AZIZA DA AZIMA COMPLETE HAUSA NOVEL

AZIZA DA AZIMA 61-70

     Jiƙa mata furen huririn akayi,tana sha ta ware.

     Su mom sun saki jiki da mutanen yankin kwana sai hira sukeyi kamar an jima da sanin juna.

      Sai da dare ya tsaga Ardo yace su mom suje su kwanta su huta, su mom gidan Arɗo aka kaisu aka gyara musu wajan kwanciya, su Nawaz kuwa gidan Sarki Chubaɗo aka kaisu.

        A ranar Aziza da Hajja basuyi bacci ba kwana zaune sukayi suna kuka suna hira, Azima na kafe a gefe, sai da akayi asuba tukunna Aziza ta fara jin bacci Baffa kuma ya ce mata ta fito zai daure Banju sai ta sakesa, Aziza ta miƙe tana hamma dan bacci takeji.

      Kayan yaki Baffa ya tanada, sai wajan   takwas jama’ar yankin kwana suka hallara, Baffa ya kalli Aziza ya mata ido alaman ta saki Azima, gya ɗa kai Aziza tayi tasa hannun ta dafe goshin Azima wani haske na shiga goshin Azima, wani ajiyar zuciya Azima ta sauke, nan ta dawo hayyacinta, idanunsu ne ya sarƙe da na Baffa

“MAGAJI BAWA!!?”

“na’am BANJU! maraba da dawowa Yankin kwana!”

         ????????????????????

MOMYN AHLAN✍????

[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????

    ????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨

    (???? _Macizai ne_????)

    MALLAKAR.

*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*

SAHIBAR KAINUWA.

Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din

0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.

Sanarwa.

Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.

*بسم الله الرحمن الرحيم*

*____________________________________*

*????KAINUWA WRITERS✍???? ASSOCIATION*????????

“`{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}“`

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan*????????

https://bakandamiya.com/group/71/kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*MARUBUCIYAR.*

1- _HALITTA DAGA ALLAH NE._

2- _GUDU A JEJI._

3- _SHUHADA._

4- _NIDA ƘANNEN MIJINA._

5- _WA’YA KASHE ZAHRA’U?(#200)._

6- _COLONEL UBAIDULLAH._

7- _ITA CE ZUCIYATA(#200)._

8- _SAMIMA (MACIJIYA CE._

9- _GAWURTACCEN SOJA(#300)._

10- _DA NA SANI NA._

  11- _BADAWIYYAH_

12- _DEPUTY SUPERINTENDENT OF POLICE (DSP ALIYU HAIDAR)_

Now

13- _AZIMA DA AZIZA (MACIZAI NE????)_

_Follow me on wattpad,@Fateemah’0_

   ????????????????????

*PAID.*

????️=6️⃣9️⃣↪️7️⃣0️⃣

“Wlh Baffana bani bace! Wlh ban yi yunkurin kasheka ba!” gya ɗa kai Baffa ya yi yana shafa kan Azima ya ce

“Na sani Azima” riƙe Baffa tayi gam tana kan ci gaba kuka, nan al’umman yankin kwana suka hau hamdala ana taya juna murna, wa inda sukayi wauta da farko ta hanyar dukan Aziza suka hau ba wa Baffa hakuri yace shi kam ya wuce a wajansa, nan aka zauna ana ci gaba da jajinta lamarin, lokaci zuwa lokaci Azima tana ɗaga ido ta kalli Almazeen wanda yake lullubi idonsa a lumshe bai san hayaniyar da ake yi ba.

     Maga isar da sako ne ya shigo da sallama yace Sarakunan Yankuna da Muƙarrabansu sun fara isowa da wani lokaci za a fara fafatawa?” Baffa ya ce

“A shirye nake, amma a bar fafatawar sai anyi sallar la’asar da yamma kenan, a ƙara shiryawa mutanen yankuna wajan zama mai kyau da abun motsa baki dan kar su gajiya, sannan a dama musu nono mai kyau a tabbatar an basu isasshe ba ƙasasshe ba” Maga Isar da saƙo ya amsa da to, sannan Baffa yace

“Mu tafin ku dan a kara shiri” dukkansu suka fice aka bar Nawaz da Azima da Aziza, Azima idonta na kan Almazeen wanda lokaci daya taji zuciyarta ta harba da shi, a yanzu yana cikin wannan halin ne sabida ita, wani  kuka Azima ta kara sakawa tana rufe fuskarta da sauri Aziza tasa hannu ta riƙo hannunta tana fadin

“Haba Azima miye haka? Godiya zakiyi wa Allah dasu Mom da Hamma Mazeen” cikin kuka har tana sheshsheƙa ta dago idonta wanda yanzu ya koma daidai amma dik da haka basu da baƙin ido ta kalli Aziza tana girgiza kai ta daga hannuwanta hawaye na zuba ta ce

“Aziza! Ni! Wai ni da kaina na ke son kashe mahaifin da ya haifeni! Wai ni da kaina na rayuwa bana bautar wanda ya halicceni! Wai ni da kaina mutane suka shiga masifa da tashin hankali! wai ni da kaina na maida yar uwata ta biyuna macijiya! Wai ni da kaina….!” kuka yaci karfinta da sauri Aziza ta rungumeta tana bubbuga bayanta itama tana kuka 

“Taya zan manta da wannan abun a rayuwata! Kenan mu haka kaddararmu take!” ɗago fuskarta Aziza tayi tace

“Karki yi sab’o, ki godewa Allah, sannan duk abunda kika lissafa ai bake kikayi ba Banju ne ya yi, dan haka ki bar fadin haka Sis” cikin kukan tausayi da Azima ta kasa tsayarwa tace

“Amma da jikin wa!? Da fuskar wa?” 

