HAUSA NOVEL

ALAMARIN SUHAILAT Complete Hausa Novel

*_The beginning…_*

*KANO*

B.U.K NEW SIDE, FACULTY OF EDUCATION DEPARTMENT OF PSYCHOLOGY…

Wata hijabyt-Niqabyt lady na hango tana tafiya a hankali daga gani abun hawa take nema, tana yi tana juyawa, wani zubin ma har ta tsaya ko zata ga abun hawa yana tahowa, ganin dai kamar babu alamun abun hawan yasa ta ɗaga ƙafa sosai tana tafiya.

Sanye take cikin brown ɗin hijabi har ƙasa, fuskar ta kuma lulluɓe take cikin niqabi babu abunda kake gani sai fararen idanun ta wainda suke madaidai ta, ƙafar ta kuma cikin brown socks, da takalmin ta half cover light brown….

Sai da tayi tafiya me nisa, har ta kusa fita daga faculty ɗin nasu, sannan taji tahuwar wata bus da student Suke hawa wanda suke kiran ta da modesty.

Yana ƙarasowa inda take ya tsaya kasancewar yasan abun hawan take nema, shiga tayi ya kawo ta bakin gate ɗin makarantar, a nan ne kuma ta samu me napep wanda zai sada ta da unguwar su da take zoo road sabuwar mandawri shagari quarters, sun yi tafiyar kusan 30minute kafin suka ƙaraso dai dai layin nasu, a bakin layin ya sauke ta ta shiga cikin layin. A gaban wani ɗan madaidaicin gida ta ja ta tsaya, nan naga ta fara knocking, ba a jima ba wata budurwa wanda nake tunanin baza ta wuce 19 years ba ta buɗe ƙofar.

“Salama alaikum”

“Wa alaikum salam ya Suhaila sannu da zuwa”

“Yauwa sannun ku da gida” ta faɗa tana ƙarasa shiga cikin gidan.

Dab ta zata shiga ƙofar palon na su ta ƙara yin wata sallamar, nan wata mata da nake tunanin ita ce mahaifiyar su ta amsa mata ba yabo ba fallasa, tana daga cikin ɗan madaidaicin kitchen ɗin nasu da yake cikin palon.

“Ammi, sannu da gida”.

“Yauwa Suhaila sannun ku da zuwa”.

Niqab ɗin fuskarta ta cire a nan ne kuma na samu damar ƙare mata kallo, black beauty ce, komai nata ɗan madaidaici, baza ka ce mata tana da muni ba, sannan kuma baza ka ce muguwar me kyau ba, ita dai dai moderate ce, amma fa akwai ta da farin ido ga kuma one side dimple da take da shi.

Ɗakin su ta wuce direct, tana shiga babu wani ɓata lokaci ta shige wanka, bayan ta fito ta saka kaya tana shirin ɗaukan hijab ɗin ta zata tayar da sallah, kira ya shigo wayar ta.Besty na gani a jikin screen ɗin wayar, babu wani ɓata lokaci tayi picking kiran.

“Salama alaikum’ how far Sury?

” Wa alaikumu salam, hmm not that too far na gode sosai, daga ki jirani mu gama magana da Abubakar shine kika taho kika barni a department ko?

“Surayya bana son complain , yanzu kina ina?

” Gani nan a gate yanzu zan hau napep, kuma da kika taho kika barni sai da na biya ta libarary nayi clearance ɗina, kinga gobe ke kaɗai zaki shiga school ki fafata”.

“Hmm naji ba komai”.

“Kafin na shiga gida plss zan biyo muyi magana”.

“Okay, Amma indai kin san maganar Abubakar za kiyi mun ma kar ki zo wallahi”.

“Hmm sai dai nazo ɗin”.

Bayan sun gama waya ta kabbara sallar azhar, tana idarwa ta yi azkar, kafin ta fita zuwa kitchen ko zata samu abunda zata temakawa Ammin nasu.

Amma tana shiga kitchen ɗin Ammi ta ce”Suhaila na riga da na gama komai ki barshi kawai, ganyen nan ne ya rage kuma shima yanzu zan zuba shi don har ma na wanke”.

Kallon Ammin nata tayi tana tunanin ko sai yaushe zata sakko oho, bata ƙara cewa komai ba ta fita a kitchen ɗin, idan da sabo ai ta saba da halin Ammin nasu, idan akayi faɗa da Abbun su to ranar akan su zata huce.

Fridge ta buɗe don ɗaukan ragowar grapes ɗin ta da ta ajiye jiya da daddare, amma ta ga wayam, nan da nan annurin fuskarta ya ɗauke, don idan akwai abunda Suhaila take so cikin kayan fruits to ya biyo bayan grapes, shiyasa kusan kullum idan Abbun su zai dawo sai ya siyo mata idan ma be siyo ba ita zata siya da kanta.

“Ke Fadila!, wa ya sha mun ragowar grapes ɗina tsakanin ke da Mubarak ummm?.

