AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 51-60

“Ina bakijin maganata? Ina cewa ki saketa amma kinki ko?” turo baki tayi tace

“Ba komai nake yi daukawa ba,kuma ma ai sabida kai nayi” tana gama fadi ta fice tana tura baki ta bar shi tsaye, murmushi Almazeen yayi ya fice ya tafi office.

       Ko a office din ya kasa aikin kirki tunanin Azima kawai yakeyi, wayarsa ce tayi kara yana dubawa ya ga Alisha,guntun tsaki yaja,yau kusan sati tin dawowarsa kano take kira baya dagawa.

       @@@@

“Yanzu me zamuyi wa wannan yarinyar dan tana son fin karfinmu?” cewar Maman Hanan, Maman Beena ta ce

“Shegiyar taga kudi duk yadda akayi sonsa takeyi”

“Abunda za ayi muyi mata sharrin sata na san shi da kansa zai koreta, dama yau su Summy da Sady zasu zo ko?”

“E sunce ma sun kusa isowa”.

    (Summy da Sady, kannan Hajiya Lawiza da Hajiya luba, wanda suke so su aurawa Al’mazeen).

      ????????????????

MOMYN AHLAN✍????

[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   ????????????????????

*PAID.*

????️=5️⃣5️⃣↪️5️⃣6️⃣

Da kyar ya tattaro jarumta jin yadda kafafunsa suka yi sanyi ya shiga parlourn, ya samu Al’mazeen zaune yana cin abinci, zama shi ma ya yi Sultana ta zuba masa ta tura masa gabansa, amma tunani yasa ma yaji abincin ya fita kansa, Aziza kuwa tin sadda ta ba wa driver sako ta maqale ta kasa shiga gidan ganin yayi babakere a bakin kofa, sai da ya shiga ta siɗaɗo a hankali ta shige dakinta da gudu,tana shiga ta zube a gado ta saki kuka, ba jimawa Sultana ta shigo ta sameta tana kuka ta ce

“Subhanallahi! Aziza lafiya me ya faru?”

Cikin kuka ta dago ta ce

“Anty Sulty Hamma Nawaz ya ga idona”

“Mtswww! To sai me dan ya ga idonki?”

“Wlh tsoro nakeji kar ya koreni, dan naga yana mini kallon tuhuma kamar yasan wani abu a kaina”

“Kinga Aziza dan Allah ki kwantar da hankalinki ki samu natsuwa kinji? Babu abinda zai faru,na san me zanyi, kuma ma ai idan ya san wani abu a kanki ai ya rage mana aiki, balle ina ma zai sani? daga wajena sai wajan Mom,kuma Mom da kanta ta kwabeni tace kar na gaya masa ta san ta yadda zata gaya masa,na tabbata mom bata gaya masa ba,dan da ta gaya masa zata gaya min, dan haka ki dai na damun kanki” rarrashinta Sultana ta yi har ta samu tayi shuru, kafin suka koma hiran karatu.

        Da kyar Nawaz ya yi cokali uku a abincin ya tashi, Al’mazeen ya ce

“Dude ka ce yunwa kakeji amma ka kasa cin abinci i hope dai komai lafiya?” 

“E lafiya,ina zuwa” ya fada yana ficewa, part dinsa ya koma ya kwanta a dogon kujera, hakika idonta babu bambanci da wanda yake gani a mafarkinsa, wai wacece wannan yarinyar nan ne kam? Ya zama dole ya tambayeta ita wacece sannan miye haɗinsa da ita,idan ma mayya ce to wlh shi namansa da ɗaci,kuma sai ya danna mata kashedi ta fita rayuwarsa ya huta, ya kara jan tsaki.

      Bayan Al’mazeen ya gama cin abinci ya koma part din Nawaz ya samesa yana kwance a dogon kujera,zama ya yi a 1siter yana fuskantar Nawaz ya ce

“Dr lafiya kuwa?”

