AZIZA DA AZIMA 61-70

“Na gama haukacewa na susuce a kan son….” shuru yayi ganin tana ta wani aikin rufe fuska, bakinsa yasa a saitin kunnenta yace
“Wai ni wannan kunyar na miye ne? tinda na farka ake guduna, ko dan sabida daren….” bai karasa ba ta jiyo ta sauri ta rike bakinsa tana shigewa jikinsa, murmushi yayi yace to faɗamin
“Ana sona?” ɗago kai tayi tasa idonta a na shi ta ce
“Idan ban furta hakan ba na zama butulu! wanda ya sadaukar da rayuwarsa domin tawa, miye ribata idan ban so shi ba, ance tukaicin so kauna, sabida haka ina kaunarka Hamma Mazeen” wani runguma Mazeen yayiwa Azima cike da so, kafin ya haɗe bakinsa da nata ya hau bata hot kiss, Azima tayi alkawari ba zata taba juyawa Mazeen baya ba kamar yadda shi ma bai juya mata ba a lokacin da take abun gudu a wajan mutane, shiyasa ko da yake romantic dinta bata yi yunkurin dakatar da shi ba, tsayuwa ce ta gagaresu suka zube kasa, murzanta yake yi cikin salo da shaukin kauna, Azima ganin hankalinsa ya fara gushewa ne ya sakata zare jikinta daga na shi,yayi saurin riƙota ta ce
“Don Allah Hamma, ka duba inda muke,kuma ma ai” sai kuma tayi shuru, saurin saita natsuwarsa Almazeen ya yi, amma gaskiya ba zasu kara sati a garin nan ba zasu koma dan ya samu yaji dadin bai ji ba a daren farko dan wuya kawai yaci.
Tashi yayi ya kama hannunta ya ɗagata tsaye, yace
“Muje gida” riƙesa tayi tace
“Kayi fushi ne?” ɗan murmushi yayi ya girgiza mata kai alaman a’a, wajan su Nawaz suka dawo har yanzu suna zaune a bakin ruwa yana rungume da Aziza, Almazeen ya ce
“To romio and Juliet muje gida lokacin sallar magriba yayi” Nawaz yace
“Okay Laila da Majnun” dariya Almazeen yayi dan zuciyarsa fari sol.
Gida Suka tafi, bayan sallar isha’i mom ke gayawa su Nawaz yadda sukayi da Babansu Aziza kuma itama tayi na’am da maganarsa na cewa a dan barsu Azima da Aziza tukunna, su zasu tafi gobe, Almazeen da Nawaz kamar su kurma ihu, Nawaz da gajen hakuri yace
“Har na kwana nawa?” mom tace ungo nan naka????????
“Har na tsawon wata daya,ni kuma nace a barsu suyi wata biyu tunda alfarma suka nema,kuma ai gaskiya ne tinda sun jima basu ne, yanzu kuma zama na dindindin zasuyi daku”
“Haba dan Allah mom, yanzu dake za a yanke wannan shawaran?” cewar mazeen,mom tace bana son rashin kunya, maza ku tashi ku fara shiryawa, a zuciye Nawaz ya fice Almazeen ya bisa a baya.
Washe gari asubanci sukayi, kaff jama’ar kwana aka fito yi musu sallama, Almazeen ne kawai yayi sallama da Azima inda ya jima yana tsotsar bakinta, Nawaz kuwa ya ƙi kallon Aziza dan yace itama harda haɗin bakinta dama ba son komawa take yi ba.
Baffa ya haɗawa su Mom kaya sha tara ta arziki yayinda suke zubawa juna godiya cikin mutunci da mutuntawa, haka Baffa ya rungumi su Almazeen da Nawaz, sukayi musabaha da Malam Yunusa da Alhaji Karami, su Inna wuro ma sunyi wa mom da Maman beenah abun arziki, mom tace
“Dan Allah wata rana ku kawo mana ziyara, da sunyi wata daya kuma mazajensu zasu zo su daukesu”
“In sha Allah” mota suka shiga aka dinga ɗaga musu hannu, da gudu Nawaz ya figi motar Aziza ta fito itama da gudu tana daga masa hannu ya hangeta ta glass din mota amma sai ya kara gudun motar, cikin rashin jin dadi tin daga Azima har Azizan suka juya jiki a sanyaye, a ranar haka suka wuni zuciyarsu babu dadi amma suna zuba hira da wasa da dariya da Hajjarsu,yayinda Yawuro ta fara musu gyara tana tsumasu dan tana so ace kafin nan da wata dayan nan sun sama zam-zam dasu, idan mazajensu suka kusancesu basu ba kara tunanin wata mace.
@@@@
Sabida gudun da suke yi yasa biyar na yamma suka fice daga jeji suka b’illa titi, yau ma sai da suka kara kwana cikin garin yola kafin da washe gari suka kama hanyar kd, suna isa mom ta kira sultana tace mata sun dawo, wani ihu da murna Sultana tayi a waya mom ta bata labarin abunda ya faru, bata gama ji ba zumudi yasa ta katse wayar ta kalli Khalil dake danna waya tace
“Dear su mom sun dawo” da murna a fuskarsa yace
“Alhamdulillah”
“Dear tashi mu tafi ina son ganin Aziza”
“Oh Allah sultana ki bari su huta sai muje da daddare”
“O’o ni kawai ka tashi mu tafi yanzu sai ka dawo ka daukeni da daddaren” ta fada tana buga kafafunta a kasa” hararanta yayi yace “ai saiki dauko mayafinki” kiss ta sauke masa akumatu tana godiya da gudu ta hau sama dan dauka mayafinta ta sauko a mota ta samesa ya tada suka nufi gidansu.
????????????????
MOMYN AHLAN✍????
GARKUWAR MACIZAI????????
[4/13, 10:13 AM] Mom Ahlan: ????????????????????????????????????????
????✨ *AZIMA DA AZIZA*????✨
(???? _Macizai ne_????)
MALLAKAR.
*ZAHRA ABDUL(MOMYN AHLAN)*
SAHIBAR KAINUWA.
Littafin kuɗi, naira ɗari kacal dan masoyana, turo da kudinki ta wannan acct din
0096035983 balaraba hassan accees bank, ko kuma hoton kati ta wannan lambar 08165550116, pls ban da vtu.
Sanarwa.
Ga yan niger masu bukatar book din nan su tuntubeni dan sanar dasu yadda zasu biya kar ayi babu ku.
[ad_2]