AZIZA DA AZIMA 61-70

Da kyar Banju ya ce
“Wuƙar Dafi!” Banju na faɗi wukar ta narke a cikin kan Banju ta b’ace bat, dan kuwa ba wuƙa bace kamar sauran wuƙaƙe, Baffa ne ya haɗa da hannunsa dan zuwan wannan rana, sharabbbb!! Banju ya zube a kasa, nan take ya kama da wuta har sai da yaci ya ƙone ƙurmuss!! Hamdala da Wani ihu da guɗa da al’umma suka saka suna fadin
“Magaji! Magaji! Magaji!” suna daga hannu, wani hawaye ne ya tsiraro daga idon Baffa, da gudu Aziza ta tashi ta zo ta rungume mahaifinta tasa kuka, shima Baffa tamkar an cire masa wuƙa a maƙoro haka yakeji, Nawaz ne ya taso ya zo shima Baffa ha rungumesa, sannan ya karbi wuƙar ya damƙawa Aziza a hannunta yace a mallamaka mata dan tare sukayi yaƙin, nan aka kara sa ihu ana kabbara kafin kace me an daga baffa sama ana ambatar sunansa, sarki chubaɗo mai unguwan yankin kwana ori da kowa na yanki kwana murna sukeyi harda hawayen farinciki, sauran yankuna kuwa ji sukeyi ina ma ace Magaji a yankinsu yake, ko ba komai zasu samu karramawa da girmamawa da daukaka daga sauran manyan yankuna, haka aka dinga miƙawa Baffa hannu ana jinjinawa jarumtarsa.
Da kyar suka saffe sukayi sallar magriba, wasu yankuna wa inda basu da nisa sai sun koma yankinsu wasu gobe zasu koma.
Ranar yankin kwana wasai, duk majalisa kuwa hiran Magaji Bawa ake yi da yaransa Azima da Aziza, Jauro kuwa dan kunya da tsangwaman da ake masa yasa ya kasa fitowa.
Washe gari bayan manyan yankuna sun karrama Baffa nan suka gaya masa ai a yankuna yanzu babban yanki shine yankin kwana, bayan an gama komai suka yi masu sallama, godiya sosai jama’ar kwana sukayi ma wa inda suka samu damar halartan wannan gayyata ta fafatawa.
Bayan kwana uku da faruwar hakan komai ya zama daidai alhamdulillah Ma sha Allah.
Yanzu Baffa ya maida hankalinsa a wajan yiwa Almazeen magani, sai da Almazeen ya shafe sati curr kafin ya farfaɗo ya dawo hayyacinsa, a wannan lokacin su mom sunyi sabo da mutanen kauyen kwana fiye da tunanin mai tunani.
Washe garin ranar da al’mazeen ya farka nan sarki chubaɗo ya tara su yace yana da magana, bayan kowa ya haɗu nan yake shaida bukatarsa na son sauƙa a kan kujerar mulkin yankin kwana, sannan ya bayyana Baffa a matsayin wanda zai mulke yankin kwana, girgiza kai Baffa ya hau yi kafin yace a’a tuni alumma sukace sunji sun gani, babu yadda Baffa ya iya dan kuwa bai so ba amma kowa ya nuna yana son Baffa ya mulke yankin kwana, haka sarki chubaɗo yasa aka rubuta sakon gayyata inda yankuna suka ce zasu zo, dan za ayi bikin da ba a taba yi ba na al’adun fulani.
????????????????????
Kamar yadda aka tanada haka kuwa ta kasance wajan karfe goma na safe aka fara bikin naɗa Baffa sarautar kwana, inda manyan yankuna da ƙananun yankuna duk sun zo, anyi walima Baffa ya samu alkairi ba ma iyakar shi daya ba harda jama’ar yankinsa, yankin kwana Allah ya ɗagata sama.
Wajan irinsu biyu haka aka kammala taro lafiya, an yanka su shanaye dasu kaji da zabbi an sha kindirmo, kai taro dai tayi saidai muce Allah ya taya Baffa Magaji Bawa Arɗo riƙo.