“Nml, kawai kaina ke ɗan min ciwo”

“Ayya sorry, to ka sha magani mana”

“No ba yanzu ba, bari na gani zuwa dare idan banji dai-dai ba zan yiwa kaina allura ko kuma ka min”

“Ok, Allah yakara sauki”

“Amin” Nawaz ya fada yana lumshe ido, wayar Al’mazeen ne ya sake ƙara, Nawaz ya bude ido yana jan dogon tsaki

“Mtswwwwww!!! Wannan mayyar ce ko!?”

“Meyasa kake ce mata mayya bayan kasan ita zan aura?”

“Wlh Allah ya sawwake maka da aurar wannan kakar taka, duk da nasan bana son yarinya karama amma ina zaka kai Alisha? ni fa wlh na rasa meke damunka, duk matan duniya ka rasa wacce zaka zab’a ka aura sai Alisha? Ga uban saka gashin doki a kai, ga ƙarin farce, ga saka gashin ido, ga rashin kunyar taunar cingam, gabakidayanta ma wlh zube take da karuwai! Dan Allah ka bar batun auren Alisha!”

     “Haba dan Allah Nawaz ya isheka haka mana! Kai kullum baka da aiki sai kushe Alisha? A tsammaninka dadi nakeji idan kana kusheta? Shuru fa kawai nake yi” Al’mazeen ya faɗa ransa a haɗe, Nawaz ya yi tsaki ya ce

“Aikin banza! Abunda kai ma ba sonta kake yi ba, dan an kusheta miye naka na jin haushi,wlh da ace kana son Alisha yadda nake kusheta da mun jima da rabuwa da kai”  girgiza kai Al’mazeen ya yi ya ce

“Mace ba zata rabamu da kai ba Nawaz, idan na rabu da kai waye zai dinga supporting dina? Plss karka kara fadin haka, abunda yasa nake son auren Alisha ita tana sona sosai,kuma ina sa ran zata bani kulawar da na rasa da soyayyar da ban samu ba” ya karasa fadin idonsa na canza kala,ganin haka yasa Nawaz matsowa kusa da shi ya zauna a hannu kujera ya riƙo kafadarsa yace

“Karka fadi haka, In sha Allah Aminina ya kusa fara dariya, ka tsaya kuma ka gani,mahakurci mawadaci, na fadi dai-dai?” Nawaz ya fada yana murmushi tare da miƙawa Al’mazeen hannu, shima Almazeen murmushin ya yi yana haɗa hannunsa da na Nawaz sannan suka rungume juna.

      Yau wuni zunbur Aziza ta yi a daki ta ki fitowa, bayan sallar isha’i gabadaya suna zaune a parlour suna hira, Aziza kuma na daki tana rike da book amma a zahiri ba karatun take yi ba,tunani takeyi na yadda idan mom ta gayawa Nawaz cewa ita macijiya ce ya zai dauki lamarin, tayi nisa sosai a tunani taji an turo kofar da sallama, amsawa tayi tana ɗaga idonta ta sauke a kan Mom, Mom ta ce

“Lafiya kuwa yau kika wuni a daki Aziza? Ko wani abu na damunki shine kika kasa gaya min?” murmushin yaƙe Aziza ta yi ta ce

“A’a Mom, yau din ne dai nake ɗan jin zazzabi amma ba sosai bane”

“Subhanallahi! Ai saiki faɗi ba wai ki zauna shuru a daki ba, gamu da likitoci har biyu a gida, bari nayi wa Nawaz magana ya zo ya dubaki, ko allura ya miki” zare ido Aziza ta yi sai kuma ta koma ta hau narai-narai da fuska, Mom ta ce

“Ai ba zaki zauna da ciwo ba” Mom ta fita tana ambatar sunan Nawaz, wanda suke lissafin bikin sultana shi da Almazeen

“Na’am Mom” Nawaz ya amsa yana maida hankalinsa ga mom

“Nawaz dan Allah zo ka duba Aziza kayi mata allura, ashe bata jin dadi ne shiyasa ta wuni yau a daki” Sultana ta ce

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button