AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 61-70

“Hamma Nawaz yadda wannan mota ke gudu kamar a iska inaji nan da yamma zamu isa”

“Kai har yamma?” Nawaz ya tambaya a gajiye dan tsakani da Allah ya gaji, yadda ya zare ido ya ba wa Aziza dariya dan haka tayi murmushi, suna tafiya Nawaz ya cewa Mazeen ya musu video recording ɗin hanyar, Mazeen ya ciro waya ya hau musu video ɗin.

          ????????????????

Yau tinda Hajja ta farka gabanta ke faduwa, ga shi jiya tayi mafarkin Azima da Aziza sun dawo, duk da mafarkin ba sabon abu bane a wajanta.

       Da yamma ligis wajan irinsu shidda haka Aziza ta shigo yankinta wani murna da annashuwa takeji, yayinda hawaye ya b’alle mata, hakika yanayin al’karyan ya tafi da zuciyar su Nawaz, gari kore shar dashi abun sha’awa ma sha Allah, ga korayen shuke-shuke da ‘ya’yan itatuwa, yankin kwana sun ga abunda basu taba gani ba, dan tun farkon shigowar su Nawaz a idon Salti ɗan gidan jauro nan yaje ya baza a gari ya ga wasu sabbin masifa ya shigo musu gari, wasu bayyanannun aljanu,nan yara da manya aka hau bin motar har gaban kofar gidan Baffa, nan aka hau cewa a kofar gidan Magaji masifan ta tsaya, mota na tsayuwa da gudu Aziza ta fito, su ma su mom fitowa sukayi,yayinda Mazeen ya fito da Azima Banju, dasu mom suka rufawa Aziza baya, mutane an cika ana kallon su mom, ko sallama Aziza bata iya yi ba tana shiga ta tsaya turuss tana kallon mahaifiyarta wacce ta rame sosai ta karayin wani fari fal da ita, Hajja na duƙe ta dibi ruwa a kwarya zata zagaya kewaye, su Mom ne suka shigo suma, cikin wani irin kuka da shauki irinta ‘ya wanda takeji a kan mahaifiyarta murya na rawa mai fizgar kuka Aziza ta ce

“Hajja!” kwass!! Hajja ta saki kwarya ta juyo da sauri, haba duk daren daɗewa muryar Azizanta ba zai goge a kunnuwanta ba, kallon Aziza Hajja ke yi jikinta na rawa tama kasa magana, da kyar Hajja ta ce

“Dan Allah Aziza yau karki b’ace ki barni, na yarda zan dinga zama da gizon naki dun Allah karki tafi” da gudu Aziza ta shige cikin hajja ta riƙeta gam-gam suna wani irin kuka mai ban tausayi, harta su Mom suma hawaye sukeyi, Malam Yunusa ya kalli Mom ya ce

“Hajiya Kamila(mom)Allah ya saka miki da mafificin alkairi, Nawaz da Al’mazeen Allah ya muku albarka” suka amsa da Amin.

     Ɗago Aziza daga jikinta Hajja tayi tana shafa fuskarta, Aziza cikin dashashshiyar muryarta tace

“Hajja nine na dawo, mun dawo” Hajja na shirin magana sai ga Baffa wujigan a muraran, yana can garkin shanakunsa Salti yaje ya samesa yace ai ya ga bataliyan aljanu sun nufi gidansa yanzu haka aljanun suna gidansa, shiyasa Baffa yazo a hargitse, Baffa na shigowa da sauri Aziza ta zo ta ce

“Baffa ni ce Azizanka! Baffa na dawo, kace kar na dawo sai da Azima, Baffa gata nan ga Azima nan” duk irin kunya irinta fulani nan Baffa ya rungume Aziza yasa kuka, an jima ana koke-koke, Sarki Chubaɗo dasu mai unguwa ori dasu Garkuwan yankin kwana, kai duk jama’ar yankin kwana an taro agidan Baffa, sai bayan an gama kuka tukunna aka basu abun zama, Sarki Chubaɗo yace

“Kafin a zauna ya kamata mu fara sallar magriba, hakan kuwa akayi, Aziza ta basu ruwa sukayi Alwala suka nufi masallaci.

      A cikin gida ma Hajja ce ta ba wa Mom da Maman Beenah ruwan alwala, taki yarda ta daga kai ta kallesu sabida kunya irinta fulani, Maman Beenah kuwa ba bakinciki kauyen ya mata kyau ya burgeta.

    Bayan sun idar da sallar, Hajja na zaune kusa da yaranta nan suka hau gaisawa dasu mom,mom ta kalli Hajja tayi murmushi ta ce

“Kyawu! Kyawun hali! Kunya! Natsuwa! Ashe duk ba a banza Aziza ta dauko ba, ta biyo Mahaifiyarta ne, dadtako halin girma! Jarumta a fuska da kuma jiki ta biyo halin mahaifinta ne! Ina tayaku murna da samun ‘ya kamar Aziza” Al’mazeen da suke shigowa cikin gidan yace

“Kai mom,Aziman fa?” 