“Koma da miye ne komai zan zama tahiri, ki ta nanata kalman Innalillahi wa inna ilaihirrajiun! Yafi wannan sambatun da kikeyi dan bana so,kina ji na ko?” Azima ta gya ɗa kai hawaye na kan sauka tana kallon Almazeen wanda Nawaz ke riƙe da hannunsa yana ji kamar yasa kuka dan tausayinsa, zuwa can da suka gama kukan Nawaz ya kalli Aziza ya ce

“Tashi mu tafi watakila yanzu kam ana can filin yaki, zo muje karo na farko a rayiwata naga yadda ake faɗa tsakanin mutum da aljan” tashi Aziza tayi ta kalli Azima tace

“Ki kula da kanki da kuma Hamma Mazeen uhum?” Azima ta gya ɗa kai, Nawaz da Aziza suka fita, suna fita Azima ta miƙe a hankali ta karasa jikin gadon ta kwanta a kusa da Almazeen har yanzu jikinsa da zafi sosai, tana kwantawa ta kama hannunsa tana kallon kyakkyawar fuskarsa ta ɗora hannunsa a fuskarta ta lumshe ido.

        ⚔️⚔️⚔️⚔️⚔️

Hakika su Mom sun sha mamakin ganin mutane him a wannan alkarya, mutanen yankuna sun zo daga yankuna daban-daban, jama’a an cika ana kallo, Aziza na zaune kusa da mom, Nawaz yana gefen hannun hagunta, ya ce

“Mom wlh naso ace sultana tana nan da ta ga abunda take kalla a zahiri a tv” mom tayi murmushi.

      A hankali Baffa ya fito yana riƙe da zureren takwabinsa wanda ya kashe Banju da shi a karon farko amma wannan karon bai yi amfani da zaren sakar dana ba, dan ko ya koma jejin lore ba ba shi za ayi ba,amma duk da haka yau sai ya kashe Banju da yardan Allah.

    Kunce Banju Baffa ya yi, Banju yana ganin takwabin hannun Baffa  ya ce

“Magaji! ka ajiye takwabin nan ba da shi zamu gwabza ba” murmushi Baffa ya yi ya kalli Nawaz ya miƙa masa takwabin, zuwa Nawaz ya yi ya karba yana riƙewa sai da yaji damtsen hannunsa ya girgiza, kara sarawa Baffa Nawaz ya yi sannan ya koma ya zauna.

     Banju ya kalli Baffa ya ce

“Ba kai ka yarda da kanka ba?to inaso ne mu gwabza da karfin-karfi,ni aljani ne faɗa da aljani kuma ba dadi” jan kafa baya Baffa ya yi ya ware hannunsa ya ce

“Bar ganin ka ƙereni a tsayi da girman jiki! a haka na daureka na kasheka a farko, ni mutum ne amma ba irin wanda kake tunani ba na san kasan da haka” Baffa na fadi ya hau tada guguwa, ganin haka yasa Banju wani juyi ya koma wani shirgegen Maciji???? blue mai matukar kauri da girma, wayyo karka so ka ga yadda wasu daga cikin masu kallo aka watse daga ciki kuwa har da mom, dan tace wlh wannan kallo ba da ita ba.

         Kokarin sara Banju ya hau kai wa Baffa Baffa na b’acewa a cikin iska, yayinda masu kallo aka kara ja baya ana darewa ana basu fili dan yau abun babba ne, an gwabza sosai tsakanin Baffa da Banju, da ya ga tabbas ba fa zai samu galaba a kan Baffa ba nan ya yanki wajan jama’a yana shirin ya kai musu sara dan kuwa ya tabbatar da Magaji zai kashesa! to dan haka a cikin wa innan dibbannin alumman gwara ya shafe ko da rabi ne, nan ya yi kansu gadan-gadan ganin haka yasa Nawaz fizgar hannun Aziza suka sa gudu  tare da mutane, ganin yadda Banju ya yi kan alumma yasa Baffa haɗa hayaki ya kwashe mutanen ya zubar dasu gefe, jelarsa Banju yasa zai kwashi wasu kafin ya kwashe Baffa ya kuma kwashesu, ganin haka yasa ya buɗe bakinsa zaiyi musu b’arin ambaliyar wuta cikin hanzari Baffa yayi wani tsalle ya tashi sama, dan kuwa idan Banju yayi b’arin wutar nan za a mutu dayawa, kafin Banju yayi tuni Baffa ya haye saman kansa tare da zaro wani wuƙa ya dab’awa Banju a tsakiyar kai, cak Banju ya tsaya, a hankali ya fara sulalewa yana zama mutum har ya zama mutum gabadaya, yana gama zama mutum Baffa na zaune a saman wuyarsa da karamin wukar da ya dab’a masa, tsalle Baffa ya yi ya sauka daga wuyar Banju ya dirƙo akan kafafunsa ya juya baya ya maida hannunwansa ya rungume a bayansa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button