Shigo mana yar fullo” a hankali Azima ta sa kafa ta shiga, a wani jagalgalalliyar katifa ta zauna tana saƙa abubuwa dayawa a ranta, tana zama sai ga Bariki dadi ta banko kofar kamar zata b’alla shi, Azima bata dago ba illa Hoge dake fadin

“Wannan wani irin iskanci ne haka?” 

“Ga ka nan kuwa babban dan iskaci baƙin munafuki! Ka hanani kula ko wani bunsuru, sannan ka dauko wata banziya daga dawowarka ka huce da ita a gabana! To wallahi sai naci Uwarta! Ke kuma munafuka zo nan! Sai wani rufe fuska kikeyi sai kace wata ta Allah kina sunkuyar da kai, to idan baki sani ba ki sani! Kina sa kafarki a nan gidan dukkan wata mutuncinki ya zube kuma saina koya miki hankali!” murmushi Azima ke yi a ranta ta ce

“Inason mutane irin haka! Wa inda basu shiga gonata ba ina kau dasu balle wa inda suka shiga” bata gama maganar zucinta ba Bariki dadi ta shaƙo wuyarta, tashi tsaye Azima tayi,tana tunanin dame zata kasheta! ta sareta ne ko ta watsa mata dafi? Hoge ne ya fizgi Bariki Dadi ya koɗa mata mari sannan ya ingizata waje ya juyo yana ba wa Azima hakuri, bata ce masa ci kanka ba,illa da ya gama rawar bakinsa ya fice wai zai kawo mata abinci, bai jima ba kuwa ya shigo da bakar leda ya ajiye mata, budewa Azima ta yi nan tayi arba da kayan dadi murmushi tayi dan bata taba ganin kalar abincin ba, da sauri ta buɗe ta hau ci tana lumshe ido tana gya ɗa kai, shi kuwa yana zaune a gefe yana kallon gashin kanta da ya rufe mata fuska aransa ya ce

“Hummm! dama ana ganin irin wa innan matan a gaske? Dole na shana wlh,daga ganin wannan ɗanya ce jaƙab, zatayi ruwa zata kai yadda ake so, idan tayi daga nan zata zama cikata!” sai sambatu yakeyi a zuciyarsa yana hadiye yawu,Azima kuwa fess ta cinye abubuwan da ya kawo mata, ta kwankwaɗe maltina har tana lashe baki, tana gamawa ta koma ta jinginu da banko tana sauke ajiyar zuciya ta lumshe ido,jin saukar numfashi ta yi a wuyarta, saurin buɗe ido ta yi ta gansa ya matsota sosai, sai wani washe baki yake yi, bata gama karantarsa ba taji yana fadin

“Meyasa kike rufe baiwar kyawun da Allah ya miki da wannan dogon gashin naki? Duk da ba a ganin fuskarki da kyau amma da an ganki an ga kyakkyawa ajin karshe, dan Allah ki buɗe idanunki na ganki,sannan ina so ki bani hadin kai nayi miki alkawari zan baki duk abunda kikeso zan miki komai” cije baki Azima ta yi jin yadda wani baƙin ciki ya mamaye zuciyarta,daurewa ta yi tasa yatsarta babba manuniya a kan goshinsa, ta ture kansa daga wajan saitin wuyarta sannan ta ce

“Kasan daga ina nake? Sannan ni fuskata kallo daya ake mata,idan har ka gani babu fuskar da zaka kara kalla a rayuwarka”

“E na yarda ni dai ki bude fuskarki na gani, sannan zan baki abun dadi” ya fadi yana shirin kai hannunsa kirjinta,da sauri Azima ta ja da baya tana fadin

“Owohh kenan kai ɗan iska ne! Zan koya maka hankali, ka taba ganin maciji?” 

“E amma a zahiri sau daya na taba gani kuma ƙarami ne ma,amma ina gani a fina-finai”

“To yau zaka ga Babban a zahiri ido da ido!” ta faɗi tana dariya yayinda ta kwashe gashinta ta maida su baya,blue eye dinta ya bayyana, a gigice hoge ya ja da baya, yayinda ta hau rikiɗewa,tun kafin Azima ta taba Hoge numfashinsa ya fara barazanar daukewa, yana ganin zureren Maciji har na sheƙi a gabansa nan ya fadi sumamme, Azima ta sa baki ta saresa a gabansa, sannan ta koma mutum ta fice, ta zo fita kenan suna karo da Bariki dadi,shaƙeta bariki dadi tayi,Azima tace

“Dama kafin na tafi ina nemanki!” tana gami fadi ta zaro harshenta ta watsa mata dafi sannan ta bar gidan.

        ????????????????????

Kuka Hajja keyi yayinda Inna Wuro da Yawuro suke ta aikin bata hakuri suna rarrashinta,amma pinaa Hajja kamar ba da ita ake yi ba, idonta ya kumba ya yi him sabida kuka fuskarta ya yi jaa! Baffa ne ya duka a gabanta ya ce

“Jumala? Kiyi hakuri,In sha Allah idan anyi duniya DAN MANZON ALLAH S,A,W, Azima da Aziza zasu dawo garemu In sha Allah,kuma yaranki zasu dawo mutane ko da kuwa zan rasa raina na miki alkawari!” ita dai Hajja bata ce komai ba, tun daga wannan rana Hajja bata um bata um-um, idan ta zauna idonta na kan bakin kofa,ta ajiye idanunta har izuwa ranar da yaranta zasu dawo gareta.

       ????????????????

Fitan Azima yawatawa ta ci gaba da yi,dama ita ba sallah take yi ba balle ya dameta, idan kuma wani mai kararren kwana tsautsayi tasa ya shiga hidimarta ta kashesa ta yi gaba, yau kwananta uku da shigowa garin kano bata damuwa da wajan kwana idan dare ya yi duk babbar bishiyar da ya mata zata zama macijiya ta hau ta kwanta tayi bacci ko ta huta, yau ta fito tana cikin tafiya taji ƙaran mota ƙiiiiiii! da sauri ta juyo ta ga wata matashiyar budurwa ce wacce zata kai shekara ashirin da biyar,fitowa tayi tana zazzagawa Azima zagi, yayinda take binta da ƙaramin kallo

“Ban da hauka taya zaki rufe fuska ki dinga tafiya a kan titi! Sakarya kawai bagidajiya!!” cije baki Azima tayi meyasa ake son ce mata bagidajiya? duk da bata san ma’anar kalman ba amma taji ta tsani kalman, lankwabe murya ta yi ta ce

“Dan Allah ki taimaka mini, ni yar gudun hijira ce an kashe dukkan yan uwana a rigarmu ni daya ce kawai na rage,ban san kowa ba ban san inda zanje ba, dan Allah ko aiki ne a gidanku ki nema mini zan dinga yi” yatsine fuska ta yi tana fadin

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button