“Har da itama mana”

“To kishi kakeyi dan an yabi Aziza?” cewar Nawaz yana hararan Mazeen, murmushi su Arɗo sukayi sannan aka zauna aka hau gabatarwa da juna kai, mom ce tayi musu bayanin komai har izuwa auren da su Azima da Aziza suke da shi a yanzu, sannan ta gabatar da Nawaz a matsayin mijin Aziza ta gabatar da Al-mazeen a matsayin mijin Azima, ta ɗan bada tahirin kansu a gajarce, dago ido baffa yayi ya kalli Al’mazeen ya Kalli Nawaz kawai sai ya fashe da kuka, Baffa Mandi ya hau bubbuga kafadun Baffa yana fadin

“Alhamdulillah! Hakika Allah baya bacci,kuma yana tare da masu hakuri da masu jahadi da sadaukarwa, hakika kayi jahadi wa yankuna da dama, kayi sadaukarwa wa yankinka da komai naka, sannan kazo ka kara bi da hakuri da juriya, taya Allah zai barka a haka Magaji? yanzu dubi ka ga mijin da Allah ya bai wa Azima da Aziza, da munata tunani da kokonta wa zai auri Azima da Aziza dan ya kawo mana karshen Banju, sai ga shi Allah ya turo mana mutane daga wasu duniya daban”

Sarki Chubaɗo ya ce

“Tabbas kuwa Magaji,kai ba mutum bane kamar kowa bane, hakika muna yiwa Allah godiya daku sirakananmu, mun gode da wannan jahadi Allah ya baku lada” aka amsa da amin, nan Sarki Chubado da mai unguwa ori suka bada umarni a shiryawa manyan baƙi kuma sirakanan Magaji Bawa Shugaban garkuwan kwana abinci mai rai da lafiya, nan aka kawo wa su Mom hadaddiyar kindirmo yasha damu, Inna wuro ta ce

“Wata kila ba zaku iya cin abincin mu ba” Mom tace

“Ai idan muka sha wannan furan wlh alhamdulillah sai kuma gobe” Al’mazeen ya ce

“Ana ta magana amma banji anyi maganar matata ba?” Baffa ne ya sunkuyar da kai Hajja kuwa rufe fuska tayi, Arɗo ne yayi murmushi ya ce

“Ohh Allah Kaɗo babu kunya, yanzu kai a gabanmu kake maganar matarka?”

Almazeen ya sosa keya ya ce

“To ai kaka gani nayi to bari dai nayi shuru” aka sa dariya, Baffa yace

“Kayi hakuri ɗan nan, sakin matarka ba tare da kayan aiki ba babban hatsari ne ga mutanen yankin nan gabadaya, ka jira har zuwa gobe idan na daure shi tukunna, ai yanzu ba matarka bace katon aljani ne mugu” shuru Almazeen yayi yana kallon Azima wacce ta koma gunki, a hankali Aziza ta miƙe zata shiga bukkarsu, jiri ne ya kwasheta nan ta fadi, kafin kowa yayi kanta Nawaz ya fara dagota, Hajja kuwa ganin su Mom sun rufu a kan Aziza yasa ita taji kunya ta koma gefe tana leken fuskar Aziza, Baffa ne ya kama hannunta ya ce

“Ya salam! Aziza an huda jikinki ko?” gya ɗa kai Aziza tayi tana jan numfashi, Baffa yace

“Dole sai an nemo furen huriri”

“Me hakan yake nufi Baffa?”  cewar Almazeen

“Ai kasan ita ba asalin mutum bace,maciji kuma baya son tab’o”

“Amma an harbi Azima bai bata illa har haka ba?”

“E sabida ita Aziza Banju ya rigada da ya maidata macijiya shine dalili, ga shi yanzu dare yayi ina zan samu furen huriri?” tashi Baffa ya yi ya fita zaije jejin kwana ko Allah zai sa ya samu, yana fitowa da Inno Fandi ya hadu ta mika masa furen huriri tace

“Ina matukar farin ciki da Allah ya dawo da Azima da Aziza lafiya, sai kuma shirin kashe Banju a gobe ko?” Baffa ya sosa kai yace 

“Humm Fandi, abun kunya nake jin kunya” Inno Fandi ta gano abunda yake nufi dan haka ta hau masa dariya, dan kunyar kuwa na kusantar Azima da Al’mazeen zaiyi ne,tunda dole sai Almazeen ya kusanci Azima kafin Banju ya fita a jikinta a kashesa.

      Da sauri Baffa ya koma ciki, Ardo yace

“Magaji ina da kaje?”

“Da wai zanje jejin kwana ne nemo furen huriri to sai Fandi ta kawo mini” jin sunan Inno Fandi yasa Aziza fara murmushi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button