AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 31-40

“Kuma fa kamar naji Hajiya na neman mai aiki,to amma gaskiya sai dai na sakaki a cikin both dina dan ba zaki shiga mini mota ba”

“Ina ne shi hakan bat din?” 

“Banza jahila both nace, nan kenan zo ki shiga” ta fada tana mata nuni da both tana budewa,Azima ta shige tana murmushi tare da fadin

“Matakin farko!” tana rufe murfin both din Azima ta koma Macijiya, shiga motar tayi ta ja tana tsaki.

      A kwana ukun nan Aziza ta fito daga bakin titi ita ma,tana fitowa ta zube a kan titi tana sakin kuka tana kiran sunan Hajjanta da Baffanta, Inno Fandi ce ta taimaka mata ta fiddota bakin titi sannan ita ta koma, kuka sosai Aziza ta yi kafin ta tashi ta hau tafiya, tana ganin kamar ta shigo wani sabuwar duniya ne, bata ma san a inda take tafiya ba, shi kuwa da sauri yake jan mota,yana driving yana duba tym, wayarsa ce ta yi kara yana dubawa ya ga Friend 4 Life, dagawa ya yi, ya ɗan yi shuru tukunna kafin ya ce

“Hey Dude bazan maka karya ba,wlh bazan je na dubasa ba,guy din nan ya raina min hankali, jiya banyi niyyar kwana a garin yola ba amma ya sakani kwana, yanzu haka ma nikam gani a hanya ko kwana zanyi sai dai na kwana amma yau din nan sai na kasance a cikin garin Kd in sha Allahu!” yana magana a waya ransa a b’ace sai ji ya yi, ya yi sama da mutum, wani mahaukacin burki yaja ya fito da gudu, yana isowa gareta tana lumshe ido, duk da bai ga fuskarta da kyau ba gashi ya rufe amma daga ganinta a jeji ta fito, kallon gabas ya yi,ya kalli kudu,ya kalli arewa,ya kalli yamma bai ga wani ɗan adam ba, shi a tunaninsa sun fito kiwo ne yan uwanta suka tafi suka barta, to amma idan haka ne shi ya zaiyi da ita? Ga kanta ya fashe yana zubda jini, “No dogon tunani ba nawa bane i need to save her lyf first” ya faɗa yasa hannu yana shirin daukarta, wani mummunar faduwar gaba ce ta riskesa inda yaji dukkan wata gab’a ta gangar jikinsa ya sake, saurin kauda abun a ransa ya yi ya dauketa ya sakata a mota ganin bata motsa, yana addua Allah yasa dai bata mutu ba.

      ????????????????????

MOMYN AHLAN✍????

[4/13, 10:12 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   ????????????????????

*PAID.*

????️==3️⃣7️⃣↪️3️⃣8️⃣

Murmushi ya mata ta zo ta rungumesa tana yi masa sannu da hanya, ya amsa da “yawwa sannunki,ina Mom kar dai har tayi bacci?”

“Kai anya kuwa, da muna zaune da ita a nan bata jima da tashi ta hau sama ba”

“Okay bari na dubata” ya faɗa yana maida dubansa ga tv’n ya ce

“Ke da kallon horror ko, sai kin fara ganinsu a gaske zaki sani” murmushi Sultana ta yi ta koma tana zama shi kuwa ya hau sama,dakin Mom ya shiga da sallama tana zaune tana waya, zama ya yi kusa da kafarta har sai da ta gama wayar ta ajiye kafin ta kallesa cikin kulawa ta ce

“Nawaz sai yanzu? Ya hanya an dawo lafiya?”

“E wlh Mom, Alhamdulillah! ina wuni? Ya gida? na sameku lafiya?”

“Alhamdulillahi Doctor, fatan dai lafiya ko? Ko dai gajiya ce dan fuskarka ta tuna,yanzu haka ma da Amminka muka gama waya wai ta kiraka wayar bata shiga nace ba mamaki hanya ce ba netwrk”

“E hakane zan kirata gobe yanzu dare yayi zan shiga part dina,kunyi waya da Son dinki ne Mom?”

