AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 51-60

“Lahh Hamma Khalil marabalale” ta fada tana hawa sama da gudu ya yi murmushi ya ce.

“Kanwarmu kenan” ya nemi waje ya zauna, da gudu Aziza ta shiga dakin Sultana ta haye gadon ta janyeta, Sultana ta bude ido cikin haushi ta ce

“Dan Allah miye haka Aziza!?”

“Kai Anty Sultana kin san da cewa Hamma Khalil zai zo shine kike bacci har yanzu baki masa girki ba, ba kiyi wanka ba haba dan Allah” ai Sultana tana jin an ambaci sunan Khalil yazo ta miƙe zunbur, ta ce

“Ke Aziza da gaske Khalil yazo?”

“Wlh yazo yana parlourn kasa” da sauri Sultana ta miƙe da kayan bacci ta ɗiro a gadon ta fita ta shiga dakin Mom ta ce

“Mom wai Khalil yazo” 

“E na sani”

“Shine Mom ni ban sani ba, bai fa gaya min zaizo ba, ga shi ban shirya masa komai ba, ban yi wanka ba” Mom ta dauki mayafinta tana fadin

“Too idan kin gama mitan saiki haɗa masa komai ɗin sannan kiyi wanka” ta fice, fita itama Sultana ta yi, ta samu Aziza na kwashe kaya a parlourn sama,ta ce

“Aziza yanzu ya zanyi?”

“Karki damu Antyna,yanzu kedai kawai kije ki cakare wanka, zan kula da saura”

“Thats my lil’sis” Sultana ta fada tana shiga daki da sauri, kasa Aziza ta sauko ta shiga kitchen, a cikin mintuna qalilan ta jera tray ta haɗa abubuwa a kai na burgewa da ban sha’awa tazo ta ajiye a gaban Khalil wanda yake duƙe a gaban Mom suna magana, sun jima suna magana da Mom kafin Mom ta tashi ta koma sama, ba jimawa gimbiyar tasa ta sauko, nan aka hau hiran soyayya na yaushe gamo, sannan ta kara gabatar masa da Aziza.

         Kamar yadda Khalil ya fada bayan sati daya da dawowarsa aka zo aka tsaida ranar aurensa da Sultana wanda za ayi nan da wata daya da sati uku,wanda Nawaz shi da Khalil ɗinne suka yanke wannan shawara.

      Tunda aka saka wannan rana Khalil ya hana Sultana sakat, tayi-tayi ya bari suje kano amma ya ƙi, yace ta bari ba yanzu ba,ita da basu shiri da yan kano din ma, bayan sunyi haka da shi ta gayawa Aziza, Aziza ke tambayarta meyasa bata son kano, Sultana ta ce

“Ni da Hanan yadda kika san kamar wuta da auduga, sannan rashin kirki da mugunta irin na Maman Hanan da Maman Beenah abun ba a magana karki so ki yadda suke yiwa Yaya Almazeen, kuma shine mai kudin fa, gwara ma dai Beenah muna ɗan shiri amma banda Hanan, bana son halinsu ne sabida muzgunawa Yaya Al’mazeen da sukeyi”

“Mutane kam ai sai addua, Allah ya kyauta kawai” Sultana ta amsa da amin.

       ????????????????

Hadiza! Hadiza! Hadiza!.

Da gudu Hadiza ta fito ta zube a gaban Hajiya Lawiza Maman Hanan kenan, cikin yauki ta kalli Hadiza ta ce

“Hadiza, maza ki kirawo Azima ki haura da ita can sama part din Al’mazeen ta fara gani da tattare ƙura, suna nan dawowa nan da sati biyu”

      ????????????????

*BACCI NAKEJI WLH????????♀️????????♀️????????♀️????????????????♀️*

[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   ????????????????????

