AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 31-40

“Bari naje na kawo miki wasu kayana ki saka yanzu kiyi wanka duk da nasan kayan zasu miki yawa, amma ki canza na jikinkin nan” Aziza ta amsa da to na gode sosai, Sultana tana fita Aziza tayi shuru tana saƙa da warwara, zuwa can ta mike zata shiga bayi har ta manta da ciwon kafarta sai ji ta yi ta takesa, zafi taji ta saki kara sannan ta koma ta zauna tana fadin

“Ba zan iya jurewa ba” hannu tasa ta shafe wajan nan kafarta ya dawo dai-dai sannan ta shiga ta yi wanka kamar yadda Sultana ta nuna mata amma bata wanke kanta ba,tana fitowa Sultana na shigowa ta kalleta ta ce

“Ba ki wanke kanki ba? To ki bari karki wanke,idan kikaji sauki sosai sai muje a wanke miki, wannan gashin naki ai sai wajan masu salon, yanzu ga wa innan kayan ki fara lallabawa da shi Mom ta ce zata siyo miki wasu” godiya sosai Aziza tayi,ta dauki wani dogon abaya ta saka ya mata kyau duk da ya mata yawa tasa ta dau hijabi ta tada sallah,ta jima tana addua Allah ya bata mafita a kan wannan babban lamari nasu, kafin sultana ta shigo ta kirata ta fito taci abinci.

        ????????????????

*KUNTAU.*

wani hamshakin gate Azima ta tsaya tana kallon gate din, ganin tsaruwarsa da haduwarsa zuciyarta ne ya raya mata wannan gida taji gidan ya kwanta mata a rai,kuma dole uwar naki sai ta zauna a wannan gida ko ana ha maza ha mata, da wannan tunani ta yi gate din ta hau kwankwasawa.

       ????????????????

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button