“E dazu ya kirani dan albarka”

“Mom muna cikin waya da shi dazu tsautsayi tasa na buge bafulatanan yarinyar mutane”

“Subhanallahi!” Mom ta faɗa tana zabura

“Kwantar da hankalinki Mom tana hospital dina” nan ya bata labarin yadda hatsarin ya kasance har izuwa shawaran da ya yanke na tahowa da ita kaduna idan taji sauki sai a maidata gida, Mom ta sauke ajiyar zuciya ta ce

“Shawaran da ka yanke mai kyau ne Nawaz, Allah ya bata lafiya, ma je mu dubata gobe idan Allah ya kaimu ni da Sultana”

“Allah ya kaimu Mom” ya faɗa yana duba agogon hannunsa

“Dare yayi Mom zanje na kwanta na huta akwai gajiya a tare dani”

“To Allah ya tashemu lafiya a huta gajiya,Allah ya yi albarka” Nawaz ya amsa da amin yana tashi ya fice a dakin, yana saukowa ya kalli Sultana ya ce

“Idan baki kashe tv’n nan kinje ki kwanta ba Allah sai na zaneki” da sauri Sultana ta miƙe ta kashe tv’n kasancewar tasan halin Yayan nata, sai da ya ga ta hau sama kafin ya fice ya nufi part dinsa, wanka ya yi ya gabatar da salloli har da nafila ya jima yana addua kafin ya tashi ya koma gado ya kwanta,har ya lumshe ido ya buɗe ya dauki wayarsa ya kira Amininsa suka hau ɗan taba hira inda yake ba shi labari ya buge bafulatana, Allah ya kiyaye gaba ya masa,sannan ya ce

“Yaushe zaka dawo america?” Nawaz ya sauke ajiyar zuciya ya ce

“Nan da 2wks In sha Allahu,but idan nazo ina shekarar karshe zamuyi mu dawo gida gabadaya?,dan gaskiya na gaji da zaman outside”

Daga can bangaren ya ce

“In sha Allahu, duk da ni bana son zaman nigeria gaskiya”

“To ya zaka yi dole ka dawo,duk lalacewa kasarka kasarka ne, sannan karka damu da abinda Momma take maka, ka ci gaba da yi mata biyayya a matsayin uwa,wata rana zata gane In sha Allah” ajiyar zuciya ya sauke, nan Nawaz ya gane damuwar dake damunsa dan haka ya kau da hiran ya jawo musu wata, sun kai biyun dare kafin suka yiwa junansu sallama, yana ajiye wayar bai jima ba bacci ya kwashesa,yana cikin bacci ya hau mafarkin yarinyar da ya buge da mota, suna cikin wani ƙasurgumin jeji sai faman ihun take zabgawa tana fadin ya taimaketa ya taimaki rayuwarta, tana ihu tana gudu yana binta a baya, da haka har suka je jikin wata babbar bishiya taja ta tsaya kanta a sunkuye tana sanye da kayan fulaninta,ta ƙanƙame jikinta tana ihu, shi kuwa yana riƙe da fitila a hannunsa yana haskawa sabida tsananin duhun jejin, yana shirin matsowa gareta ya ga mummunar tashin hankali dan kuwa gani ya yi ta koma wata zabgegiyar macijiya???? fara sol sai ƙyalli take yi,tana ci gaba da ihun ya taimaketa.

     A mugun gigice Nawaz ya farka yana fadin

“INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJIUN!!³” hannu ya miƙa ya kunna wutar dakin ya rike kansa da karfi dan ji yakeyi kamar kan na shi zai faɗo kasa, gabadaya jikinsa ya jiƙe da gumi, yayinda ko wani kofar gashi ta gangar jikinsa ya buɗe sun miƙe tsaye, jijiyoyin wuyansa duk sunyi waje, jikinsa sai b’ari yake yi har yana jin wani zazzabi, da kyar ya jawo wayarsa ya duba tym ya ga karfe biyar, tashi yayi ya shiga bathroom ya dauro alwala ya tada sallah, yana nan zaune yana addua har aka kira sallah, sai da yayi raka’atul fajir sannan ya miƙe da kyar ya fita zuwa masallacin da yake wajen gate ɗin gidansu, bayan an idar da sallah ya shiga ya gaida Mom bai wani zauna ba yace mata kansa na ciwo zai sha magani ya kwanta dan bai samu bacci daren jiya ba, Allah ya kara sauki Mom ta masa ya koma part dinsa ya kwanta, ba jimawa bacci ya sake kwasansa amma still mafarkin daren jiya shine ya kara tayar da shi, cikin kiɗima ya zauna a bakin gado yana tunani barkatai.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button