*PAID.*

????️=5️⃣7️⃣↪️5️⃣8️⃣

Damm! Gaban Azima ya buga tayi saurin ware blue eye dinta,  ta maimaita

“Azizaa! Aziza dai!?” Maman Beenah ne ta kallesa ta ce

“Al’mazeen kasanta ne dama? Sannan sunanta ba Aziza bane, wannan sunanta Azima ne” girgiza kai Al’mazeen ya hau yi yana ƙarewa Azima kallo,yatsar hannunta ya kalla yaga irin zoben da ya gani a hannun Aziza dazu, sannan ace kuma ba Aziza bane? Ko dai ya yi gamo ne? da sauri ya haura sama, yana shiga part dinsa ya ga sai kyalli yakeyi an gyara sosai bai tsaya karewa ɗakin kallo ba, wayarsa ya ɗaga zai kira Nawaz sai kuma ya fasa ya kira layin mom,ringing uku mom ta daga suka gaisa yace mata ya isa lafiya,mom tayi hamdala ta masa sannu da hanya ta kara da cewa

“Ya ka samu mutanen gidan,su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba?da kuma yaran?”

“Lafiyar su lau”

“Ya naji muryarka haka Al’mazeen? Kamar kana cikin tashin hankali ko damuwa, ba dai daga dawowarka suka fara cusa maka baƙin ciki ba?”

“A’a mom basu bane, amm nace ba mom? Aziza fa? Ya jikin nata?”

“Alhamdulillah da sauki, ko ba sauki musulmi ai ba zai ce babu ba sai dai yace alhamdulillah, Sultana tana tare da ita dik da naji tace tana da paper 12 zataje skull ga abokin naka ma shima baida lafiya, bayan tafiyarka da ya shigo idonsa a kumbure wai kansa ke ciwo”

“Subhanallahi! Allah ya basu lafiya, dama tunda na ga yanayinsa na san bai da lafiya dan ina kyautata zaton jiya bai yi bacci ba dan a parlor na samesa zaune da asuba, amma da na tambayesa yace min ba komai,zuwa 12 in sha Allah zan kirasa naji ya jikin nasa maybe yanzu yana bacci, bari na kira sultana naji ya na Aziza yake” nan ya yiwa Mom sallama yana katse wayar, sultana ya kira a lokacin tana magana da wata classmate ɗinta a waya,tana gaya mata ba zata samu zuwa skull ba, Brothern’ta da sistern’ta basu da lafiya, suna cikin magana ta ga wayar Al’mazeen ya shigo dan haka sukayi sallama da kawarta ta daga na  Al’mazeen, sai da ta masa an isa lafiya kafin yace mata 

“Ya jikin Aziza?” kuka ta sa tana kara masa wayar a saitin fuskar Aziza dake fidda huci tana gurnanin zazzabi,bayan ta kara masa wayar  yaji kafin ta maida wayar kunnenta tana ci gaba da kuka tana fadin

“Bro ka ji ta ko? Yadda ka barta haka take sai ma abunda ya ƙaru”

“Subhanallahi! Allah ya bata lafiya kin bata wa innan maganin kuwa?”

“E bai jima ba da na bata,amma kamar bai yi aiki ba”

“Karki damu kinji zai mata a hankali kiyi ta yi mata addua, Allah ya bata lafiya!”  daga haka ya katse wayar,ya hau jeka ka dawo a daki yana saƙa da warware, “AZIMAA!?” ya faɗa yana rike kai

“To ko dai yar uwar Aziza ce? Tunda sunansu mai haɗi iri ɗaya ne? Amma kuma Nawaz yace an kashewa Aziza kowa bata da kowa! To ba mamaki kamanni ne” daga haka ya miƙe ya shige toilet abunsa ya watsar da tunanin jin yana shirin saka masa ciwon kai.

        A kasa kuwa ba ƙaramin daru aka sha da Azima ba a kan abincin da za a kai wa Al’mazeen, ta dage ta kafe tace wlh ba zai ci wannan abincin ba, Maman Hanan ta ce

“E lallai kam Azima, wato kin samu waje kinyi freesh shiyasa zaki fara murza iskanci son ranki ko! To wlh ki bi a hankali” ba tare da Azima tayi magana ba ta karbi abinci a hannunsu Hadiza tayi wajan kitchen da shi ta ajiye ta hau yiwa Al’mazeen sabo, girki takeyi duk da ba wai ta wani iya sosai bane, amma da taji ance Al’mazeen zai dawo yasa kullum tana kitchen dasu Hadiza tana ganin yadda ake girkin barin ma wanda aka ce mata Al’mazeen ɗin ya fi so.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button