AZIZA DA AZIMA 51-60

“NA AMINCE MOM! ZAN AURETA!” da sauri Sultana tazo ta duƙa ta rungumesa cikin murna, “da gaske yaya zaka aureta!? Wayyo dadi wlh nayi farinciki”
“Allah ya maka albarka Nawaz” cewar mom tana shafa kansa.
Nan suka zauna a dakin har sai da aka yi sallar la’asar kafin suka fita da niyyar sallah, nawaz msallaci yaje, bayan sun idar ya jima yana kwararo adduoi a kan wannan lamari da yake gani tamkar a mafarkin da ya saba ne.
Bayan ya dawo part dinsa ya wuce, ya dauki wayarsa ya ga miss calls din amininsa,kiransa ya yi ya daga yana tambayarsa ya jikinsa,Nawaz ya amsa da sauki shima yana masa ya gajiyar hanya, Al’mazeen ya amsa da alhamdulillah ya kara da fadin ya jikin Aziza, alhamdulillah Nawaz ya fada, sun ɗan jima suna magana inda Nawaz yake ji ko ya gayawa Al’mazeen? Daga baya kuma ya fasa har suka gama wayar sukayi sallama.
Sai wajan shidda Aziza ta farka sultana ta taimaka mata tayi alwala tayi sallah a zaune kamar dazu, bayan ta idar tayi addua sultana ke gaya mata sadda ta suma mom ta gayawa Yaya Nawaz komai, a lokacin da sultana ke gayawa Aziza Nawaz sun shigo shi da mom, kuka Aziza ta saka tana fadin
“Shikenan zai koreni! Dan Allah Anty Sultana ki ba shi hakuri kar ya koreni, wlh da na samu Azima zan tafi da kaina,tafiya na har abada ba zai sake ganina ba in sha Allah” rasss! gaban Nawaz ya buga jin tace zata tafi na har abada, a hankali Nawaz ya juya ya fita ganin yadda take kukan duk sai yaji babu dadi yana danasanin abunda ya mata, tayi mugun karya masa zuciya.
Mom tace
“Injiwa yace zai koreki a gidan nan? Bana so na ƙara ji kince zaki bar gidan nan na har abada, dan kuwa kina nan a gidan nan har abada In sha Allah,kinji ko?” Aziza ta gya ɗa kai tana kuka.
@@@@@@@@
Da washe gari tana kwance tana fama da kanta,bata san ta yadda zata samu furen huriri ba, da ace ta samu da tuni an wuce wajan, turo kofar akayi da sallama, jin muryan mai sallaman yasa gaban Aziza bugawa, murya na rawa ta amsa, karasowa yayi a hankali ta dago idonta ta kallesa a tsorace, ta gansa da plate a hannu, mamaki ne ya kamata, zama yayi a gefen bedside’drower fuskar yau da sassauci, murya a can kasa ya ce
“Ya jikin naki?”
“Alhamdulillah, ina kwana?”
“Tashi kici abinci ki sha wannan rubutun, wani babban aminin Daddyna ne malami ne wajansa naje jiya da daddare na masa bayani a kan matsalarki, yace na baki wannan zakiji dama-dama duk da ba lallai bane ya dauke miki abunda kike ji gabadaya ba, amma zaki samu karfin jiki” mamaki ne ya ƙara kamata, amma bata da lokacin tsayawa mamakin, a hankali ya dagata ya jinginata da pillow, ya dau spoon ya ɗibi abincin ya kai mata shi saitin bakinta, tsananin mamaki ya hana Aziza buɗe baki taci dan ji take kamar mafarki takeyi, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Nawaz furta kalman
“I’m sorry Aziza” a sanyaye, sake yin ƙasa da kanta Aziza tayi gabanta na ci gaba da bugawa, muryarsa taji yana kara fadin
“Na sani, na cusa miki tsorona a zuciyarki, am sorry once again” kuka ta fashewa da shi, ya ɗan rintse ido ya ce
“Kamar na gaya miki bana son kuka ko?” ta gya ɗa kai
“To meyasa kikeyi?”
“Na…ba…ri” ta fada murya na rawa,
“To kici abincin” ya fada yana bata a baki cike da tausayinta, bata wani ci sosai ba ta ce masa ta koshi, cup ya dauka ya tsiyaya mata rubutun ya bata tasha tana sha taji kanta na wani mugun juyawa, ba jimawa ta zube ta hau bacci, ganin tayi bacci yasaka shi tashi ya fita,a parlour ya samu Mom da sultana, zama ya yi kusa da mom, ta ce
“Allah ya maka albarka Nawaz, Allah ya faranta maka duniya da lahira” a tare suka amsa da amin shi da sultana.
