AZIZA DA AZIMA 51-60

Tana girki tana tunanin sunan da Al’mazeen ya kirata da shi,hakika hankalinta ya ɗan tashi
“Aziza! Aziza! Ina Al’mazeen ya san Aziza? Shi da baya ma kasar, to ba mamaki wajan kiran sunanta aka samu kuskure zai ce Azima yace Aziza” share zancan tayi ta ci gaba da aikinta dan ta san wan can sakaryan tana can jeji, sai bayan da ta kammala ta jera a tray ta dauka ta haura sama.
A hankali ta tura kofar ba tare da tayi sallama ba, Al’mazeen na zaune a parlour da system a gabansa da alama aiki yake yi, yaji mutum ya shigo ba sallama, haɗe rai ya yi, ita kuwa Azima sallama baya daya daga cikin dabiunta, abunda Al’mazeen ya tsana kenan, dan shi mutum ne mai girmama addininsa fiye da komai a rayuwarsa, Al’mazeen da na riƙo da addini fiye da tunanin mai tunani, murya can kasa yace
“Fita ki min sallama, karki sake ki min magana ba tare da kin min sallama ba” juyawan kuwa tayi ta fita ta sake shigowa tare da fadin
“Salamu alaikum” tana tura bakin, bakintan kawai yake iya hangowa yadda take tura shi tana murguɗa shi tunda fuskarta a rufe yake, abun dariya ya ba sa dan haka ya ɗan murmusa ba tare da ta gani ba, abincin ta ajiye tare da fadin
“Kayi hakuri” bata ma san sadda tace masa ya yi hakurin ba, jinjina kai Al’mazeen ya yi,ya ce
“Kece Azima?” ta gya ɗa kai,
“Daga ina kike?” damm! gabanta ya buga, amma da shike zuciyarta a tsaye yake ƙyam tace
“Daga can cikin kauyen kano a wata rugar fulani”
Al’mazeen a ransa ya ce
“E tabbas to basu da alaƙa da Aziza”
“Ina abincin da aka dafa min?” murguɗa baki Azima tayi tace
“Na ajiye musu a bayan kitchen idan sun ga dama su dauka su ci ko su san yadda zasuyi da shi” tana gama fadi ta mike fuuuu ta fice, girgiza kai Al’mazeen ya yi ya ci gaba da aikinsa, sai wajan sha daya da rabi ya ja tray din da ta ajiye masa ya buɗe yana kan buɗewa sai ga ta ta shigo ta duƙa tunowa da dazu ya koreta akan bata yi sallama ba sai ta kara ficewa da sauri ta shigo tana fadin
“Salamu alaikum! ai saika kirani nazo na zuba maka”
“Kina da waya ne?” girgiza kai Azima ta yi ta ce
“A’a bani da shi,amma idan kace AZIIIMAAAA!!????️Ai zanji na taho da sauri!” girgiza kai Al’mazeen ya yi ya tashi zai shiga daki, da sauri ta ce
” *HAMMA MAZEEN* abincin fa?”
Cak Al’mazeen ya tsaya yana nanata sunan “Hamma Mazeen!” kirjinsa ne ke bugawa da sauri-sauri,
“Ina zuwa ki zuba kawai ki tafi” ya faɗa yana shigewa bedroom, Azima haushin kanta ne ya kamata, wai meyasa take masa abu kamar wanda ake sakata ko ana bata umarni ne? Meyasa take jin faduwar gaba a kansa, meyasa take jin makarin gubarta yana tattare da shi? Amma kuma tana ji kamar ita da shi an jona musu kuran karfe, saurin tashi tayi ta fice.
????????????????????
Sai 1 Nawaz ya farka ya ɗan ji kan nasa da sauki amma kan ya yi masa nauyi, wanka ya yi a nan daki ya yi sallah, sannan ya lallaba a hankali ya shiga cikin gida, ba kowa a parlor dan haka ya fara haurawa sama, sai kuma ya juyo yana kallon kofar dakin Aziza, saukowa ya yi ya nufi dakinta, a hankali ya tura da sallama, mom da sultana ma ashe suna dakin, Aziza na jingine tana sallah a zaune a kan gado, saurin karasowa kusa da mom ya yi ya ce
“Mom jikin nata ya yi tsanani ne haka shine baku tasheni munje asibiti ba?”
“Humm! Nawaz kai ma fa ba lafiyar gareka ba, ka ganta nan jiya bata rintsa ba”
“Bari ta idar da sallar sai a kaita asibiti”
“A’a Nawaz ba sai anje asibiti ba, babu amfani, zaku ƙara huda mata jiki ne kawai, yanzu sai kuce zaku sossoka mata allura a ɗaura mata ruwa aja jini, wanda hakan kuma…!” sai Mom tayi shuru, a lokacin Aziza ta sallame sallarta, Nawaz ya miƙe yana fadin
“Mom dan ta gaya miki bata son allura sai a biye mata dan lafiyar wa akeyi? Ina dan lafiyarta ne!” ya faɗa cikin haɗa fuska, ya nufeta yana faɗi wa Sultana ta tashi taje ta cewa driver ya juya mota.