Da yamma Azima da Aziza suna zaune a bukkarsu, hajja kuma suna bukkarta dasu mom, bayan Aziza ta gama koyawa Azima karatu ta kalleta ta ce
“Aziza dama ina son na tambayeki” gyara zama Aziza tayi tace
“To inajin yar uwata” maganganun da Al’mazeen ya gaya mata a kunne ne take son Aziza ta fassara mata, dan ta kwashe maganganun tsaf a cikin kanta, dan haka ta gayawa Aziza tace ta fassara mata, dariya Aziza ta hau yi har tana riƙe ciki ta ce
“Inyee! Kin faɗa soyayya ne?” haɗa rai Azima tayi tace ban son wulakanci idan ba zaki gaya min ba sai naje na tambayi mijinki Hamma Nawaz ko naje na tambayi mom”
“Allah ya baki hakuri maida wuƙar” nan ta fassara mata abunda kalmomin ke nufi, wani murmushi Azima tayi tana rufe fuskarta da tafin hannunta, Aziza zatayi magana sukaji sallamarsu Nawaz sai da gabanta ya faɗi, su dai basu fito ba sunajin maganarsu dai a tsakar gida, Almazeen ne ya ce
“Mom ya kamata mu koma gida, dan muje mu dubasu mu ga lafiyarsu, barin ma mu da muke da asibiti” mom ta ce
“Nima na fara wannan tunani zuwa anjima zamuyi magana da Baban su Azizan” wani zaro ido Azima da Aziza sukayi bama su kadai ba harda Hajja, dan tasan za a kwashesu a tafi dasu ne tunda yara da mazajensu, kuka ta fara haɗiyewa, Almazeen ya kuma cewa
“Mom ina yaran naki suke? Ya kamata dai yau su zo su kai mu yawo mu ga gari” mom ta ce
“Hakane, Azima! Aziza!” a sanyaye suka amsa da na’am, barin ma Aziza damuwarta yafi bayyana ƙarara a fuskarta, a tare suka fito suka duƙa, mom tace
“Ku dauko mayafi kuzo ku kai mazajenku yawon ganin gari” amsawa suka yi da to suka dau mayafin dama dogon abaya ce iri daya a jikinsu, mayafinsa suka dauka suka rufa kansu da shi, a kofar gida suka samu Almazeen da Nawaz sannan suka hau tafiya babu mai cewa qala, duk inda suka wuce sai an bisu da kallon burgewa ganin yadda suke tafiya tamkar wasu taurari masu haska sararin samaniya.
Bayan sun kewaya dasu, Azima ta kalli Aziza tace
“Ukhty muje rafin jimulo” a sanyaye Aziza ta amsa da to, dan tun lokacin da taji anyi maganar tafiya jikinta yayi sanyi dan idan tace tana son komawa tayi babban karya, suna isa rafin wani iska mai dadi da yake kaɗawa ga ruwa farin sol abun burgewa ga ganyaye kore shar kwance a wajan,
“Wowww!” Nawaz da Almazeen suka furta, Azima tana satar kallon Almazeen, hannunta ya kama suka zagaya ta gefen rafin dan yana da bukatar suyi luv, dik da mugun kunyarsa takeji, suna barin wajan Nawaz ya maida idonsa kan Aziza wacce duk ta taburce kamar ma kuka take son yi, dan ita har yanzu bata taba ji Nawaz yace yana sonta ba, dan haka itama ba zata buɗe zuciyarta ba balle ta cutu, hannunta ya kama tayi saurin daga ido ta kallesa, janta yayi ya haɗata da bishiya murya a can kasa ya ce
“What’s the matter?” girgiza kai tayi sai kuma hawaye suka biyo baya, hannu yasa ya goge mata yace
“Ba ki so ki koma ne ko?” shuru tayi, wani murmushi yaƙen takaici ya yi yana sakinta ya juya baya ya ce
“Na faɗi daidai shiyasa kika ƙi cewa komai?, karki damu duk yadda kike so kiyi, bcox u are free now” ya faɗa kamar a ɗan zafafe, rungumesa ta baya Aziza tayi tasa kukanta mai sauti, rintse ido ya yi ya ce
“Kamar dai na taba gaya miki bana son kuka ko? To sakeni!” sake riƙesa tayi, hannunta yaja suka isa bakin ruwan ya zauna ya zira kafafunsa a ciki, itama zaman tayi kusa da shi ta kamo hannunsa ta kifa kanta a kafadarsa, bata san lokacin da ta furta masa cewa
“Hamma Nawaz, ka taba ji kana sona? Ko kawai tausayina kakeji?” ajiyar zuciya ya sauke ya juyo ya fuskanceta yace
“Idan har zaki iya karanta abunda yake cikin idona, sannan ki auna bugun zuciyata” ya fada yana ɗora hannunta a saiti zuciyarsa dake bugawa da sauri
“Zaki iya ba wa kanki amsa, idan hakan bai samu ba, ki bari idan muka koma kd zaki tabbatar” daga haka bai sake cewa da ita komai ba banda rungumeta da yayi.
????????????????
Almazeen suna zagayawa baya da Azima ya rungumeta sosai a jikinsa, rufe fuskarta tayi da kirjinsa tana murmushi tanajin wani bakon yanayi a tare da ita, sakinta Mazeen ya yi ya rungumeta ta baya ya ce