AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 51-60

“Nawaz lafiya kuwa?”

“Mom kaina ke ciwo jiya banyi bacci ba” 

“Subhanallah! Sannu Allah ya baka lafiya, ka sha magani ka kwanta”

“To Mom” ya faɗa yana tashi, yana so ya tambayeta Aziza amma yakasa,dan haka ya koma part dinsa ya sha magani ya kwanta.

    bayan ya fice wayar Mom ya dauki ruri, tana dubawa ta ga malamin da tasa ya mata istihara a kan Nawaz da Aziza, da sauri ta daga suka gaisa cikin girmamawa,nan ya shaida mata akwai alkairi mai girma da yardan Allah tsakanin Nawaz da Aziza, shi gwargwadon abunda ya gani kenan, godiya sosai mom ta masa nan ta kara jin karfin guiwa.

      Dakin Aziza taje ta samu jikin nata ya kara tsanani, sultana idonta ya zazzago tsananin tashin hankali, Sultana tace

“Mom a gayawa Yaya ko akwai maganin da zai bata, kar ta mutu”

“Sultana shima baya da lafiya idonsa a kumbure da kyar yake budewa shiyasa ban gaya masa na Azizan ba,mu bari nasa ya sauka tukunna” Sultana ta ce

“Mom,anya kaddaran Yaya ba a haɗe yake da na Aziza ba kuwa?” shuru Mom tayi, sai zuwa can tace

“Allah ka bayyana mana Azima cikin sauki Ya Allah, Allah ka jinkirtawa wannan baiwa taka Aziza,duk da tana karama da kananun shekaru amma tana da hakuri da tawakkali da juriya” hawaye Sultana ta goge ta fice a dakin, khalil ta kira a waya tana kuka tana roƙonsa a kan a daga bikin nan kar ayi nan da wata daya, dalili ya fara tambayarta amma ta kasa gaya masa,inda a karshe ya katse wayarsa dan ya kasa gane me Sultana take nufi ko dai ta daina sonsa ne?.

       ????????????????

Yau fa Azima murna tun daga baka har kunne, Al’mazeen na hanya, bayan su Hadiza sun gama shirya masa abinci ita kuma ta gyara masa part dinsa tas, ta zo shiga cikin kitchen ta hangi Maman Hanan akan abincin Al’mazeen tana barbaɗa masa magani, girgiza kai Azima tayi, ta bar wajan ba tare da maman hanan ta ganta ba,amma tayi alkawari ba zata bari al’mazeen yaci abincin nan ba.

 

        Goma da rabi motar Al’mazeen ta yi parking a harabar parker motoci, ya jima a motar yana sauke ajiyar zuciya kafin ya fito, nan ma aikatan gidan suka hau masa sannu da dawowa tare da gaya masa sunyi kewarsa, cikin parlour ya wuce nan Maman Hanan da Maman Beenah suka hau murna suna masa oyoyo, a hankali ya russuna ya basu girmansu ya gaishesu sannan ya fara haurawa samansa, Maman Hanan ta ce

“Fuskar mutum kamar fura a dame kullum, Hadiza! Zo ku kai masa abincinsa sama”

       “Ba zai ci wannan abincin ba, wani zan dafa masa!” saurin juyowa Maman Hanan da Maman Beenah sukayi suna kallon Azima da kanta ke duƙe da lullubi, cak Al’mazeen da zai hau sama yaja ya tsaya jin kamar ya san mai irin muryar, Maman Hanan ta ce

“Sabida me ba zai ci ba?”

“Sabida bana da bukatar yaci, a bai wa wasu su ci,ko a ajiyewa su Hanif su ci idan sun dawo!” a daqile Azima ke magana, da sauri Al’mazeen ya dawo da baya,nan kuwa ya ganta sanye da bakin abaya itama fuska a lullube, yatsar hannunta ya kalla ya ce

“AZIZAAAA!?” a mamakin ce.

         ????????????????

*PAID.*

????️=5️⃣9️⃣↪️6️⃣0️⃣

“To yanzu miye mafita? Wani sharrin satan zamuyi mata?” cewar Maman Hanan, Maman Beenah ta ce

“Yanzu ke Maman Hanan idan kikace ta sace miki abu za ace dan ta murɗewa Hanan hannu ne, Al’mazeen ba zai yarda ba, tunda su Sady suna hanya mu jira isowarsa kafin mu yanke shawara” Hanan dake kuka ta ɗago tana kallon hannunta da shati ya fito raɗa-raɗa ta share hawaye tana fadin

“Wlh sai na koya mata hankali, zata gane shayi ruwa ne,ita har ta isa! Wacece ita! Waye ubanta! Tana ‘yar aiki!”

“Bar ta ubanta zamu ci dan naga abun nata ya fara wuce gona da iri” Beenah ta ce

“Hummm! Ku ga sadda tazo gidan nan ba ruwanta, amma daga dawowar Al’mazeen sai wani falli take ji da shi, ga shi kullum tana part ɗinsa da yana nan da baya nan, anya kuwa babu wani abunda yake gudana a tsakaninsu?”