Aziza kuwa ganin ya nufota yasa ta kwalalo ido waje, dan kuwa jikinta yana fidda farin sab’ar maciji idan ya gani fa? Saurin girgiza masa kai ta hau yi muryarta a shaƙe da baya fitowa sosai ta hau fadin ya kyaleta kar yazo inda take, ko kaɗan bai tsaya ya saurareta ba yasa hannu ya yaye bargon jikinta ya kamo hannunta,ji yayi kamar wani fata ya maqale masa a hannunsa, sake hannun nata ya yi yana kallon tafin hannunsa, wani zare ido Nawaz ya yi sai kace idon zasu faɗo ƙasa,ganin sab’ar fatar maciji fari sol a hannunsa, Aziza kuwa banda kakkarwa babu abinda jikinta ke yi,tana sake boye hannunta a cikin hijabin dake jikinta tana jan bargo tana son rufe kafafunta, saurin fizgar bargon Nawaz yayi jikinsa na kyarma, yasa hannu ya figi hijabinta ganin haka yasa mom cewa da sauri
“Nawaz ka haukace ne!? baka da hankali ne!? mai kake shirin yi!?” ba tare da ya saurari mom ba ya ɗago Aziza tsaye wacce jiri ke kwasarta, hannunta ya riko ya ware nan kuwa ya ga jikinta duk b’awu, a lokacin kuma Aziza ta suma, dagota ya yi yana jijjigata cikin tashin hankali yana tambayarta wacece ita.
Cikin kuka Sultana tasa hannu ta kwace Aziza daga hannun Yayanta ta rungumeta ta ce
“Yaya ta suma fa? Dan Allah Mom kiyi wani abu a kai”
Nawaz yasa hannu zai kara jan Aziza daga jikin sultana, sultana tayi saurin juyawa da ita ta kwantar da ita tana murza tafin hannunta tana kuka
“Zan fa karyaki Sultana ina wasa dake ne!!?”
“Wlh Yaya ko kasheni zakayi ba zan bari ka kasheta ba, dan Allah mom kiyi magana ki gaya masa gaskiya,babu amfanin wannan boye-boyen”
“Nawaz ya isa haka! Aziza Macijiya ce!” Mom ta faɗa a tsawace,
Nawaz ne ya yi baya-baya yayi zaman yan bori sharab, mom ta karaso ta kama hannunsa.
kenan mafarkinsa akan yarinyar macijiya ce gaskiya ne? Kallon Mom ya yi da jan ido ya ce
“Mom da macijiya muke rayuwa kuma ke ma kin sani? Taya hankali zai dauka ace mutum maciji? Da ace sultana ce ta faɗa ba abunda zai hanani ban kaita asibiti an duba min kwakwalwarta ba”
Ajiyar zuciya mom tayi tace
“Zaka iya tsayawa ka saurareni uhum? Nawaz magana nake maka” kifa kansa ya yi a kafadar Mom hawaye suka hau gangaro masa wanda bai san dalili ba.
“Nawaz labarin Azima da Aziza da baffansu da kauyensu abun tausayi ne mai cike da zallar al’ajabi” cikin taushin murya Mom ta hau zayyanawa Nawaz labarin Aziza bata boye masa komai ba kamar yadda Aziza ta ba su haka ta bai wa Nawaz, mom tana gama ba shi labarin ya dago yana fadin
“Wlh mom yawancin abun da kika faɗa min ina ganinsa a mafarkina, tun ranar da na bugeta a mota na kawota kaduna tun daga ranar na daina bacci kirki,mom ina yawan ganinta a siffar macijiya tana kuka tana neman taimakona!” jinjina kai Mom tayi ta ce
“Ba mu san me Ubangiji ya boye tsakaninka da Aziza ba Nawaz, amma inaso muyi wani jahadi wana Allah ya zama silar shigarmu aljanna, Nawaz har zuciyata ina jin Aziza,yarinya ce mai hankali da natsuwa da sanin ya kamata duk da tana da kananun shekaru amma tana da hankalin manya da imani da kaddara ga tawakkali da miƙa wuya,kuma dama abunda akeso kenan ga musulmi mumini ko mumina, Nawaz sultana zata bar gidan nan kwanan nan, dan Allah ina so kayi jahadi ka *AURI AZIZA!!*” dummm!! gaban Nawaz ya bada ya kalli Mom da sauri, Mom ta gya ɗa kai tana fadin
“Tun kana yaro ban taba cewa ina neman alfarma ka kasa min ba, ina so ka taimaka ka auri Aziza, ka zamo silar warkewarta, duk wanda ya zama silar farin cikin mutum daya Allah zai zama silar farincikinsa a ranar da babu wani mai gata sai fiyayyen halitta, Nawaz kana da ilmi duk abunda zan gaya maka ka sani sai dai na kara yi maka tuni, idan ka auri Aziza ka zamo silar warkewarta hakika zaka saka mutane dayawa ne farinciki, zaka fidda UWA da UBA daga ƙunci, da sauran yan uwansu, wlh har zuciyata na aminta” kallo fuskar Aziza Nawaz ya yi, hakika daga fuskarta zaka san cewa tana jin jiki