AZIZA DA AZIMA 51-60

“Ya Salam! Aziza akwai zurfin ciki wlh,nan fa dazu babu kalar tambayarta da banyi ba amma tace min babu komai, dan Allah Bro Nawaz muje ka dubata”
“To ba ga Al’Mazeen ba” Nawaz ya fada yana shagwabe fuska yana kallon Mom, mom ta ce
“E ai naga Al’mazeen din nace kai kaje ka dubata, idan kuma ba zaka dubata ba sai ka gaya min na cewa Son yaje ya duba min ita” Nawaz ya miƙe yana fadin
“Yaushe na isa, yi hakuri Mom luv ɗina, yanzu kuwa zan dubata, Sultana je ki dauko min box ɗina” Sultana ta amsa da to ta fice da gudu, shi kuma ya yi hanyar dakin,yana zuwa ya tura kofar ya sameta kwance ta zubar da gashinta a kan pillow, a ransa ya ce
“Wai idan wannan gashinta ne ma sha Allah” sai da ya yi gyaran murya kafin ya yi sallama, da sauri Aziza ta mike tana jan hularta dan ta rufe kanta, tana saka hular wanda bai rufe mata gashi ba sauran ya kwanta a kafaɗunta, ta dukar da kai jikinta na rawa, kallonta Nawaz ke yi yana yaba kyawunta a zuciyarsa sai furta ma sha Allah yake yi, har Sultana ta shigo dakin tana masa magana amma bai ji ba, sai da ta tabosa kafin ya juyo, dariya Sultana ta hau maqalewa tana miƙa masa box din, ganin haka ya dalla mata harara ba shiri ta hadiye dariyarta, murya can ciki yace
“Me kike ji a jikinki?”
Murya na rawa Aziza ta ce
“Amm…..uhum……zazzabi ne sama-sama”
“Kinci abinci?”
“E naci”
“Tun yaushe?”
“Tun karfe biyu”
“Na rana?”
“E”
“Baki da hankali ne! Taya zaki zauna da yunwa bayan baki da lafiya! Ko baki san shima wani babban ciwon bane! Sultana je ki kawo mata abinci yanzun nan taci a gabana, na duba na gani allura zan mata ko magani zan bata” jin ya kira sunan allura yasa Aziza ta ɗago, nan hawaye suka b’alle kamar an buɗe pampo, cikin fuskar tausayi ta ce
“Dan Allah Hamma Nawaz zan sha magani amma banda allura,bana son allura” ta hau masa magiya tana kallonsa amma shi idonsa a kwayar idonta yake yana kalla bugun zuciyarsa yana kara tsananta, da kyar ya dauke idonsa a kanta ya juya baya, sultana ce ta shigo da plate da abinci da ruwa ta mikawa Aziza dake kuka wiwi, Nawaz ya ce
“Na fa tsani kuka, kici abincin nan idan baki son allura,bana son shirme, idan kuma baki ci ba alluran zan miki” jin haka yasa Aziza fara ɗurawa cikinta abinci, sai da taci rabi ta kalli Sultana da tayi shuru kamar bata wajen, ta ce
“Anty sulty na koshi, Hamma Nawaz bani maganin” kallon Sultana yayi babu alamun wasa ya ce
“Karba plate ɗin ki fita da shi” karba sultana ta yi ta fita,sultana na fita ya hau jan ruwan allura ganin haka yasa Aziza fashewa da kuka tana ba shi hakuri kar ya mata allura, bata so ko kaɗan karfe ya huɗa jikinta kasancewar tana da jikin maciji hakan zai iya mata illa dan karfe ne zai huɗa jikinta,maciji kuma baya son tab’o, ko kaɗan Nawaz bai damu da kukanta ba duk da yanaji har can kasar zuciyarsa, ya rasa meyasa yake jin tausayin yarinyar, bai so ko kaɗan yana mafarkinta a mugun yanayi, bayan ya saita alluran ya nufeta, da sauri Aziza ta miƙe ta diro a gadon ta hau ja da baya, ihu ta saka zata gudu yasa hannu ya jata, Mom da Sultana da Almazeen da suke parlour suka jiyo ihun Aziza da sauri suka tashi suka yo dakin da gudu, suna shigowa suka samu Aziza da Nawaz sai zagaye daki suke yi, Mom tace
“Miye haka me zan gani?” ganin Mom yasa Aziza rugawa da gudu ta buya bayan mom, tsaki Nawaz yayi yasa hannu ya jata a bayan Mom yana fadin
“Mom ai kinga irinta, bana son hidiman yarinta wlh,allura fa zan mata amma kalli yadda ta sakani zagaye daki sai kace wacce zan zare ranta!”