       “Ai dama ba banza ba! kinga dai yadda Al’mazeen ke shakkarmu…”

“A’a fa Maman Hanan ba dai shakkarmu ba,yana dai kyalemu kasancewarsa mai biyayya yana shanye duk baƙinciki da takaicin da muke ƙunsa masa” Maman Beenah ta katsewa Maman Hanan hanzari ta hanyar faɗin haka.

       “To ai ga shi yanzu wannan ‘yar banzar mai aikin tana shirin hanamu rawar gaban hantsi ‘yan kuɗaɗen da muke karba a wajansa wannan shegiya ‘yar banzan tayi ƙyam-ƙyam” Maman beenah zata kuma yin magana suka jiyo sallamarsu Sumy da Sady da karfi sai kace zasu tada gidan, kafin su Maman Hanan su sauko Azima ce ta fara sauƙowa ta fito part din Al’mazeen hannunta dauke da kaskon turaren wuta da alama saka masa tayi, wani kallo Sumy da Sady suka bi Azima da shi har ta gama saukowa tayi hanyar waje ta kofar baya ba tare da tasan Allah ya yi wasu halittu a wajan ba, Sumy ta ce

“Tooo! Ina aka samu balarabiya ko ba india?” yatsine fuska Sady tayi ta ce

“Oho” saukowarsu Maman Hanan ne ya katsewa su Sumy maganar da sukeyi, nan aka hau musu sannu da zuwa, sai amsawa sukeyi a gadarance,Sumy ce mai gajan hakuri ta ce

“Anty (maman Hanan kenan) wacece wata ‘yar dogowar yarinya fara ,tasa riga da wando da wani baƙin glass sai kace ba india?” Maman Hanan tayi tsaki tana bin Sumy da Sady da kallo ta ce

“Yoo ai ita ce wacce muke gaya muku Azima” 

“Kan Uba! To ma uwarwa ta yiwa wannan shigan a gida tana mai aiki uban wa ya bata wannan damar!?” cewar Sumy, Hanan ta share hawayen da suka gaza tsayuwa dan ji take kamar hannunta zai fita ta ce

“Ba dai yanzu ku ka iso ba? To tunda Al’mazeen ya dawo take ji da iskanci iri da kala”

“son Al’mazeen din take yi ne?” cewar Sady tana tabe baki, Beenah tace

“Kar dai har kin fara kishinsa?”

“Wa? Ni? Allah ya kyauta! Al’mazeen baya raina sam, dan haduwa ya hadu amma ni zan auresa ne dan kudinsa kamar yadda ku ka ce Anty,zamu auresa ne sabida kuɗinsa da mun kwasheshi sai ya sakemu”

“Kai kuyi magana a hankali a ƙasa fa muke, kuma wannan shegiyar tana nan, to ma yanzu kin san me ya faru?” cewar Maman Hanan, nan ta basu labarin tsiyar da Azima ke yi a gidan, ta kara da murɗewa Hanan Hannu da Aziman tayi da safe sadda Al’mazeen zaije aiki, har Hanan na nuna musu hannunta da ya kumbura, haɗa baki Sumy da Sady sukayi suna fadin zasu ci Uban Azima, suna kan meeting din yadda zasu korata a satin nan sai gata ta shigo tana shirin sake wucewa kamar dazu Sumy da ta hangeta tun farkon buɗe kofa ta ce

“Keee ƙidahumar jeji jikar shanuka! Zo nan” wani birki Azima taci ta tsaya cak ba tare da ta dawo ba, Sady ta ce

“Dake ake ballagaza!” cije baki Azima tayi idonta na sake rinewa, rintse ido tayi ta hadiye takaicinta sannan ta dawo da baya ta tako tazo gabansu ta tsaya, Sumy ta ce

“Keee! Cire wannan bakin glass din idon naki!”

     “Ke a wa fa!? idan naki cirewa wata uwar zakiyi!?” Azima ta faɗa tana tinkaro Sumy, ja da baya sumy tayi, ganin haka yasa Maman Beenah faɗin

“Kee Azima! ba kya ganin baki ne? Ki dau kayansu ki haura musu da shi sama a wannan dakin da Hadiza ta gyara dazun nan”

“Su ɗin kutare ne? ko basu da hannun dauka ne? idan sun ga dama su da kayan nasu su kwana a nan” Azima na gama faɗi ta juya tana taku jikinta na langwasa harta taka step daya ta juyo ta kalli Sumy ta ce

“Kee kuma! karki kuma kuskuren fadin cewa na cire wannan madubin, dan kuwa kallo daya ake yiwa idanuna! idan kika kallesa baki kara kallon komai a rayuwarki!” Azima na fadi ta hau sama fuuuu! Aka bar su Maman Hanan a daskare.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button