Fadila da take kan sofa ta guntse dariyar ta kafin tace” Aaaa ni, bani bace, Mubarak ne, na hannun daman naki yana can yana buga game a ɗakin shi”.

“Mubarak! “ta faɗa tana jin jina kai.

Bata tsaya ɓata lokaci ba ta nufi hanyar ɗakin na shi, ai kuwa tana shiga ta ganshi ya baje akan sofa, ga Uban Bluetooth ear piece ya kafa a kunne a gefe guda kuma he is busy playing his game.

Sai da ta ƙare mai kallo tsaf kafin ta hango robar grapes ɗin a gefan shi wanda be fi saura guda shida a ciki ba…

“Lallai ma yaron nan ya raina mun hankali”

Ganin in ta tsaya sallama ma ba jin ta zai ba yasa ta shiga cikin ɗakin direct.tana ƙarasawa ta tallaƙe mai ƙeya kafin ta zare ear piece ɗin.

“Sannu fa, ka zo ka kafa wannan abun a kunnen ka sannan kuma kana busy buga game, duk kai kaɗai ko. sannu sara, kai ka siya mun da za ka je har cikin fridge ka ɗakko mun abu na ka sha?

“Wayyo ya Suhaila wallahi da zafi, gashi kin sani na faɗi a game ɗina kuma wallahi saura kaɗan na gama level ɗin”.

“Wannan kuma kai ta shafa. bani amsar tambaya ta tukunna”.

Shafa ƙeyarshi yayi kafin yace”Wallahi yunwa ce ta koroni daga school, na dawo kuma Ammi bata gama girki ba.

“look at you, village boy kawai, ko uniform baka cire ba amma kazo ka ɗau game kana yi, am sure ko sallah baka yi ba Mubarak”.

“Wallahi ban yi ba, saboda yunwa, da cewa nayi idan naci abinci sai nayi sallar”.

Kunnen shi ta murɗai in a playful way kafin tace”Wallahi ka tashi idan ba haka ba ranka zai ɓaci, ai wannan buga game ɗin da kake yi ba wasting energy kake ba ko?

Ta ƙarashe maganar tana ɗaukar ragowar grapes ɗin, ta nufi hanyar barin ɗakin.

“Haba ya Suhaila ki barmun ragowar mana”.

“ƙwalelen ka bazan bar maka ba!

Ta bashi amsa wanda already ta kusa komawa cikin gidan.

” Haba mana zan tsam miki Apple ɗina nima fa yau da daddare! “. Ya faɗa ta window.

“Naƙi wayon, baka isa ba!

*****

Ɗaki ta koma ta janyo laptop ɗin ta, cikin wasu documents ta shiga wanda nake tunanin projects ɗin ta ne.

Editing nashi ta cigaba da yi tana yi tana shan raguwar grapes ɗin ta.

Bayan ta gama editing ɗin ta sha ruwan da ta ɗakko a fridge kafin ta shigo ɗakin, bata wani daɗe ba bacci ya ɗauke ta.

*****

Cikin bacci taji an ɗala mata duka a cinya, ai kuwa babu shiri ta tashi firgit daga baccin, tsaki ta ja don ta san babu me yi mata irin wannan wasan sai aminiyar ta ta.

“Haba Sury, meye hakan? Kawai ina bacci na me daɗi zaki zo ki tashe ni”.

“Come on dalla malama tashi, kasa kawai, ke dai da kin ɗan samu space sai ki kama barci mussaman ma yanzu kinji fanka”.

“To wallahi baki isa ba sai na rama”. Itama dukan ta ɗala mata a cinya kafin ta ƙara gyara zaman ta.

“Auchhh amma fa da zafi, don wanda na miki be kai wannan zafi ba, any way kin rama, one one, ba me bin wani bashi”.

” Shine kika taho kika barni ko?.

“A to kin tsaya kina kula wannan mutumin mai kai kamar naki ai dole na taho na barki da shi”.

“Hmmm naji dai ki faɗi duk abunda kike so ki faɗa, but please ki kula shi mana, ki gwada, ai sai an gwada a kan san na ƙwarai ko?

” Hmm kema kin san ɓata bakin ki kawai kike don ni kam bazan kula malam Habu ba”.

“Au harma suna kika canza mai”.

Ɗan yatsina fuska Suhaila tayi kafin ta ce”A’a ban canza mai suna ba, ai duk sunan shi ne”.

“To yanzu dai naji, let be serious, please ya kama ta ace zuwa yanzu kin samu mijin aure Suhaila ki dena ignoring maza don Allah”.

“Surayya kenan kin fi kowa sanin halin da nake ciki a gidan nan, kuma Abubukar ba sa’an Aure na bane, he is my course mate, yaushe muka gama service har ya samu aiki muka yi aure ummm, kuma bama wannan ba he is very arrogant, ni kuma bana son mutum me shegen girman kai, wanda mata suke bi, kuma kinga duk yana da wainnan qualities ɗin, so bazan iya ba gaskiya”.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button