“Haba Nawaz! Miye haka sai kace ba likita ba, ka lallabata mana ka bita a hankali, Aziza ki tsaya kinji? idan ya miki zakiji sauki, kinga yau kin wuni a daki ga jikinki da zafi, bana son ina ganinki a haka kinji?” girgiza kai Aziza ke yi tana fadin
“Mom zai min illa!”
“To dan Allah fa kiji mom, wai zai mata illa, taya allura zai miki illa ana shirin nema miki lafiya” yana faɗi ya haɗata da jikinsa ya matseta,a karfinta na nml mutane ta kasa kwace kanta, sadakarwa tayi, jin ya matseta ya danna mata allura yasa ta ƙanƙameshi tana kara sa kuka, allura biyu ya mata kafin ya saketa ya fita a dakin, Al’mazeen wanda ya ƙura mata ido yana kallonta ya fita ya bar su Mom da sultana suna rarrashinta, cikin kuka ta ce
“Mom allura karfe ne,kuma jikina na maciji ne, zai min illa” a tare mom da sultana suka zaro ido,mom tace “Aziza meyasa baki gaya mana da wuri ba? Subhanallah! Yanzu me zai faru?” girgiza kai Aziza tayi jiri na dibarta ta zube a jikin mom abun tausayi, hawaye Mom ta goge tace
“Ya Allah, kasa abunda yake zuciyata wanda nake shirin haɗawa ya zama alkairi, Allah kasa ya zama jahadi dani da iyalaina, ya zama silar shiganmu aljanna!”
“Me kike shirin yi Mom?”
“Inaso na saka Yayanki Ya Auri Aziza!” jinjina kai Sultana tayi ta ce
“Mom nima na jima da fara wannan tunanin, dan babu wanda zai auresu yayi wannan jahadin idan ba wani ikon Allah ba,mom ya kamata ki gayawa Yaya tun daga yanzu, sannan dan Allah mom a daga bikina zuwa shekara mai zuwa” wani harara mom ta gallawa Sultana sannan tace
“To je ki gayawa Nawaz” shuru Sultana tayi dan ko giyar wake take sha ba zata gayawa Yayanta Nawaz a daga bikin ba, yanzu sai ya daki banza.
Aziza zazzabi da kaɗan-kaɗan ya fara rufeta, ga shi abunda take so babu shi a cikin gari, furen huriri shine zata jiƙa ko ta tauna ganyensa shi kadai ne zai dawo da ita hayyacinta,amma ina zata samu?” haka ta dinga b’ari.
@@@@@@@
A daren yadda Aziza bata rintsa ba,haka ma Nawaz, wanda da ya rufe ido ita yake gani sadda take kuka tana cewa kar ya mata allura, tausayinta ne ya rufe masa zuciya, tashi ya yi ya kalli Almazeen dake bacci, parlor ya fito ya zauna ya riƙe kansa, ji yake kamar yasa kuka, ko yaje ya ganta ko zaiji sauki a ransa, abunda ya shafe wata uku yanaji a ransa bayaso ya tabbata, baya so zuciyarsa ace ta kamu da son wannan jaririyar yarinyar, sannan meyasa yake mafarkinta tun daga ranar da ta shigo rayuwarsa, meyasa yake ganinta a siffar macijiya? Saurin tashi tsaye ya yi, tare da naushin iska, a fili yace
“Kamata ya yi ace na tsaneki, dan kin takurawa rayuwata da yawa! Tsawon dare bana bacci duk sabida dake! Why! Why! Why Azizaaa!!” ya faɗa yana rike kansa da yakeji kamar zai rabe gida biyu, anan ya zauna har asuba, bayan Almazeen ya farka ya shiga bathroom yayi alwala ya fito parlor nan ya ga Nawaz yashe a parlor, kallonsa ya yi ba tare da ya yi magana ba yace
“Nawaz kayi alwala kazo muje sallah” Almazeen na fadi ya fice, shima Nawaz din alwala ya yi ya bi bayan almazeen bayan sun dawo daga masallaci, Al’mazeen ya hau shiri, yana shiri yana tambayar meke damun Nawaz, Nawaz yace masa ba komai, bai takura ba ya kammala shirinsa, takwas ya shiga ya yiwa mom sallama, mom tace dan Allah kafin ya wuce ya shiga ya duba Aziza ya bata magani dan jiya bata rintsa ba jikin ya yi tsanani,da to Al’mazeen ya amsa.
Aziza kwance sai b’ari takeyi jikinta mugun zafi, hannunta Almazeen ya kama ya ga wani zobe a hannunta a ƙaramin yatsarta na karshe, bai damu ba, ya gama dubata ya ajiye mata magunguna sannan yamusu sallama ya tafi.
Har wajen mota Nawaz ya raka amininsa tare fadin sai sunyi waya Allah ya tsare, sai da Al’mazeen suka fice kafin Nawaz ya shiga ya gaida mom idonsa a kumbure shima dan baiyi bacci ba ga kansa dake ciwo,cikin kulawa mom ta ce