Ko da ta farka taji jikin nata da dama-dama,dan kuwa ta miƙe da kafafunta har tana iya tafiya, jirin ne dai bai daina dibarta ba.
????????????????????????
Bayan kwana biyu taji sauki alhamdulillah amma lokaci zuwa lokaci jiri na zubar da ita, tsakaninta da Nawaz kuma yanzu babu tsangwama, sai tausayawa, har mamakinsa take yi,ita dai ba zata gushe ba tana yiwa su mom addua.
????????????????????
Bayan sati daya da dawowar Al’mazeen kano komai ya canza a gidan, Azima ke zuba mulki son ranta, ga shi yanzu tana kwatowa Al’mazeen yancinsa a cikin gidan, duk wani guba da maganin mallaka idan aka zuba masa a cikin abinci sai dai azo a samu Azima ta juyewa karnuka abincin, su Hajiya Lawiza da Hajiya Luba sun rasa yadda zasuyi da Azima, ta bangaren Al’mazeen kuwa a sati ɗayan nan kacal ya shaƙu matuƙa da Azima dan har zuciyarsa yake jinta, shi mutum ne mai son kulawa da soyayya amma bai samu ba, sai ga shi rana tsaka ya samu a wajan mai aiki dan ba karamin kulawa da shi Azima ke yi ba.
Kamar yadda Azima bata son dogon magana haka ma al’mazeen, amma su kan zauna suyi hira, inda take gaya masa ai itama bata da kowa duk an kashesu, idan Azima na magana ya kan ji muryan Aziza, duk da ba wai ya taba ganin fuskokinsu sosai bane, dan itama Azima duk shaƙuwan nan bata buɗe fuskarta, bayan dawowarsa da kwana uku taso guduwa ta bar gidan amma haka ta kasa har ya kai sati daya,inda takeji kafafunta sunki amincewa da barin gidan.
Yau ma kamar kullum ya shirya zai tafi asibiti, yana kan saukowa kasa har ya zo step din karshe sai ga Hanan, tana ganinsa sarai ta bangajesa briefcase dinsa ta faɗi, amadadin ta tsaya ta ba shi hakuri sai tana shirin rab’awa ta gefensa ta wuce, Al’mazeen cikin haushi ya ce
“Kee Hanan! Baki ga abunda kika min bane! Zo ki dau jakata ki bani”
“Wlh Al’mazeen sauri nake yi inaso naje na gwada wannan memoryn ne” ta faɗa tana shirin hawa sama taji an wani fizgota ta baya, ta ma zata Al’mazeen ɗin ne amma tana juyowa ta ga Hajja Azima wacce yau tayi shigan riga da wando idonta sanye da wani black shadow, Al’mazeen ne ya siyo mata jiya kasancewar itama ta masa karya da cewa ai idonta na ciwo.
fuskarta a haɗe da ka ganta sai tayi maka kama da irin bosawan film din indian nan, ashar Hanan tayi ta kalli Azima sama da kasa tace
“Wato na kauye ya shigo gari ko?”
“Ki duƙa ki ɗau jakarsa ki basa sannan ki ba shi hakuri” Azima ta faɗa cikin murya mai nuna umarni take badawa ba shawara ba.
“Lalala! Wlh ni ba irinsu Hajjaju bane, da zaki dinga yab’a musu magana kina juyasu kina basu umarni kina gasasu! Wlh ni karyaki zanyi! dan ni bana son raini!”
Hannunta Azima ta kama ta murɗe Hanan tasa ihu, Azima ta cije baki tace
“Kinga ni nayi miki kama da wacce take son raini? Tun kafin ki san wacece asalin Azima dau jakarsa ki ba shi sannan ki ba shi hakuri!”
Maman Hanan da Maman Beenah da beenah da Hanif ne suka sauko jin ihun Hanan.
Nan suka ga Azima murɗe da hannun Hanan Al’mazeen na cewa da Azima a kan ta saki hannun Hanan, ita kuwa tace ba zata sake ba, sai Hanan tayi abinda ta sakata,jin wuya yasa hanan cewa zata yi yadda Azima tace, sakinta Azima ta yi ta duka ta dau jakar ta ba shi ta ce
“Kayi hakuri”
“Kayi hakuri wa?” Azima ta faɗa a tsawa ce.
“Kayi hakuri Al’ma….” dauketa da mari Azima tayi har saida Hanan ta kai kasa,Azima tace
“Hamma! Daga yau idan na cire su Hajiya duk gabadaya Hamma Mazeen zaku na ce masa tunda ya girmeku, maza gaya masa!”
“Kayi hakuri Hamma Mazeen” Hanan na faɗi ta hau sama da gudu, Maman Hanan da Maman Beenah da Beenah suka bi bayanta, Al’mazeen ya haɗa rai yace